Murmushi ta sakar mashi wanda ya kasheshi, sosai yaga ta k'ara kyau dukda dai ba kwalliya a fuskanta, fuskanta cike da annuri ita kanta batasan mai yasa hakanba, gaisheshi tayi, kanta a k'asa, shima ya ansa, kallanta yake cikin kulawa da kauna yace mata, "kinci abinci kuwa?" .kanta a k'asa ta girgiza masa kai, magana zakimin, "a'ah har yanzu banci ba amma yanzu nakeson naje na dafa koda indomie ne", Umar yace "ya mukai dake?", Phaty tace "Uhmm, uhmm nasan baka iya girki ba kuma banaso nasa wanda ya girmeni aiki shiyasa ma". Umar dariya yayi yace "ba wani nan, kikasa auntynmu aikin had'a breakfast, daka k'arshema kikak'i ci".
Phaty tai saurin katseshi da cewa "Noo aiba ita ta had'a ba 'yar aikice fa tayi, aida itace da tuni na sanko na tayata".
"Hmmm naji" cewar umar, mika hannunsa yayi bayan motar ya d'auko basket food, d'aura mata basket d'in yayi akan cinyarta yace mata, "ga break fast d'inkinan, inaso ki cinyesa tas, banaso ki barmin komi". zaro idanu Phaty tayi tace, "wannan uban kayan zan iya cinyewa, wlh kasan bazan iyaba".
Lumshe idanuwansa yayi yace, "tabbas sai kincinye minshi duka". Phaty tace "naji, naji, to amma a ina ka samomin wannan kayan?". Umar kallanta yayi, irin kallon kin rainamin wayo ma, yace mata "ya za ai kice a ina na samomaki kayannan, kin manta nace maki nida kaina zan shiga kitchen na had'oma k'awata breakfast ne? serious nina girka miki, ina fatan zaki cikamin tunbinki da abinci". Zum6uro baki tayi tace, "nidai wlh banda tumbi". Kallanta kawai Umar yake, don kuwa abunda tayi yayi mashi kyau matuk'a, kallansa tayi taga ita yake kallo, d'aga masa gira tayi tace "wannan kallan fa", Murmushi yayi mata yace, "Phaty ana fad'a maki kina da kyau kuwa?". Wani irin kallo tai masa wanda ya kusan da tafiya dashi, tace "so kake kawai ka zageni amma kaikanka kasan kafini kyau nesa ba kusa ba""Phaty kenan wlh kina da kyan da ba ko wacce mace kedashi ba, kafin asamu mace maikyanki sai antara mata dubu dakyar za'asamu mace guda mai kyanki a ciki"
"To naji kuma nagode, bari naje na karya don cikina sai k'ugu yake".
Kallanta Umar yayi yace "nimafa banci ba tare nayo mana girkin, nasan idan ina kusa dake sainafijin na k'oshi da wuri".Kallansa Phaty tayi tace "kana nufin baka karya ba kaima?"
Murmushi Umar yayi yace "Mamaki kike?, wlh ban karya ba tunda kikace baki karya basai naji banason cin abincin, sai naga kin k'oshi tukun"Murmushi tai wanda ya k'ara bayyana kyanta tace, "bari naje d'akin bak'i na gyara ina tunanin yayi k'ura tunda ba shiga akeba, bari nazo", tana k'ok'arin fita Umar ya ruk'o hannunta, kallan hannun kawai tayi yayi saurin sakinta yace "am sorry, dama magana zan maki why not muje kawai inyaso na tayaki aikin,tunda naga kin gaji karna saki aiki, Phaty tace "Ohk shikenan muje to" zata d'auko basket d'in yace tabarshi shi zai dauka, a harabar gidan ya tsaya, itakuma ta shiga ciki dan d'auko key, tsintsiya, da mopper, d'aukowa tayi tace "friend muje ko" tafiya suke har suka isa d'akin, saka key tayi ta shiga d'akin tace mai "bismillah, shigo" suna shiga d'akin tace "friend kagama ba datti sosai yanzu za muyi mu gama", Umar yace "gaskiya ba datti, yanzu ke zaki shara ni kuma nai mopping ko" Phaty tace, "hakanma yayi, bari na fara ko" cire hijab d'inta tayi, ta ratayeshi, sam ta manta da irin kayan dake jikinta, ta fara shara, sam Umar bai kulaba kasancewar yana danna wayarsa, d'agowa yayi yaganta da sauri ya runtse idanunsa, azuciyarsa yace, _"wannan yarinyar tana nema ta kaini bango fa"_, a hankali ya kira sunanta kamar mai rad'a yace "FATIMA", Sosai sunan ya bugi kunnan Phaty ta waigo tace "na'am, yadai naji voice d'inka ya canza ne, ko baka da lafiya?", dakewa Umar yayi yace "K'alau nake, yaka mata kisa hijab d'inki". Kallan jikinta tayi taga atamface amma fa sun matseta sosai, idanma ta tsuguna har boobs d'inta zakagani, gashi dama akwaita da hips, data tsugunna sai suka k'ara girman gaske, sai tace mai "But friend kasan hijab d'in yanada girma, bazanji dad'in aiki dashi ba wlh, na kusan gamawa, idan nagama saina saka ko" saita cigaba da aikinta, don kuwa ita harga ALLAH bata kawo komai aranta ba, aganinta tasha fita da kayan da sukaci uwar wannan a fitsara, Umar yaga Phaty bata damu ba, kawai ya tashi ya d'auko hijab d'in, Phaty batasan wainar da ake toyawa ba, saboda shararta kawai take hankalinta kwance, ji tayi kawai and'agota, zatai magana kawai saitai shiru saboda ganin yanayinsa datayi ba wasa, hijab d'in ya saka mata, yace "Gaki da d'an banzan rauni, amma kin iya bad dressing, inga kin kuma"
YOU ARE READING
PHATEENJIDDAH
ActionYana maganane akan yara guda biyu Wanda suka kasance tagwaye, gashi Allah yayi musu rashin basajin magana ko kadan, sannan kuma ina gargadin iyaye da su runka jan 'yayansu a jiki basu wancakalar dasu ba akan wani dalili nasu na daban,👭