page 42

98 7 0
                                    

Ajiyar zuciya Jiddah tayi a karo na ba adadi, ta kalli Aunty fa'iza yayinda abincine lode a gabanta ta kasaci tace "Wallahi Aunty fa'iza bansan inda Phaty take ba, kuma na kira wayanta tanata ringing ba adauka"

Aunty Fa'iza kallan Jiddah tayi cikin tausayawa tace "Karki damu, insha ALLAHU zaki ganta nidai babban burina kici abincinnan ko yayane, tun dazu sai share hawaye kike ina kallanki"

Murmushi Jiddah ta kakulo wanda baigai zuci ba tace "Shikenan Aunty Fa'iza nagode sosai da irin kulawarki a garemu"

Phaty ce ta fara bude idanunta wanda sukai mata nauyi, dakyar ta budesu duka ta tsaya tana kallan dakinda take kwance a ciki tasan ko ba'a fada mata ba a cikin asibiti take, azuciyarta tace _"Garin yaya?, maiya faru dani?, wanene ya kawoni cikin wannan asibitin?"_ Tuni tunaninta ya dawo ta tashi a zabure tace "A'ahhhh" da karfi, cire karin ruwan da akai mata tayi ta diro daga kan gadon tana gunjin kuka, tana fadin "Please Dad ka yafemin wlh na duba, Oh my God, ALLAH ka taimakeni gani gareka, kai kasan halin danake ciki, fushin iyayena ba karamin abu bane a rayuwata tamkar na rasa rayuwatane" kokarin fita tayi tana bude kofar sukai karo da Umar dauke da flask da kuma cooler a hannunsa, ko kallansa batayi ba balle tasan koma wanene, kokarin fita kawai takeyi daga dakin, taji an ruk hannunta, rukone bana wasa ba, kallan hannun nata tayi tana tunanin wani hamshakinne yake ta izzar taba mata hannun, bin hannun tayi da kallo harta saukesu akan fuskaf Umar wacca ta sakata natsuwa, kallansa take babu kiftawa yayinda shima kallan nata yakeyi, ruko hannunta yayi ya shigar da ita ciki, akan gado ya zaunar da ita ya koma ya kwaso kayan da suka zube a hannunsa, yana dawowa ya bude flask ya hada mata tea mai kaurin gaske ya dora kofin a saitin bakinta babu musu ta bude bakin ta runka shan tea din cikin natsuwa har saida tasha da dan dama dama, sannan ta kauda kanta alamun ya isheta ba musu ya ije kofin ya bude cooler ya dauko flait da fork yana zuba mata chips, shima daukowa yayi yana feeding dinta a haka har taji ta koshi sosai, dan rabanta dacin abinci tun jiya da rana, gyara zamanta tayi cikin murya irin ta marasa lafiya tace "Good morning"

Umar bai ansa ba sai kafeta yayi da ido yana kallanta, jikintane ya bata ana kallanta ta dago suka hada ido hudu dashi, da sauri ta sadda kanta kasa dan bazata iya jurar kallansa ba, cikin wata irin murya wacca batasanshi dashi ba yace "Ya jikin naki?"

Idanunta sun ciko da ruwan hawaye muryarta na rawa tace "Naji sauki"

Sai Umar yaji tausayinta ya mamaye mai zuciya, yasan ba karamin abu bane zaisa Phaty yin sanyi lokaci guda, yasan ba karamin abu bane zuciyarta zata buga nan lokaci daya, yanaso yaji karin bayani daga bakinta, amma bayaso ya tada mata da hankali, dan daga ganin hankalinta ba akwance yake ba, tashi yayi daga inda yake zaune ya zauna a gefen gadonta yana kallanta, yayinda ita kuma hawayene ke malala a fuskarta, tun tana hanasu zubowa harta gaji ta sharewa ta daina, handkerchef Umar ya ciro a aljihun wandansa ya share mata hawayenta, cikin sanyi murya yace "Please stop it, banason inga kina hawayannan, komi ya faru dake ki fawwalawa ALLAH shi, sannan kuma ki runka yawaita gode masa akan halinda kika tsinta kanki, dukda dai bansan maiya faru dake ba, amma ina neman Alfarma kancewa a daina batamin beautiful face dinnan"

