page 45

95 6 0
                                    

Bayan su Alhaji Abdul-aziz sun gama 'yar karamar walimansu sannan Alhajin Umar da Dad din Dausayi suka fara yima Hajiya Amina da Alhaji Abdul-aziz yan nasihohi masu ratsa jiki, sannan Dad din Dausayi yace "Yanzu dai zamu maida date din bikinnan karshen wata mai kamawa, wato wata daya kenan, kai kuma Abdul kar inkarajin wani abu makamancin abunda ya faru daga baya inba haka ba zamu bata zamuyi baram baram dakai"

Dariya Alhaji Abdul-aziz yayi yace "Haba abokina wancanma tsautsayine da bacin rai amma insha ALLAHU babu abunda zakaji sai alkhairi"

Nan hira ta barke tsakaninsu, Hajiya Amina da Hajiya Maryam kuma suka haura upstair dan tattauna yadda sha'anin bikin zai kaya.

Hajiya Aina'u ce zaune ta kishingide itada Dija suna tattauna yadda zasu kara yima umar wani makircin yadda dole sai Abbansa ya yarda ya aureta, Dija kallan Aina'u tayi tace "Aunty yaka mata ace yanzu boka ko malam mun daina dogara dasu, haba dan ALLAH sai kace mudin ba mata bane, muda muke da hanyar makirci kala-kala kwando-kwando, gaskiya nagaji dabin bokayannan suyita faman amfani dakai wani sa'inma babu wata biyan bukata, nidai na gaji inma fa ba hali wlh saina fara zagon kasa, wato na kasance mai ladabi da biyayya a wajansa tunda naga gaskiya abun ba sauki"

Hajiya Aina'u kallanta tayi shekeke sannan ta kwashe da dariya tace "Ban taba sanin baki da hankali ba sai yau, sannan kuma bansan ke wawiya bace ba sai yanzu, naji a barshi zaki kasance mai biyayya awajansa, kuma ya amince yace zai aureki to shi wawan inane da bazai gane budurwa ba da wacca maza suka sani barin ke da kika zama kamar motar hawa kowa hawanta yake, barinki nawa muke zubarwa, ai wlh aranar inada tabbacin saiya nada miki na jaki sannan ya koroki da takardar saki, dan haka tun wuri yaka matama ki farka idan mafarki kike, ai irinsu Umar maganinsu shine boka da malam, amma wlh makirci bazai taba yimai ba barinma idan ya tabbatar ba a budurwa kikazomai ba, saukinki daya shine idan ya dandanaki yajiki a budurwa shine zan iya cewa zaki iya shawo kansa, shawara dayace ki hada da makircin da kuma malamai, shine zaki samu biyan bukatarki"

Dija shiru tayi nadan wani lokaci tana nazari sannan tace "Kuma fa Aunty maganarki gaskiyace, wlh yadda yake da bakar zuciyarnan ina tunanin kashenima zayyi sbd yadda ya tsana zina a rayuwarsa, ba komai Aunty kibarmin wuka da nama a hannuna zakiga aiki da cikawa" dariya sukayi hade da shewa suna tafawa.

Umar ne tsaye shida mahaifinsa suna tattaunawa, Umar kallan babansa yayi yace "Alhaji, ina neman wata alfarma a wajanka"

Kallansa yayi yana nazarai yace "Uhmm inajinka, wata irin alfarma kake nema haka?"

Umar yace "Banaso Hajiya tasan cewar ba'a fasa bikinnan ba, dan ALLAH yadda ta dauka an fasa ka barta a hakan, inhar tasan bikinnan yana nan bansan wani mataki zata daukaba nan gaba"

Murmushin manya Alhajin Umar yayi yace "Karka damu, dama nima hakance a raina kar ta kara cutar da yarinyar mutane, kaga hakkinta muma bazai barmu ba sbd ta sanadiyarmu ake mata haka"

Murmushin jin dadi Umar yayi yace "Nagode kwarai da gaske Alhaji, ALLAH ya kara budi da azziki mai amfani"


Aminssa ce zaune tana shan shisha tare da wasu gayu a gefenta, lumshe idanuwanta tayi tace "Guy kana da labarin twins wai aure zasuyi?"

Wani dogon saurayi mai kyau amma babu tarbiya tattare dashi yace "Haba Beb wasa kike, ina garinnan twins zasuyi aure, ai wallahi basu iya ba, ai banga macen da zata cimin kudina a banza ba wallahi, bazanyi asarar kudina akansu ba daga karshe sukaima mijin da zasu aura virgin dinsu, dukkansu ban cire kowa ba a cikinsu"

Aminssss lumshe idanuwanta ta karayi tai wata dariya tace "Ai idan kana wannan maganar barina gargadeka karka sake kace zakai agaban Bash inba haka ba wallahi zaku kwasa 'yan kallo a wajannan, kasan yadda ya kwalllafa rai a kan Phaty ALLAH bai nufa ba, kuma nayi imani har yanzu bai cire rai da itaba, shida yace wlh ko saura minti biyarne daurin auranta ya samu dama saiya ketata balle kai kazonan kanamin hayaniya akai"

PHATEENJIDDAHWhere stories live. Discover now