Page 14

117 6 0
                                    

Yana fita Phaty tai dogon tsaki tace, "mayaudari kawai" sai kuma ta fara rera kuka, sosai abunda Umar yayima Phaty ya ta6ata, kuka kaWai take, tace, "ALLAH ka sakamin abunda wannan bawan naka yayimin, ALLAH na tuba ka yafemin kurakuraina, astagfirullah, astagfirullah, ALLAH ka shiryeni, shirin addinin islama," sosai Phaty take kuka, nan take zazza6i ya rufeta, zazza6i mai zafin gaskene ya kamata, muryanta ya dashe sosai, gashi bata gani sosai, kasancewar tasha kuka harta godewa ALLAH, a daddafe ta tashi ta fara tafiya dak'yar, dak'yar ta isa cikin babban falon, tafiya kawai take, amma kukan zuci take, aunty fa'iza ce ta sauko taga yanayin da Phaty take, tace "subhanallah, daugher maiya faru haka?, keda waye haka?", Phaty da gudu ta fad'a jikin aunty fa'iza ta fara rera kuka, kuka kawai take aunty fa'iza ta rud'e matuk'a, jan Phaty tayi ta kaita cikin bedroom d'inta, still Phaty bata daina kuka ba, aunty fa'iza gyaran murya tayi tace, "Ya isa haka kukan, ki natsu ki fad'amin abunda ke damunki, sannan kuma ina bak'on da kikacemin yazo d'azu?, Phaty kimin shiru nace, kima ALLAH ki fad'amin abunda ke damunki, waittt me bak'onnan yayi maki?". Sosai aunty fa'iza ta had'e giran sama da k'asa, ta k'ara cewa "Ke! kimim magana uban me wannan guy d'in yayi maki, wlh tun muna mu biyu ki fad'amin ko ranki ya 6aci"

Maganar aunty fa'iza ta daki zuciyar Phaty ba kad'an ba, a zuciyarta fad'i take _"hmmm itama kenan inaga wani, ta maidani mace mara kamun kai, idan har ta yadda dani, ai ko wani hali ta ganni bazata ta6a zargin cewa ni 'yar iska bace, me aunty fa'iza take nufi da hakan, ban ta6a dana sanin rayuwata ba sai yau, dama haka ake kallon mace mara kamun kai?, koda ita ba 'yar iska bace tana abu na marasaji, haka mutane zasu tanbarata da cewar ita 'yar iska ce, ALLAH kaine shedata"_

Aunty fa'iza ce ta katse mata tunaninta tace, "watoma kin maidani y'ar iska, ina tambayarki kinyi iskar kare dani"

Cikin sanyin murya Phaty tace "ba haka bane aunty kawai mun samu misunderstanding dashine, shiyasa kika ganni a haka coz ya 6atamin rai sosai..."

Bata k'arashe abunda takeson fad'a ba aunty fa'iza tace "k'arya kikeyi wlh, ni zaki maida 'yar iska, idan har baki fad'amin ba ai idan nakira mamanku ita zaki fad'a mata ko".

Mik'ewa Aunty Fa'iza tayi, tana k'ok'arin kiran waya, Phaty ruk'e hannunta tai tace, "please Aunty karki fad'a mata kinsan halin Momy, zan fad'a maki dawo ki zauna" Sosai muryar Phaty ke rawa, zama Aunty Fa'iza tayi tace "Uhmm inajinki fad'amin meke damunki, karkiyi tunanin kamar ina takura maki Phaty, ko kad'an ba takura maki nake ba, ke kanki kinsan da haka, banason ina ganinki cikin wannan halinne, nasan halin maza, shiyasa nake guje maki tsoron sharrinsu"

Phaty kallan Aunty Fa'iza kawai take, sosai take k'aunar Auntynta saboda tana matuk'ar jansu ajiki ba kamar momynsu ba, Aunty Fa'iza ta6a Phaty tayi tace "Fad'amin mana inajinki"

