Page 8

126 9 1
                                    

*PHTEENJIDDAH*

*MALLAKAR*
*_Ƴar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
 
   *Please Subscribe My Channel*

https://www.youtube.com/channel/UCWyfuDW1EWCBqzOrwaCnq3Q
  Domin kawu muku Audion littattafan Hausa

     
                             8

"Dan ALLAH ki dawo zamuyi maganane", cewar Umar, Phaty banza tayi dashi ta cigaba da tafiyarta, Umar dayaga Phaty batada niyyar saurarnsa, ya fincikota, yasata a seat d'in mai zaman banza, ya rufe k'ofar, ya zaga ya zauna a driver seat, Phaty zazzaga masifa take akan ya ijeta inda ya ganta, amma yayi banza da ita, juyowa tayi taga ita yake kallo, kallansa tayi sama da k'asa tace

"malam bud'emin k'ofa tun muna shaidan juna kafin na tara maka jama'a a wurinnan".

Kallanta yayi a tsanak'e yace, "Phaty mai yasa kike hakane wai?, kefa ba k'aramar yarinya bace ke, so please ki tsaya muyi magana ta fahimta, saiki tafi abunki".

Wani kallo tayi masa wanda ke nufin kama rainama kanka wayo, tace "Kaga tunda sauran mutuncika a idona ka bud'emin k'ofa, idan ba haka ba zannuna maka ainihin fuskata, please ka barni na fita". Sosai maganar ta bashi dariya, dariya kawai yake, dariyar ba k'aramin kyau ya k'arayi ba, gabantane ya fad'i a cikin ranta tace, _"anya wannan mutum ne kuwa?, wannan kyan nasa yayi yawa, ina ganina mace mai kyau mai class, amma dana tsaya agaban mutuminnan saina raina kaina, ALLAH ka rabani da wannan bawan naka lafiya"_

Maganarsace tadawo da ita haiyacinta, "Bakison ki fitane shiyasa, da kinason fita aida tuni kin saurareni kowa yakama kansa".

"Hmmmm inajinka kayi sauri ka fad'amin dan inada wurin zuwa, kuma jirana akeyi tun d'azu wancan banzayen sojojin suka 6atamin lokaci"

"Phaty ina zakije haka?"

"ikon ALLAH ina ruwanka da inda zani kuma?"

"party zaki ko?, partyn k'awarki Amin's koba haka ba?, Phaty dan ALLAH mai yasa kikeson 6ata rayuwarkine?, mai yasa?, iyayanki sun baki tarbiya nargarcacciya amma mai yasa kikeson bad'a masu k'asa a idone?, whyyy?".

Phaty sakin baki tayi tana kallansa, acikin zuciyarta kuwa fad'i take _"tabbas wlh na yadda bada mutum nake zaune ba, tayaya zaisan abubuwa da dama akaina, alhalin ban ta6a ganinsa ba,"_
nan take tsoro ya mamaye mata cikin zuciyarta, amma da yake ta iya barikanci saita dake, tace mai,

"Oh dama bibiyata kakeyi bansani ba, wai malam dakata ina ruwanka da harkata mawai?, idan iyayena suka gane meye naka a ciki?, kuma inna mutum tare za a binnemu ne kake tsoron kar laifina ya goga naka?, kasani fa, bawa shida ubangijinsane bawai da mutum ba, please karka k'ara shiga sabgata inhar wannan maganganun zaka rink'a yiminun kaji ai"

Kallonta kawai yakeyi cikin zuciyarsa kuwa fad'i yake _"lallai inada aiki agabana Phaty tayi mugun nisa batajin kira, amma nasan ta hanyar da zan biyo mata"_
"Kadaiji abunda na fad'a maka ai". Ajiyar zuciya yayi wanda har ita Phaty saida taji, murmushi yayi mata wanda ke kashe 'yan mata, yace mata,

"kai Phaty daga wasa, naga kin d'au abunda zafine, kinganni nan, nima mugun d'an a hutane, party baya wuceni, bari na fad'a maki nifa idan zan had'a partyna, bana na k'ananan k'wari, saboda ni ba a nigeria nake had'a casuna ba, k'asashen waje nake fita na had'a partyna, hope duk ranar danai inviting d'inki zaki ansa goron gayyatata,". Ya kashe mata ido d'aya tare da d'aga gira, kallonsa tayi sama da k'asa, acikin zuciyarta tace, _lallai guy d'innan d'an hutu ne, komi na jikinsa mai tsadane, bana tunanin maganar daya fad'amin k'aryane coz komi nashi na manyan masu kud'ine, idanfa na jone dashi girmana zai k'ara k'aruwa zan zama babbar mace, kuma zan k'aro wulaqanci, gashi da kyau ga kud'i samun irinsu a bubariyyannan zansha wahala fa, gashi ALLAH ya kawomin tsuntsu gashashshe har gida, amma fa dole naja masa class._

Umar yace,"Yadai naji kinyi shirune?"

