page 49

116 7 0
                                    

Abun dai ba wuya yau bikin Phateenjiddah sauran kwana biyu kacal, yayinda suka nuna su baza suyi duk wasu bidi'o'i da akeyi a biki ba sundai ce zasuyi walima dan godewa ALLAH subhanahu wata'ala, shirye-shirye kawai ake dan ba karamin abubuwa akeyi ba, gaba daya anguwar ta bade da kamshi, suko amare an killacesu waje guda ana basu wata irin kyakykyawar kulawa ta musamman dan idan ka gansu zakayi tunanin bakin labarawane sukazo gidan basu ba dan ba karamin haskee fatarsu tayi ba da kyau da sheki, ko kadan ba a barinsu fita tun lokacin da bikin ya ragr sati daya sukayi ban kwana da fita, dan wata kwararriyar mai gyara amarya aka dauko musu daga sudan ta kware  kwarai wajan fanni ciki da waje na amare, kai gana ganinsu kaga amare dan sun fita daban wajan al'ummar wajan, mutanene kota ina sunata faman kewaye gidan kana ganin gidan Alhaji Abdul-aziz zakasan lallai ana sha'ani a cikin gidanshi dan mutane makil agidan sai kace yaune daurin auren.

Dija kuwa tana nan a asibitin babu laifi jikin ya fara samun sauki amma agaskiya Dija bazata taba dawowa yadda take daba dan fuskarta gaba daya ta kwaile gashi likitoci sunyi kokarin daidaita fuskar danta dawo ko yaya take amma ina abun ya faskara sbd fatar jikinta tayi laushi da yawa sanadiyar man bleaching din datakeyi yasa fuskarta baxata taba dawowa daidai ba

_(Mata ayi hattara man bleaching dinnan illa yake mana amma mun dage mun kuke sai munyi haske, kowafa ya ganki yasan ba hasken ALLAH bane haskene na kanti na bleaching kikeyi, kina wuce jama'a aita nunaki ana fadin da idan kaganta kamar duwawu take amma kalleta ynx yadda tayi jawurrr, da kudin mai ya kare kaga tayi wani irin baki mara kyawun gani, soo yan mata da matan aure a farga fa dan maza sunsan komi wallahi saidai su kalleki, ALLAH yasa mu dace)_

Dija abun duniya ya isheta da wanne zataji da rashin fuskarta koda rashin zuwan Umar tunda aka kwantar da ita, goge hawayan fuskarta tayi ta kalli Hajiya Aina'u tace "Aunty yanzu ki duba a kalla zankai wajan kwana ashirin a asibitinnan amma Umar bai taba takowa yaga jikina ba, wannan waca irin kiyayyace Umar yake nunamin dan ALLAH, kuma na tabbata Alhaji ya sanar dashi dan agabana ya kirashi yana shaida masa bansan dai mai yace mai ba amma yasan komai wallahi"

Hajiya Aina'u wani dogon tsaki tayi tace "Wallahi tallahi baki da zuciya ko kadan, yanzu akan wannan shashashan kike faman damun kanki?, ai yadda yayi kamar baisan damu ba muma haka za muyi kamar bamusan dashi ba, keda kinyo zuciyata akace ki mishi kallan azziki zama kiyine mtseeeeeewwwwwwwww"

Dija kallanta tayi kamar kai nazari tace "To Aunty ya zanyi?, ALLAH ya kaddaramin wata azababbiyar soyayyarshi a cikin zuciyata ko da wasa sonshi baya raguwanmin wallahi saidai ya ninku ma, kedai ki tayani da addu'a ALLAH ya yayemin wannan san nashi inba hakaba wallahi akwai matsala"

Hajiya Aina'u tace "Karki damu kanwata insha ALLAHU san Umar da kikeyi saidai ya zama tarihi"

"Uhmmm" kawai Dija tace, dan tasan koda san Umar zai fita a cikin zuciyarta to gaskiya ba a wannan karnin ba dan san Umar tamkar a jininta yake, komawa tayi ta kwanta ta lumshe ido tana hango rayuwar da zasuyi da Umar inhar ya aureta.

Aina'u tabe baki tayi tana faman mita akan inzata cire Umar a ranta gwanda tun wuri ta cire dan tasan Umar koda wasa bazai taba santa ba har abada.

Umar ne ke kwance kan makeken gadonsa sai faman zabga tsaki yakeyi a karo na ba adadi, daukan wayar ya karayi ya kira Phaty amma stil ba'a dau wayarba, Jiddah ya kira itama duk ansar dayace, tsaki yayi mai karfi ji kike "Mtseeeeewwww ni wallahi banga amfanin wannan gyaran ba, dacan ai ba gyara naganta kuma nace inaso amma za'a wani kafa musu dokar karsu dau wayar kowa dan wulakancima harda wayana nida zan aureta wallahi wannan iskancine kawai, itama Phatyn zamu hadu da ita ko satar hanya bazatayi ba ta kirani mu hadu amma ta waniyi burus ta shareni sai faman dakon santa da kaunarta nakeyi, nidai gaskiya ba'a kyautamin ba kuma ba aimin adalci ba ko kadan yau sauran kwana  biyu kacal ta zama matata mallakina amma an hanani na ganta, aiduk ita taja ma da sun yarda za'ayi partynnan ai dole su fito ko anaso ko ba'aso, wallahi idan har suka bari mukai ido hudu da ita to wallahi an gama gyarannan haba dan ALLAH" kara tafka wani uban tsaki ya karayi yace "Uhmm zaki sani wallahi zan kamaki ne a hannu zaki fadamin yaya gyaran yake" tuni zuciyarsa tace _"Ka manya da Aunty Fa'iza ne?"_
Da karfi Umar yace "Yessssss" ya dauko wayarsa yana neman layin Fa'iza, ringing daya biyu aka dauka, tuni Umar ya sauke ajiyar zuciya kamar Phatynce ta dauka.

PHATEENJIDDAHWhere stories live. Discover now