page 37

88 4 0
                                    

*PHTEENJIDDAH*

*MALLAKAR*
*_Ƴar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
 
 

     
                             37

Abu dayane ya fadoma zuciyar Phaty yaya ma akai wannan guy din yasan inda take, harya iya kawota gida ba tare daya nemi taimai kwatancan gidansu ba, acikin zuciyarta kuwa fadi take _"Wanene wannan?, koma waye ya sanni, to a ina?, tayaya?, sai kuma tace bani da amsan wannan tambayayoyin nawa, koma wanene ALLAH yasa da alkhairi yake nufi dani"_ Wayanta ne tajiyo yana ta faman ruri janyota tayi ta daga ba tare data duba mai kiran nata ba, ji tayi ance "Kizo ina kofar gida, ke nake jira yanzu" kafin tai magana taji an yanke kiran dubawa tayi daga ai Umar ne ke kiranta murmushi tayi mai kayatarwa tace "My everything" Mikewa tayi taima fuskan nata kwaskwarima ta dauko hijab ta saka, fita tayi dan a tunaninta su Dad and Mom dinta sun tashi, suna nan inda suka barsu kana ganinsu kaga masoya tsantsa dan dukkaninsu fuskokinsu cike take da annuri, Phaty ce ta karasa wajan tace "Dad wai Umar yana kirana yacemin yana waje"

Dad din kallanta yayi yace "Kice mai ya shigo mana sai kace gidan bakonsa ne"

Phaty tace "Nima zan fada mai haka kenan naji ya kashe wayan ga dukkan alamu baisan shigowane shiyasa"

Mom tace "Kodai yau an rigasa shigewa dakin baki ba, dan dazu Dausayi yazo suna tare da Jiddah ma"

Dariya Dad yayi yace "To kinji dalilinsa na kin shigowa, amma in banda abunsa duk fadin gidannan ace daki daya muke dashi ana hira shima yasan ba haka bane, to inkinje ki gaishemin dashi"

Phaty fita tayi tana fadin "Zan fada masa Dad"

Cikin sauri Phaty ta fita waje, tana zuwa ta tsaya a bakin get din gidan tana hango Umar, gani tayi ya kara yi mata haske da kyau, cikin zuciyarta fadi take _"Tsarki ya tabbata ga ALLAH, mai halitta bayinsa"_ Jikin Umar ne ya bashi ana kallansa, waigawar da zaiyi sua hada ido da Phaty, wani sassanyar murmushi ta sakin masa mai kara narkanmai da zuciya, tuni yaji gwiwarsa ta sage, dan zuwan da yayi yazo ne yayi mata fada matuka saidai su bata, dan bazai runka dakon faduwar gababa, sai wata zuciyarsa ta shaida masa cewar bafa laifinta bane, ganin yadda taga Umar bai maida mata da martani ba tasan akwai matsala, ga dukkan alamu baya cikin walwala, karasawa tayi jiki ba kwari, tana zuwa bakin motar tace "Ka shigo cikin gida maba, ka tsaya a waje"

Umar kafeta yayi da idanuwansa mai rikitar da ita, yana nazari, Phaty kuwa ganin kallan da yake matane jikinta ya tabbatar mata da akwai matsala, dan Umar baya yi mata wannan kallan haka kawai, Murmushi ta kakulo ta kara cewa "Ka shigo mana naji kayi shiru, ko yau bakason shigowa gidannamu ne?"

Ajiyar zuciya yayi yace "Ba haka bane, akan hanya nake shiyasa, dama nace ne bari nazo na ganki kina lafiya, dan dazu na kiraki baki daukanmin waya ba, na dauka ko laifi nayi miki wanda banda masaniya akai"

Phaty kallansa tayi nadan wasu dakikai tana nazarinsa, ko shakka babu akwai abunda Umar yake boye mata, amma da yake Phaty akwai iya bariki saita basar, bude murfin motar tayi ta shiga, tace "Ina fata hankalinka ya kwanta tunda yanzu kaganni ko?"

Murmushi ya karayi mata a karo na biyu yace "Kwarai ma, hankalina ya kwanta sosai, saidai na tambayeki baki bani ansata ba"

Phaty kallansa tayi, tace "Wata ansa kuma zan baka?"

Umar yace "Mai yasa dana kiraki baki dauka ba?, sannan kuma baki biyo bayan kirana ba?"

Phaty tace "Dan ALLAH kayi hakuri, Dad ne ya samu wani aiki nida Jiddah tun safe, kuma inaso na kiraka amma banda lokaci coz aikin ba karami bane shiyasa"

Murmushi mai ciwo Umar yayi yace "Dan ALLAH yaushe zaki daina yima mutane karyane da rainin hankalinki?"

Juya idanuwa Phaty tayi tana kallansa tace "Wannan wani irin magana kake fadamin?, nifa yau naga take takenka da fada kazo dan haka please ka bari mu rabu lafiya coz ya banajin hayaniya"

PHATEENJIDDAHWhere stories live. Discover now