Nannauyar ajiyar zuciya Phaty ta saki, sannan ta kwashe komai, abunda ya faru tsakaninta da Umar ta fad'ama Aunty Fa'iza. Aunty Fa'iza ajiyar zuciya ta saki sannan tace "Bai maki adalci ba, kinga kuma abunda nake fad'a maki kenan, kikai uwar shegu dani, har gwara Jidda tanajin magana kece mai hure mata kunne, yaka mata gaskiya ki gyara don kuwa girma kikeyi, kuma tabbas da gaske yake yana k'aunarki, ba yaudara bace, kamar yadda kike tunani, yana sonki sosai a yanayin yadda kika ban labarinsa, dole kiyi taka tsan-tsan dashi, kuma inaso ki nuna masa kuskuransa akan abunda yayi maki, idan ba haka ba haka zai runk'a yi maki, har sai randa zai tabbatar da cewa ke ba 'yar iska bace, idan hakanma ya faru kenan, ki tashi kije ki wanke fuskarki, sannan kuma kije kiyi break fast d'inki bana tunanin kinyi, gashi yanzu har sha biyu da rabi"

"Aunty na k'oshi coz ya kawomin abinci naci d'azu ,please paracetamol kawai zaki tai makeni dashi, maybe nai bacci" cewar Phaty. Aunty Fa'iza mik'ewa tayi tace "bari naje na duba box aid ko za'a samu, zanba aarif ya kawo maki, ki tabbatar kinsha coz zazza6i ya kamaki da ciwon kai, kinji ai"

Kwantawa tayi akan gadon tare da lumshe idanunta, kamar ance Aunty Fa'iza ta fita wayar Phaty ta fara ruri, tana duba sunan, taga sunan Umar ne bayyane akan screen d'in wayar, tsaki taja sannan tai rejecting d'in call d'in, tanayin rejecting ya k'ara kiranta, a silent ta saka wayar ta cillar da ita, sosai Umar yake bata haushi, don a halin yanzu ta tsaaneshi, tsana ba 'yar kad'an ba, lumshe idanuwanta tai taji ana knocking d'in k'ofa, "Yes come in" cewar Phaty dan tasan magani aka kawo mata, aarif ne ya shigo d'akin yace "Aunty wai ammi tace ki tabbata kinsha,  gashi, bari na mik'o maki ruwa a cikin fridge"

"Uhumm" kawai Phaty tace don kanta ya fara yi mata ciwo ba d'an kad'an ba, tana shan maganin bacci yayi awan agaba da ita.

A 6anagaran Umar kuwa hankalinshi inyayi dubu to duk sun gama tashi, Sosai ya shiga tashin hankali, ya rasa mai zaiyi yaji dad'i, safa kawai da marwa yake ta faman zabgawa a cikin makeken falonsa, sosai ya kasa natsuwa, a k'alla ya kirata yafi sau d'ari, ya tura mata da messages yafi k'arfin arba'in amma duka no respond, yana cikin yanayinnan ne Jafar ya shigo, tunda yaga yanayin Ogansa yasan lallai ba lafiya ba, yana ganin Jafar yayi saurin k'arasawa wajansa yace "yawwa Jafar please zokajemin gidansu Phaty, wacca aka nuna mana gidansu tare dakai, plz kaje yanzu kaji, kaje kaga a wani hali take ciki, plz karka nuna mata cewar kama sanni, jeka kawai, kad'au key d'in waccar motar kawai, plz duk yadda kukai, ka kirani ka fad'amin kafin ka dawo" Umar magana kawai yake ba tsayawa don kuwa sosai hankalinsa ya tashi.

