*PHTEENJIDDAH*
*MALLAKAR*
*_Ƴar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
*Please Subscribe My Channel*https://www.youtube.com/channel/UCWyfuDW1EWCBqzOrwaCnq3Q
Domin kawu muku Audion littattafan Hausa
11Cikin nishad'i Phaty ta isa k'ofar gida, horn taita faman yi amma taji shiru, fita tayi a motar ta fara knocking, mai gadi kuwa tuni yayi nisa da baccinsa, kamar a mafarki yaji ana buga get d'in dak'yar ya taso ya bud'e mata get d'in, yace, "ranki ya dad'e dan ALLAH kiyi hak'uri sam na manta kincemin zakikai dare shiyasa na kwanta" Phaty tace, "ba komai baba, ai nicema na dad'e, kayi hak'uri na katse maka baccinka"
"babu komai 'yannan sannunki da dawowa""yawwa", shiga motar tayi ta shiga cikin gidan, a parking space tayi parking d'in motar ta fito, sosai take sand'a saboda batasan ta tashi mutanan gida, harta kai tsakiyan falob taji motsi, ad'an firgice ta juyo sai taga aunty fa'iza, yak'e tai mata tace "aunty fa'iza baki kwanta ba kenan", kallanta Aunty Fa'iza tayi dakyau tace "dama yau zaki dawo basai ankai amarya dake ba", cikin in-ina Phaty tace "wlh Aunty bansan ina kwana a wani wajen shiyasa nace komai dare saina dawo gida, amma danima aka kai amaryar". Aunty Fa'iza tace "shikenaan gobe kya nunamin hoton amaryar tamu, nasan kunsha dinner yau" Phaty batasan lokacin datace "iyyeeee" da k'arfi ba, sai kuma ta fara sosa k'eya, tace, "to Aunty fa'iza ALLAH ya kaimu goben dan yanzu wlh bacci nakeji, ai amarya ta gaji dakyau saima kin ganta", tuni Phaty tayi gaba, bata tsaya jiran amsar da Auntynta zata bata ba, tana shiga d'akinta ta wurgar da jakarta, towel ta d'auka, ta shiga bayi danyi wanka, tunanin gobe kawai take kar Aunty Fa'iza ta kamata, tsaki kawai tayi, ta cigaba da wankanta, alwala ta d'auro sannan ta shimfid'a dadduma don gabatar da sallahr ishsha, tana idarwa tayi shafa'i da wut'ri, addu'o'inta ta gabatar kamar yadda ta saba kullum na neman tuba, mai ta shafa mai k'amshin gaske sannan tasaka kayan baccinta, janyo wayarta tayi dan dubata sai taga wayar nata haske, dubawa tayi taga umar ne ke kiranta, batasan lokacin data saki wani k'ayataccen murmushi ba, d'aga wayar tayi ta karata a kunnanta, umar baisan lokacin daya saki wata ajiyar zuciya ba, sallama tayi mashi da muryanta mai sanyin gaske, kasa amsawa yayi yace "wlh kin tsoratar dani, na d'auka har yanzu baki dawo gida ba, inata kiran wayanki no answer, kuma naga dare yayi, bansani ba ko kin iya tuk'in dare, saifa haushin kaina nakeji da bani na kawoki gida ba".
Murmushi tayi mai k'ayatarwa tace, "wlh ba haka bane na dad'e da dawowa, abubuwa nayine kuma gashi wayana a silent take shiyasa, yanzu ma na d'aukotane naga tana haske, ina fatan yanzu hankalinka ya kwanta""Ai tunda kika d'aga wayan, sannan kuma naji muryarki hankalina ya gama kwanciya" muryansa k'asa-k'asa yace mata " i miss you so much" Dariya tayi tace, "yaushe muka rabu dahar ka fara missing d'ina?, kufa mazannan dama an fad'amin akwaiku da dad'in baki"
"Uhmm baki yadda ba kenan, ni bana cikin mazan da sukema mace dad'in baki abunda ke zuciyata kawai nake fad'a maki, nayi missing d'inki yadda bakya tunani wlh"
"Uhmm kawai Phaty tace domin kuwa yadda yake kashe mata murya harya fara kashe mata jiki"
_Niko nace su Phaty ke ko wani irin sak'o kar6ewa kikene_
Sosai Umar yake ta zuba mata plus masu tsadan gaske, tun Phaty tana amsa mashi yadda yaka mata, har ta fara shiru domin kuwa baccine ke fizganta ba d'an kad'an ba, gyaran murya tayi tacemai, "Friend wai bakajin baccine naga lokaci yaja, kuma nasan kagaji, yanzu k'arfe biyu da rabi fa na dare yaka mata ace ka kwanta"
"Au korata kikema ko"
"Noo ba haka bane wlh bacci nakejii karkanai maka bacci fa kayita faman magana kaji shirune shiyasa but ni ba korarka nai ba""Kinsan idan ina tare dake bana gajiya ko kad'an, nakan nemi gajiyar danake tare da ita narasa, na nemi rashin lafiyar danake dashi narasa, hakama baccin na nemeshi na rasane, duk ta sanadiyarki, karki damu ni banajin bacci, amma duk lokacin da bacci yazo maki karki hanasa kiyi kayanki kawai, batare da kinkashemin waya ba, kinji"
Uhmm kawai tak'ara cemai, domin kuwa bacci takeji ba kad'an ba, kalamai masu dad'in gaske yake zuba mata, tun tana iya respond harta daina, tuni bacci yayi awan gaba da ita, saukar numfashinta yaji a hankali a cikin wayar hakan ya nunamai alamun tayi bacci kenan, numfashinta take fitarwa a hankali, acikin zuciyarshi kuwa fad'i take _" wataran tare ma zaku kwana gaka ga ita, kuna nunawa juna tsantsar soyayya, na hango maka nasara a tattare da lamarinnan insha ALLAHU zaka mallaki Phatynka"_ cewar zuciyarsa, murmushi yayi mai k'ara bayyanamai kyawunsa yace "Insha ALLAHU komai zai tafi daidai da yardar ALLAH, i love you FA'DIMA love you lyk a crazy". kawai imaging d'in yadda rayuwarsu zata kasance dashi da Phatynsa yake, tashi yayi ya d'auro alwala dan gabatar da sallahr nafila, Sosai Umar yake addu'a idan har Phaty alkhairice agaresa ALLAH ya mallaka masa ita cikin sauk'i da salama, haka ya kwana yanata fama shauki.