Phaty kallansa tayi shima kallanta yake yana sakin mata wani tsadaddan murmushi, murmushin itama ta sakin masa wanda baikai zuci ba, nan take idanunta suka ciko da hawaye, girgiza mata kai kawai Umar yake alamun ta daina amma ina hawayen ya subuce mata, kuka ta farayi a hankali mara sauti, Umar matsowa yayi gab da ita ya sa kanta a kafadarsa yana shafa mata baya alamun tayi hakuri, cikin dashashshiyar muryarta wacca bata fita tace "Umar!, Daddynah, Mommynah, Twin Sis dita, na rasasu, Dad ya koran yace karna kuma zuwa inda yake and yace bazai dauramin aure ba, He means bazai auramin kai ba, gashi wayana na barshi a gida balle na kira Jiddah naji, nasan idan kowa yana juyamin baya ita bazata taba juyamin ba, Umar na rasa happiness dina, bansan inda zan saka raina ba, ni nasan mai laifice awajansa, amma hukuncin daya yake a gareni tayimin tsauri, bazan iya ba, wallagi banso na tashi na ganni a wannan duniyar ba, naso ace ALLAHya dau raina, saboda ban taba ganin Dad a irin wannan yanayin na bacin raiba sai yau, kuma bacin ran nasa akaina, Wallahi Umar i hate my self, na tsani kaina na tsani halayyata" kallan sama tayi tace "Ya ALLAH ka dau rayuwata da gagggawa ko ALLAH zaisa na huta da wannan kuncin da nake fama dashi, ya RABBI ka........."

Da sauri Umar ya rufe mata baki yana girgiza kanshi, kallanta yayi yadda dukta burgice kamar ba Phatyn saba, yace "Haba Phaty, wannan wani irin abune haka? kinaso kiyi sabone?, koko bakisan ki cinye jarabawar da ALLAH ya daura makine?" Sassauta muryarsa yayi yace "Karki damu, insha ALLAHU zaki daidaita da Dad nai miki alkawarin haka, Dad zaisoki fiye da yadda ya soki da, i promise you, ki yadda dani, kuma ranar da aka sa mana tana nan bazai taba dagawa ba, zamuyi aure, zamu kasance tare, Insha ALLAHU zanyu kokari na samu Dad na fahimtar dashi"

Kankameshi tayi tana cusa kanta cikin kirjinsa tace "ALLAH yasa, ALLAH yasa ka shawomin kan Daddynah dana Mommynah, i love you my sahibul qalbee love you so much"

Sosai Umar yaji dadi da yaga Phaty ta sake, durkusawa yayi daidai fuskarta yace mata "Love you too" wani zazzafan kiss yayi mata a kumatu, yayinda Phaty taji wani shock.

Dausayine zaune a makeken falonsa, dan tunda ya tashi yau yaji gabansa yana mugun faduwa, ga kasala tana neman rufesa, zazzabine kai zafi ya mamayeshi, yana rawar sanyi kadan-kadan, yagama ainawa akwai abunda zai faru dashi kuma abunnan ba karami bane babbane, runtse idanuwansa yayi yana faman addu'o'i a zuciyarsa kan duk abunda zai sameshi ALLAH ya kawo maishi cikin sauki. yana cikin wannan yanayinne wayansa ta fara ruri, gabansane ya cigaba da faduwa yayinda yaga mai kiran nasa, sunan Dad dinsa ne ya bayyana, cikin karfin hali ya dauka ya gaishe dashi, nan take Abbansa yayimai Umarnin da yazo yana nemansa da gaggawa, cikin karfin hali yace masa gashi nan zuwa, bedroom ya fada ya dauko jallabiyansa ya gaura sama dan zuwa gun mahaifinsa.