Phaty tace, "inajinka"

Umar yace, "ko zan iya samun number d'inki?"

Yatsina fuska tayi tace, "Wayana na barota a gida". Jakanta ya d'auka, tace, "please karka bud'emin jakana dan ALLAH kabani zan baka numbern"

"To maye a jakan da bakiso a gani?, kuma saina bud'e, bani zakima rowan number ba"

Marairaice fuska tayi tace , "dan ALLAH kabani jakana wlh zan baka numbern".

Shiru yayi yana nazarin to maiyasa batason abud'e mata jaka?, anya yarinyarnan tana da gaskiya kuwa, zuciyarsa ta raya masa cewar _"kasani tana yawo da tablet din hana d'aukar cikine,   shiyasa batason gaka abunda yake ciki,"_ take jikinsa ya fara rawa baisan lokacin daya bud'e jakar ba, always (pad) yayi karo dashi, sai kayan kwalliya, sweet, cingum da kuma waya da kudi, gaba d'aya saida ya ciro kayan, ya duba yaga ba komai, ajiyar zuciya ya saki mai k'arfin gaaske, ita kuwa tunda taga ya fiddo always ta saka kanta cikin cinyoyinta tanata jero masa ALLAH ya isa, domin kuwa yasata jin kunya over, sweet d'aya ya 6are yana sha, ya maida mata komi na cikin jakarta banda wayarta, shi sam bai lura da yanayinta ba, d'agowa yayi yace "to me kike 6oyewa a jakarne da bakison agani,?" danshi bai maida always abunda za a 6oye ba, kar6e jakarta tayi, tace "naga alama baka da kunya, kalli yadda kake d'aga pad sai kace abinci,"

Mamakine k'arara a fuskansa dama akan always ta hanani jakarnan, kai yarinyarnan tana da fuska biyu, amma insha ALLAHU sai naga d'ayar fuskar, yak'e yayi mata, yace, "dama akan wannan abarne kika hanani, ohh kice period kikeyi"

Phaty narai-narai tayi da idanu "please kabari banaso dan ALLAH ba danni ba" Sosai abun ya bashi mamaki, "waccan k'ananan kayanfa nawaye?, kona zuwa partynne?," Banza tayi dashi, ya d'au wayarta yaga akwai password, yace "wayar mara gaskiya dole saida password fad'amin password d'in"

"banna bud'ee maka dai"

"a'ah saidai ki fad'amin konai maki d'ai-d'ai da pad d'inki"

tsaki tayi a hankali tace kasa _Allahu_. sosai maganar ta bashi dariya, yace "kina tunanin bazan iyaba kenan, barima ki gani, k'ok'arin zage zip d'in jakar taga yanayi, tace, "wlh ALLAH da gaske nake maka ka gwada kagani mana"

Bai mata magana ba ya saka password d'in saiko yaga ya bud'u, sosai yayi mamakin ganin application d'in addini a wayar, duba contact d'inta yayi, memakon yaga numbers da yawa sai yags akasin haka, hasalima batada numbern wani namiji aciki, dama ta musty take da ita yanzu kuma sunyi baram-baram ta goge, numbers d'in dayagani a wayanta baiyi tunanin haka zai gani ba, wayanta baida matsala ko kad'an ya fad'a. gyaran murya yayi yace mata,

"Ina d'ayan wayan naki?, nasan wannan ne wayar cikin gida, ina wayar outside d'inki take, banaso nasa maki numberna anan"

"kamar yaya, aini wayana d'aya, kasamin numbernka anan kawai"

Kallanta yayi yace "kin tabbata ba matsala insa anan?"

'Daga masa kai tayi, tace "aiba kowa nake ba numberna ba shiyasa"

"Owk to nagode da wannan karramar taki, wani suna zan saka maki?"

"kasamin sunanka zan gane"

"a'a bazan saka maki sunana  ba, za6a zakiyi".

"to kasamin friend shima zan gane"

"friend kuma?, friend kika kaini?, please canzamin wani sunan"

"idan bai maka ba to kayi saving numbern kawai zan gane, na fad'a maka jirana akefa"

"karki damu ai zan kaiki" mik'a mata wayar yayi, yace gashinan zakiga ansa best friend itace numberna"

kar6a tayita saka a jaka, tace nagod....
wayanta ne ya katseta da abunda zatace, amin's tagani a jikin screen din wayar, d'agawa tayi tace "hello beb, kiyi hak'uri wlh matsala na samu a hanya amma insha ALLAHU gani nan very soon". Shiru tayi tana sauraranta, tace "owk yanzu kuna hotel d'in kenan, ba damuwa yanzu zan taho please kiyi hak'uri.

PHATEENJIDDAHWhere stories live. Discover now