_Gud nyt Umar da Phaty mu kwana lafiya lovers_
Asuba nayi Umar ya tashi, alwala ya d'auro dan zuwa masallaci, d'aukar wayarsa yayi ya kira abar k'aunarsa, ba'a wani 6ata lokaci ba ta d'aga, sallama taimai ya ansa yace mata, "Har kin taashi?" cewar Umar
Phaty tace, "Eh na tashi mana, kasan asuba tayi"Umar yace, "ai ban d'auka zaku tashi kan lokaci bane coz baki kwanta da wuri ba"
Phaty tace, "Na tashi wlh, sallahma zanyi naga kiranka"
Umar yace, "har lokacin sallahn yayi anan kenan?"
Phaty tace, "Ah mana harma sun tada wasu masallacanma"
Umar yace, "Nima bari naje masallaci amma dan ALLAH kina idarwa ki kwanta kar kanki yayi maki ciwo kinji"
Phaty tace, "To ba komai nagode da wannan kulawar taka agareni"
Umar yace,"Kin wuce haka, ki kulamin da kanki, sai anjima"
_Nima nace ohhhh Umar he's in love so much_
9:00AM
Wayan Phaty ya fara ruri dakyar tad'au wayan saboda baccin dake idanunta, "hello" tace cikin muryar maijin bacci.
"Sis baki da kirki wlh dama haka alk'awari yace?, tunda kikazo abuja baifi so uku mukai waya ba, kuma kince zaki runk'a kirana a k'alla so uku a rana, ainagani"
Tuni Phaty ta watstsake tace, "wlh Sis ba haka bane ansamu damuwa amma insha ALLAHU yanzu komai normal, kiyi hak'uri kinji Sis i apologize"
Jidda tace, "dama nasan haka zakice, yanzu yaushe zaki dawo?". Shiru Phaty tayi, Jiddah tace "owk ba rana kenan? thanks, haka mukai dake", Still shiru tayi ba ansa, Jiddah kamar zatayi kuka tace "Shikenan nagode kinsan danice da bazan yi maki hakaba amma ba komai", tuni ta katse wayanta, sai Phaty taji ba dad'i tasan bata kyauta mata ba, domin kuwa ba haka sukayi da itaba, haka kawai Phaty ta tsinta kanta na rashin san tafiya daga abuja, ko ita kanta ta rasa dalilin haka, d'aga wayanta tayi tanata faman kiran Jidda amma bata d'auka ba, domin kuwa Jidda ta cika tayi fam da abunda Phaty tai mata, Phaty tun tana d'aukan abunda wasa tajima Jidda ta kashe wayanta kwata-kwata, sosai hankalinta ya tashi domin kuwa Jidda bata cika fushi da itaba sosai ba, yanke shawara tayi ta tura mata ta message kamar haka _"Please my only kiyi hak'uri, nasan ban kyauta maki ba, amma gobe insha ALLAHU am on my way, kinji banaso kina fushi dani pleaseee"_
Tunda ta tura mata da sak'on Phaty ta kwanta tunani kawai take inhar ta tafi kamar bazasu k'ara had'uwa da Umar ba, sosai ya kwanta mata arai.
_Niko nace A'a Phaty duba rannaki ki gani ba kwanta maki yayi ba, mamaye zuciyar yayi_
YOU ARE READING
PHATEENJIDDAH
ActionYana maganane akan yara guda biyu Wanda suka kasance tagwaye, gashi Allah yayi musu rashin basajin magana ko kadan, sannan kuma ina gargadin iyaye da su runka jan 'yayansu a jiki basu wancakalar dasu ba akan wani dalili nasu na daban,👭