*PHTEENJIDDAH*
*MALLAKAR*
*_Ƴar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
39Phaty kallan Umar take a tsorace, cikin wata irin murya wacca tasha kuka ta koshi cike da tashin hankali tace "Dan ALLAH Umar, kayi hakuri, ka barni naje gida kar asan ban kwana a gida ba, kayi hakuri nai maka alkawari wlh na tuba da yardar ALLAH bazan karaba, ka tai makeni ka rufamin asiiri"
Umar kallanta yayi idanunsa jajir kamar mai ciwon idanuwa, zuciyarsa na kuna, tashi yayi ya fita dakyar yake iya gane hanya saboda dishi-dishi kawai yake gani, toilat din cikin falo ya shiga dan dauraye fuskarsa, nan take sai hawaye mai dumi ya saukarmai akan kuncinsa, bai damu daya gogesu ba ya cigaba da tunanin da yake, alwala yayi ya fito ya shimfida dadduma, zuciyarsa ba karamin zafi kawai takeyi ba ya rasa mai zaiyi a rayuwa yaji dadi, kunci yayimai yawa, sallah ya tada dankai kukansa gun mahaliccinsa, duk sujada sai Umar ya zubar da hawayen bakin ciki, gashi ko kadan san Phaty bai goge acikin zuciyarsa ba, wata irin wutar santane ke tashi daga cikin zuciyarsa, ko kadan bashi da niyyar cutar da ita amma abubuwan datake mashi a yanzu sun farayin yawa, addu'a kawai yakeyi akan ALLAH ya kawo masa sassauci acikin zuciyarsa.
Phaty kuwa kawai takeyi kamar ranta zai fita, ta rasa yaya zatai, tasan inhar bata koma gida a darannan ba to asirinta yana gabda tonuwa, hannu ta saka aka ta cigaba da rera kukanta, komai ta tuna tayi sauri ta zabura ta fito daga dakin, hanyar waje kawai ta nufa tana kokarin fita, Umar yana kan prayer mat ya hangota tana kokarin fita, cikin sanyi murya yace "Ina zaki a cikin tsohon darannan?"
Phaty cikin muryar kuka tace "Zan tafi gida, wallahi bazan iya kwana anan ba, Daddyna, Mommyna, Sisterna duk suna bukatata, please Umar karka hanani tafiya, nasan nai maka laifi mai girma, amma duk abunda kaga ya dace kaimin to kaimin danka huce haushinka akaina, amma a gaskiya bazan iya kwana anan ba, inhar akasan ban kwana a gida naka yarda danii raina zai mugun baci, kuma zanyi danasani mai tsanani a rayuwata, please believe me wallahi na tuba, idan harna rantse maka bansan ina aikata hakaba nasan bai zama dole ka yadda dani ba, wallahi bansani ba, bansani ba, sai dazu naita tariyo abubuwa da dama kuma nasan ban aikata hakaba, nasan bazaka yadda da duk abubuwan da zan fada maka ba amma ALLAH shine shaidata" Sosai Phaty take kuka tana fadawa Umar abubuwannan, tsugunnawa tayi a kasa tana kuka mai tsuma zuciyar duk wani mai sauraro, a hankali tace "Ni nayi imani ga ALLAH wannan jarabawa ce a gareni, banma gama cin jarabawar tawa ba, akwai abubuwa da dama da zasu faru dani mai tsananin nan gaba dan kuwa jikina ya bani hakan, ina zatonma acikin tawa kaddarar harda rabuwa dakai, dan nasan bazaka taba saurarata ba, nasan zakai tunanin da sanina nake aikata wannan abun, ni nasan da nayi rashinji amma harga ALLAH bazan iya aikata wannan abubuwan dakaina ba, nasan akwai wani boyayyan al'amari amma ALLAH shine kadai yasan da haka" Shiru tayi ta cigaba da kukanta maiban tausayi.
Umar tsayawa yayi yana kallanta dan kuwa ba karamin tausayi ta bashi ba, hamdala kawai yakeyi a zuciyarsa, dan kuwa yana kyautata zatan sihirin da akaima Phaty ya karye tunda yaji jawabanta, haushinta da yakeji yaji ya kau, soyayyarta ce kawai cike a cikin zuciyarsa, nan take yaji kaunarta ta mamaye mai zuciya, tsugunnawa shima yayi ya kamo hannuwanta, shiru yayi yana nazari, Phaty kuwa kuka kawai takeyi kasa-kasa, kamo hannuwanta yayi yajisu zafi rau, kallanta yayi itama shi take kallo, sun dau mintuna wajan shida a gaka, sannan Phaty tai sauri sadda kanta kasa, dan bazata iya kalla ba, yana mata kwarjini da yawa, sosai Umar ya kafe Phaty da kallo, santa na kara karuwa a cikin zuciyarsa, Phaty dagata baida niyyar yin magana saita fara kokarin zare hannunta daga nashi, amma ta kasa kasancewar ba karamin danka yayima hannun nata ba, Mikar da ita yayi baice mata uffan ba ya shigar da ita cikin bedroom, bathroom ya shiga dan hada mata ruwan zafi, ya fito ya kama hannunta, yana shigar da ita bayin ya fito ya zauna akan gado, addu'ar neman tsari kawai yake daga shaidan dan a halin da yake ciki yanzu mugun sha'awar Phaty yake, dan harta kai ta kawoo yaji bazai iya barinta haka kawai ba ba tare dayayi mata abuba, addu'o'i kawai yake, ya dafe kansa tare da runtsa idanu, tashi yayi ya fita daga dakin yaje kitchen ya hado tea wanda yaji lemun tsami ya shanyesa tas, lumshe idanuwansa yayi dan ba karamin zugi suke mai ba, dakin ya koma dan ya tabbatar data gama shirinta, yana shiga yaga tana kokarin fitowa daga ita sai towel, da sauri ya juya baya, ita kuma ta koma cikin bayin gabanta yana dukan tara-tara, dan taga yanayinsa kamar ba kalau yake ba, dan bazata taba mantawa da irin yanayinsa ba tym din da Dija tasamai magani a abinci, dafe kirjinta tayi tanata faman addu'a.
YOU ARE READING
PHATEENJIDDAH
ActionYana maganane akan yara guda biyu Wanda suka kasance tagwaye, gashi Allah yayi musu rashin basajin magana ko kadan, sannan kuma ina gargadin iyaye da su runka jan 'yayansu a jiki basu wancakalar dasu ba akan wani dalili nasu na daban,👭