page 29

98 6 0
                                    

*PHTEENJIDDAH*

*MALLAKAR*
*_Ƴar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
 
 

     
                             29

K'ara duba screen d'in wayar yayi yana nanata sunan, "Aminssss kuma?, to maye had'in aminss da zuwa lagos?, itada na tabbata tana kaduna, amma bari na kira naji" Daukan wayar yayi, ya kira numbern amins amma ba'a d'auka ba no answer, ya kira amins yafi k'arfin so goma amma ba ansa, hankalin Umar ya fara fashi kasancewar dare yana tayi, bai gaji ba ya k'ara kiran wayar, nan take yaci sa'a an d'auka a daburce ya fara magana yana fad'in "Amm dan ALLAH da amins nake magana?"

Muryar wani saurayi yaji yace mai "Amins tana ciki, wayan na hannuna ne shiyasa,"

Umar yace "dan ALLAH yanzu kana wani garine?

Saurayin yace "Muna garin lagos, wani chasu boyfriend din amins  ya had'a mata, so shiyasa muma tai inviting d'inmu, halan kaima kana cikin wa 'yanda aka gayyata?"

Umar cikin rawar murya yacemai "Ah, ah, ina ciki so na rasa wurarenne gashi nima ina cikin lagos d'in"

Saurayin yace "Ayya, ba damuwa, kasan emission club?"

Umar yace "Wallahi bansanshi ba, amma inajin sunansa, please kozaka iya yimin kwatance dakyau?"

Saurayin yace "Badamuwa, yanzu kai kana inane?"

Umar yace mai "Ni yanzu haka ina complacency hotel"

Saurayi yace "kagama ai abun yazo da sauki, ina cikin shopping mall din hotel d'in ka fito kawai ka sameni a parking space"

Umar yanajin haka ya katse wayan cikin 'yan mintuna wanda bai wuce uku ba yaje gun parking space d'in, kiran saurayin yayi yace "Gani a wajan, ina jiranka"

Ba ad'au lokaci ba saurayin ya bayyana, ba laifi yana da nashi kyan daidai gwargwado, yana zuwa suka gaisa, Umar yace "muje ko"

Saurayin gaba yayi Umar yana binsa a baya a wani makeken club sukai parking, umar bin gun yayi kawai da kallo dan duk mutanan wurin babu na azziki ko kad'an, tafiya suke tayi har suka isa inda ake chasun, babu abunda ke tashi sai kid'a, Umar kutsa kansa yayi ya shiga ciki, basu da yawa saidai babu mai shigar azziki, Phaty kuwa ta dage sai rawarta takeyi ita da wasu samari biyu d'aya a abayanta d'aya kuma agabanta sai tafi ake sharara mata dan Phaty ta k'ware wajan rawa, Umar sai raba idanuwa yake inda zaiga Phaty amma bai ganta ba, wata ya hango a tsakiyan maza sai zabga uban rawa take harga ALLAH bai kawo itace Phaty ba dan k'aramin siket ne a jikinta iya cinyarta dan kuwa ko gwiwa baikai ba sai kuma wata vest wanda hannu d'aya gareta kasancewar Phaty akwai gashi da gashin ya zubo bayanta saika rantse kace attach ne akanta, gashi tasha uban makeup kamar ba itaba, juyawar datayine  Umar ya ganta, sai yaga kamar idanunsane ke masa gizo ya za'ai Phaty tayi irin wannan shigar, Sosai Phaty take fuskantar Umar anan ne ya tabbatar da cewar itace, nan take kishi ya turnuk'esa Phatynsa ce a tsakiyan maza take rawa haka?, wanima harda ruk'e mata k'ugu, d'ayan kuma kamar zata fad'a jikinsa, runtse idanuwansa yayi, yana karanta "innalillahi wa inna ilayyir raju'un", bud'esu ya k'arayi yaga itace fa ba mafarki yake ba, a fusace ya k'arasa inda take ya fisgota tangal-tangal Phaty tafaryi kafin ta daidaita ya tsinka mata mari a kuncinta na dama ya k'ara tsinka mata mari a kuncinta na hagu.

Nan take wurin yayi tsit ana kallon ikon ALLAH, Amins ce tai k'arfin halin zuwa gun tace "Malam lafiya zakazo ka ruguzaa mana jin dad'inmu, ko mai tai maka ai baika mata kai mata haka ba, in banda rashin imani ina ruwanka da ita da zakazo kana marinta sai kace ubanta..."

Ai Amins bata k'arasa abunda takeson fad'a ba Umar yayi mata mugun kallo, nan take ta had'iye maganganunta, Umar kuwa ruk'o hannun Phaty yayi suka bar wajan, yana zuwa mota ya sata ya rufe ya zagayo ya shiga ya shiga motar shima, ba abunda kakeji acikin motar sai shashshek'ar kukan Phaty, ran Umar kuwa yayi mugun 6aci, a tsawace yace  mata "Ubanwa kikema kuka?, wallahi kimin shiru acikin motarnan konai miki dukan tsiya naga me cetonki" sassauta muryarsa yayi yace "kafin na fita me nace miki?, bana fad'a miki karki fita konan da can ba?, wato ga sa'anki shine kika kama hanya kika fita saboda kin rainanin ko Fatima?, wai mai yasa bakyajin maganane?, ki kalli kayan jikinki dan ALLAH sai kace ba 'yar musulma ba, kin shiga tsakiyan maza kinata faman zabga rawa wainan adole kin burge ko?, to kisani ke macece kuma watarn ke uwace yaka mata ki zamo mai gyara gobenki, dan lokaci tafiya yake baya dawowa har abada"

PHATEENJIDDAHWhere stories live. Discover now