Yana zuwa ya hango mahaifinsa a daki shi kadai, cikin sanyin jiki ya karasa wajansa ya zauna a kasa, yayinda mahaifin nasa ya dubesa sai yaji tausayin dan nasa ya kamashi, gyaran murya yayi yace "Dama kiran danai maka akan maganar gidansu Jiddah ne"

Gaban Dausayine ya kara faduwa ya dake yace "Ina jinka Abbah"

Yace "Dazu Alhaji Abdul-aziz ya kirani ya shaidamin cewar ya fasa aurar da yaransa, dan haka ya bani hakuri akan cewar muje mu karbi sadakinmu"

Gaban Dausayine ya cigaba da faduwa yayinda wata zufa ta fara cikamai fuska, kansa har yanzu a kasa yace "Inaji"

Abban nasa yace "Nayi mamaki daya fadamin haka, sai nace ko zai fadamin dalilinshi nayin haka, bai tsaya yimin ja yayyaba ya zayyanemin kaf abunda ya faru aka lamarin gidansa, yace bayaso ya cuceka, yanzu hakama maganar da nake gaya maka ya koresu babusu a gidan baisanma wacca duniya suka shigaba, amma nai masa fada kwarai da gaske kuma na nuna masa kuskurensa nayin haka tare da illolinsa, sannan kuma nace masa aure babu fashi, shiyasa nace bari na kiraka naji naka ra'ayin zaka iya auraanta?, dukda na yadda ta tarbiyarsu amma nai mamakin abunda Alhaji yacemin, amma nasan bazau taba yimin karya ba"

Ajiyar zuciya Dausayi gayi yace "Abba, wallahi ina sonta a duk halin datake ciki, dan ALLAH, karka bari Ummana taji wannan maganar, kuma dan ALLAH Abba kace masa nima ina nan akan bakata zan aureta a haka, dukda nasan Jiddah tana da halayya ta gari, kuma ina yawan bibiyarta aduk, wani lamarinta agaskiya batada mugun haki, Abba dan ALLAH kacemasa ko rana ban yadda a dagaba, ina kaunarta a haka"

Dad dinsa dadi yaji mara misiltuwa yace "Tashi kaje ALLAH yayi maka albarka, kuma ina mai tabbatar maka Ummanka bazata taba sani ba, jeka dan Albarka" tashi yayi zuciyarsa wasai, fargaba da faduwar gaba duk sun kau.

Baban Umar ne ya sakko daga step din bene, yayin da Hajiya Aina'u da Dija suna zaune suna kallo, karar wayar Alhajiceta dawo dasu daga duniyar kallon da sukeyi, cikin sallama ya daga, ya kara a kunnansa, saida ya gamaji kaf yace "Shikenan insha ALLAHU, ina nan zuwa tanzu zanje wani wajene idan na dawo zanzo, kuma zan shaidawa Umar din dan yasan abunda ake ciki shima.

Hajiya Aina'u tunda taji an ambata babban makiyinta ta karkace ta saki murmushi tace "Alhaji!, mai yaron nawa yayine naji ana nemansa?"

Alhaji cikin jimantawa yace "Wallahi baban yarinyar da Umar zai aurane yake bukatar ganina akan cewar ya fasa aurar da ita yanaso mu karbi sadakinmu, shiyasa nakeso naje naji dalilin haka"

Hamdala ta saki a zuciyarta tace"Alhaji, idan har mahaifin yarinyarnan bayason aurannan gwanda ku hakura, ga matanan a gari bila adadi"

Alhaji fita hanyar waje yayi yace "Dama ai baza muyi masa tilas ba shida diyarsa"

Dija tana ganin ya fita ta daga tsalle tace "Aikin malam yaciiiiiiiiiiii"

Hajiya Aina'u murmushin gefen fuska tayi tace "Ayi dai mu gani, dole ya aureki wannan karon ko yanaso ko bayaso............"




PHATEENJIDDAHWhere stories live. Discover now