*PHTEENJIDDAH*
*MALLAKAR*
*_Ƴar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
47Suna zuwa saitin Phaty sukaja wani wawan birki kafin ta ankara sun fincikota sun sakata a mota sun tada ita, wannan abunda ya faru duk a idon Umar ne dan kuwa sunada tazara a tsakani kuma kafin yayi wani yunkuri sun gudu, ranshi a bace yaja motar yabi bayansu, gudu sukeyi shina gudu yakeyi, yayinda Phaty take neman agaji taba ihu tana bubbuga motar amma ina babu maijinta kuma babu mai ganinta kasancewar bakin glass ne a jikin motar.
Basu zarce da ita ko ina ba sai wani dan madaidaicin gida dake cikin G.R.A, dan su basu san ana binsu a baya ba ko kadan, Horn sukai, mai gadi ya bude musu da gaggawa, sannan suka tura motarsu ciki, mai gadi yana kokarin kullewa sai yaga wata motar ta danno kai, haka ya tsaya har Umar ya shigo sannan ya fita ya kulle musu get din kamar yadda suka umarceshi yayi tafiyarsa, Ahuta ne ya fito yana karkada key a hannunsa yana dariyar jin dadi data mugunta, yace "Kb fito mana da cikar nan"
Tuni Kb ya fito da Phaty tana faman tirjewa tare da yi musu magiya akan su barta ta tafi, Umar ne ya fito ransa a jagule tare da wani katoton belt ga dukkan alamu na sojojine ya fara shafdawa Ahuta a bayansa, tuni wajan ya kumbura kamar wanda aka daka da dutse, Phaty waigowa tayi taga Umar ne ta tafi a guje tai hugging dinsa tana faman sauke ajiyar zuciya, kirjinta kuwa sai bugu yakeyi, kankamesa tayi kam a jikinsa, Umar tureta yayi ya kama Ahuta da Kb yayita jibga kamar an aikosa, suna ihu suna masa magiya akan yayi hakuri amma yaki ya hakura, bubbuga get din gidan ake, Umar ya kamo hannu Phaty ya sakata a bayan motarsa yace ta kwanta tai bacci, tuni Phaty ta rufe idonta sbd yadda taga Umar ransa a bace yake, zuwa yayi ya bude get din, aiko saiga sojoji wajan su goma ko wanne da abun horo a hannunsa, Umar kallansu yayi suka sara masa, sannan yace "Inaso ku horamunsu dakyau, kuma inaso suyi laushi yadda ko ance suyi wani abu da ba daidaiba bazasuyi ba, sannan karku sake ku daga musu kafa, karku basu uziri, wayoyinsu ku anshe ku kashesu, ku tabbatar sai sunyi 2weeks a hannunku, kuma inaso idan na tashi ganinsu inga na kasa ganesu, ku kwashesu ku kaisu barrack"Tuni suka tabbatar masa da angama, motarsa ya nufa ya bude ya shiga ya tada ita yabar gidan, zuciyarsa gaba daya a dagule babu dadi haka yakejinsa, waigawa yayi bayan mota yaga Phaty tana kwance kamar yadda ya umarceta saidai kana ganinta kasan ba bacci takeyi ba runtse idanunta kawai tayi, kuma a tsorace take matuka, kallanta yayi sai yaji yanajin haushinta, cikin murya mai kama da fada ya umarceta data dawo gaba, babu musu ta tashi ta dawo gaba jikinta na faman rawa, bai kalle inda take ba yaja motarsa, bai zarce da ita ko ina ba sai gidansu, saidaya tabbatar ta shiga gida sannan yaja motarsa ya wuce zuciyarsa babu dadi ko kadan.
Phaty tana zuwa taga babu kowa a falon, hamdala tayi ta fada bedroom dinsu, tuni ta kwanta akan gado tana faman sauke ajiyar zuciya, kirjinta kuwa dai harbawa yake, runtse idanuwanta tayi sai taga hoton Umar ransa a bace, a hankali ta furzar da isakr bakinta tace "ALLAH ka taimakeni, ga dukkan alamu ran Umar a bace yake, su Ahuta zasu janyomin wata tsiyar, inajin dadi komai nawa yana tafiya yadda nakeso amma sunzo sun batamin wannan moment din nawa" Daukan wayarta tayi tana kiran Umar amma no answer, ta kirasa akalla zaiyi so goma amma bai dauka ba, jiki babu kwari Phaty ta tashi taje ta watsa ruwa dantaji dadin jikinta.
Dija ce tsaye a harabar gidan ta kasa zaune ta kasa tsaye sai faman safa da marwa take tana jiran Umar ya dawo amma tajishi shiru, duba agogon dake hannunta tayi taga karfe tara da rabi na dare, kafin ta dago tuni motarsa ta danno kai tana dubawa taga shine nan take tayi ajiyar zuciya ta karasa wajansa cikin sauri tana mai sannu da zuwa.
Umar ko kallan inda take bayyi ba yana kokarin kulle motarsa yaje ya kwanta ko zai samu sauki.
Dija sai karamai sannu da zuwa take taji shiru babu ansa, cikin shagwaba tace "Haba yaya, ina maka magana kayi banza dani"
YOU ARE READING
PHATEENJIDDAH
ActionYana maganane akan yara guda biyu Wanda suka kasance tagwaye, gashi Allah yayi musu rashin basajin magana ko kadan, sannan kuma ina gargadin iyaye da su runka jan 'yayansu a jiki basu wancakalar dasu ba akan wani dalili nasu na daban,👭