Sosai jafar yayi mamaki, _"to mai kuma ya had'asu haka"_ cewar zuciyar Jafar, yana cikin tunaninne Umar yace "kai sauri kaje mana, mai kuma kake jira, kaje kawai, ina jiranka"

Haka jafar ya saka kai ya fice bai zarce a ko inaba sai gidansu Phaty, dak'yar ya samu getman ya barshi ya shiga, yana shiga ya samu akaimai sallama da ita, zuwa akai aka sanar mai batajin dad'in yanzu hakama bacci take, godiya yayi ya juya ya shiga motarsa, yana shiga ya kira Ogansa ya shaida masa abunda akace mai, Umar cewa yayi "Wait kace kanason magana da itane, magana mai muhimmanci zakuyi, dan ALLAH karka fito a gidan saikun had'u dan ALLAH Jafar kaimin wannan alfarmar,"

"Oga aika wuce haka aguna, bari na k'ok'arta maka" cewar Jafar, "Yawwa Jafar godiya nake" katse wayan Umar yayi, ya rungume hannunsa a k'irjinsa zafi kawai yakeji a cikin zuciyarsa, _"Naima kaina"_ ya fad'a a cikin zuciyarsa. Jafar haka ya k'ara aikawa, still ansa d'aya ce, Jafar yace, "baba kayi hak'uri dan ALLAH inata sakaka aiki, inba damuwa kace ina neman izinin shigowa cikin gidan, kayi hak'uri dan ALLAH"
   "ba komai d'annan" cewar baba maiba shukoki ruwa, haka ya shiga yaje ya shaida ma, Aunty Fa'iza cewar "bak'on dake neman Phaty yace Idan ba damuwa yana neman iso, wato aimai izinin shigowa"
   Aunty Fa'iza tace "ya shigo mana, ba damuwa," haka baba yaje ya shaidawa jafar, Jafar godiya yayima baba, ya ciro 10k ya bashi, godiya baba yayita zabgamai yana mai fatan alkhairi, Jafar shiga ciki yayi, ya shiga main palor, zama yayi, akan kujera, zamansa keda wuya saiga 'yar aiki ta kawo masa drinks da snaks kala-kala, tafiyar 'yar aiki keda wuya Aunty Fa'iza ta shigo, cikin sakin fuska Aunty Fa'iza ta tarbeshi, sannan tace "gashi kuma ban shaidaka ba"
Sosa k'eya jafar yayi yace "dama ni friend d'in Phaty ne na skul, to shine naji labarin tazo abuja, shine nace bari nazo mu gaisa da ita, sai kuma akace batajin dad'i, na d'auko ko batasan fitowane tacemin haka, shiyasa nace aimin iso na shigo ciki naji gaskiyar lamari"

Aunty Fa'iza tace, "Ayya ba haka bane friend d'in daugher, wlh batajin dad'i sosai, zazza6ine ke damunta da ciwon kai mai tsanani amma bari na duba maka ita naga ko zata iya tashi, sai tazo ku gaisa" mik'ewa tayi ta shiga ciki dan zuwa d'akin Phaty, tana nan inda take, baccin wahala kawai take, Jafar kuwa Aunty Fa'iza tana ficewa ya d'au waya ya kira Umar ya shaida masa yadda sukai da Aunty Fa'iza, Sosai hankalin Umar  ya tashi yace "In kun gama da Auntynta ka taho kawai, ka ansomin numbern Aunty fa'izar daga nan plz Jafar"

"Baka da damuwa, insha ALLAHU zanyi abunda kace" Aunty Fa'izace ta taho, tace "wlh har yanzu bacci take, kuma kaga ba dad'i na tasheta"
  Jafar yace "ba damuwa Auntynmu bari naje, aunty inba damuwa numbernki zaki ban" haka aunty fa'iza ta bashi numbern nata, "idan ta tashi ai mata sannu," cewar Jafar, zaro kud'i yayi a aljihunsa shi kansa baisan yawansu ba ya ije akan center table yace "gashi a siyama yara sweet" bai tsaya jiran ansarta ba yayi saurin ficewa a falon

PHATEENJIDDAHWhere stories live. Discover now