page 27

91 6 1
                                    

~_Wannan page d'in nayishine ga dukkan d'aukacin masoyan littafina, ina matuk'ar jin dad'in comment d'inku agareni, godiya ba adadi, ina k'aunarku masoyana_~






Yanayin yadda Phaty take da kanta ne yasashi cewa "Lafiya?", dafe kanta kawai tayi dan ta kasa yi mishi magana, idanunta kuwa sun kad'a sunyi jajir, d'ago kanta tayi ta dubesa nanfa yaga idanunta sun sauya kala, Umar yace "Phaty wai meke damunki ne?"
Ahankali tace mai "dan ALLAH kaimin addu'a akaina, kaina ciwo yakemin kamar zai tsage", haka Umar ya kama mata kai, nan take bacci yayi awan gaba da ita, bacci kawai takeyi, Umar kallanta yayi yadda takeyin bacci ga dukkan alamu ko kad'an baya mata dad'i, gyara mata kwanciyarta yayi akan cinyarsa ya cigaba da tunanin abunda ya had'a Phaty
da Aina'u, cikin zuciyarsa fad'i yake _"To wani irin magana Aina'u take nufi akan Phaty sai tayi datasanin sanina a rayuwarta, ALLAH ka dubeni kar a cutar da Phaty ta sanadiyata, ALLAH ka tsareta da tsarewarka"_

Motsin da Phaty ta farane yasashi dawowa daga duniyar tunaninsa, kallanta yayi yaga har idanunta ya washe kamar ba d'azu sukayi ja ba, murmushi ya sakar mata yace "Wannan wani irin baccine na 'yan sakonni?, aina d'auka kika fara kuma sai dare kinga yau ba batun tafiya kenan"

Murmushi taimai tace "Ya za'ai na hanaka tafiya?, ai yau insha ALLAHU zakaje garin lagos"

Kallanta yayi yace "ALLAH ya yarda, saidai tafiyar bazataimin dad'i ba tunda bake, ko zakizo mu tafine?"

Phaty kallansa tayi cikin zumud'i da d'oki tacemai "Dagaske kake inzo muje?"

Dariya Umar yayi yace "Kiyi zamanki abunda nasan konan da airport bazaki rakani ba"

Phaty tace "Wlh da gaske nake, in zaka dani zani"

Kallanta yayi nad'an wasu dak'ik'ai, yaga kamar fa da gaske take zata bishi, wata zuciyar kuma tace raina maka wayo kawai zatai sai kace bakasan Phaty ba, kallanta ya kumayi yace mata "Bashshi na yafe, bana buk'ata, abunda ba dad'ewa zanyi ba zan dawo, ina dawowa zan kasance dake, kingama saimu fara shirin bikinmu ko?"

Murmushi tayi tace "To shikenan tunda baka buk'atata, saidai nace ALLAH ya kaika lafiya ya dawomin dakai lafiya"

Umar cikin jin dad'in addu'arta ya ansa da "Ameen thumma ameen gimbiyata, yaka mata azo aimin hug and kisses na ban kwana", Umar duk atunaninsa yana tsokanantane dan yasan bazata iya ba,   kafin ya gama tunaninsa yaji Phaty tayi hugging d'insa tare da hot romance, romancing d'insa kawai take, Sosai Umar yayi mugun mamaki, but yanayin yadda ta kashe mai jiki ya biye mata shima, tun suna tsaye suka fad'a kan kujera, sosai suke bawa junansu love, Umar kuwa harya fara goce hanya, amma yaga Phaty bata hanashi ba, abun yaba Umar mamaki dukda yanayin dayake ciki, k'arar wayarsa ce ta katse musu abunda sukeyi, dak'yar Umar ya d'au wayar ya kara a kunnansa "Owk" kawai naji yace ya ajiye wayar, cikin wani irin yanayi mai wahalar fassaruwa suka shiga dukkaninsu, Umar kallan Phaty yayi da idanuwansa da suka soma canza kala yace mata "Sweetheart let me go, wlh ana jirana, but ina tunaninma yau zan juyo bazan kwana ba insha ALLAHU, please ki kulamin da kanki, nd thank you so much"

Phaty kallansa tayi tace "Shikenan kaima ka kulamin da kanka please, sai munyi waya kenan"

Cikin sauri Umar ya fita yaje ya samu driver d'insa yace "Mu wuce gida na manta da wasu takaddu acan"
Guy d'in yace "Ohk sir", haka ya shiga suka fara tafiya, abunda ya faru tsakaninsa da Phatyne ya fara dawo masa, sosai yake mamakin Phaty ayau, dan har yanzu ya kasa yadda da gaskene ba mafarki yake ba, a haka har suka isa kofar gidansu, cikin sauri ya fita daga motar, ta bayan garden ya shiga kasancewar a d'akin dad d'insa zai d'au takaddun, sauri kawai yake kar lokaci ya k'ure masa, Maganganun dasu Dijane sukasa Umar tsayawa cak batare da yayi wani motsi ba, Dija kuwa fad'i take "Aunty ai insha ALLAHU mallakar umar kamar anyi angama, saiya dawo tafin hannuna, in juyashi lokacin danakeso"

PHATEENJIDDAHWhere stories live. Discover now