Hajiya Aina'u kuwa ficewa tayi ta kama kanta tana mai farin ciki komai zaiso mata da sauk'i, a zahiri fad'i take "Kin gama yawo wlh, badai kince dani zakija ba, wannna maganin insha ALLAHU saiyasa kin zama magajiyar karuwai, ni kika cima mutunci ko, wlh mai irin sunana ma kinbar tozartawa balle kuma ni"
Hajiya Aina'u mai keke napep ta samu tahau, kasancewar bata iya tuk'a mota ba, ranta fess tana jiran Dija ta dawo suje su samu kwata mai d'an banzan d'oyi dan aikinsu yayi da kyau, haka ta zauna jiran Dija dan su samu anguwar da take da kwata.
Umar shiryawa yayi tsab cikin k'ananan kayanshi wanda sukayi matuk'ar kar6ansa, sannan kuma sunyi masa kyau ba kad'an ba, murmushi shinfid'e a fuskarshi, d'aukar waya yayi ya kira Phaty, tana d'auka yace "Ina fatan gimbiyata tayi shirin kar6ar bak'on nata?"
Murmushi Phaty tayi wanda har beauty point (dimple) d'inta na lotsawa, tace "Aini na dad'e da jiran wannan bak'on nawa, amma najishi shiru, ko bak'on nawa ya k'araso ne?
Dariyar jin dad'i Umar yayi yace "Bak'onki bai k'araso ba, amma ina da tabbacin yana hanya dan haka at any moment zaki iya ganin bak'onki cikin 'yan dak'ik'a kad'an, ina fatan ban 6atama gimbiyata raiba?"
Phaty tace "Saura 'yan sakonni dai ran nawa ya 6aci, tun d'azu fa kace zakazo harna fara gajiya da jiranka, gashi kwalliyana ma ya fara tsufa, ni wallahi kayi sauri", Ta k'arashe maganar cikin shagwa6a
Umar yace "Oh my God, karkisani na kasa driving, wannan kashe murya haka, ganinan insha ALLAHU nagama had'a komai nawa, fitowa kawai zanyi"
Ajiye wayoyin dukanninsu sukayi, suna masu matuk'ar k'aunar junansu.
Umar ya fito kenan daga cikin d'aki ya hango Dija ta shigo cikin gidan, kallo d'aya kawai yayi mata ya kawar da kansa gefe kamar bai san da wani halitta ba, Dija kuwa saurin parking kawai tayi tai saurin fitowa daga motar, ganin Umar yana k'ok'arin shiga motarsa yasata gudu-gudu, sauri-sauri tare da d'aga muryarta yadda zai jita fad'i take "Yaya! yaya!!"
Umar yana jinta yayi kunnen uwar shegu da ita, guy d'insa ne yace "Ranka shi dad'e, Hajiya na maka magana fa"
Umar dubanshi yayi yace "Zaka tada motarne ko bazaka tada ba?, kayi gaggawar barin wurinnan inka bari tazo ta samemu to kayi kuka da kanka"
Guy d'in yanajin haka yayi gaggawar figar motar, kasancewar getman ya bud'e get d'in fitarsu yake jira,kafin Dija ta k'araso kuwa harsun fice daga gidan, tsayawa tayi tana haki, kasancewar da tazara a tsakaninsu, tsaki taja tace "Dan wulak'anci kawai dashi, aina tabbata kajini shine saboda wulak'anci ka kama kanka ka tafi" k'wafa tayi tace "Wallahi duk randa kazo hannuna wallahi bazan saurara maka ba, saina gasa maka aya a hannu, wallahi duk bak'ar wahalar danasha ta sanadiyarka saina rama akanka, karkai tunanin kaci bulus", Murmushi tayi tare da shewa tana fad'in "Komai zai zama daidai, tunda har na bama wannan malamin had'in kai nasan zai mana yadda mukeso, bacin nagama da waccan tsinanniyar, shi kuma zan dawo kanshi sainasa an mayarmin dashi _kantace_ bama _mijin hajiya_ ba, bari naje gun Hajiya naji ina yaka mata muje mu tsiyaya abuncan, dan bazanso ya kwana ba, dan ance da zafi-zafi akan daka k'arfe", haka ta kama hanyar shiga cikin gidan tanayi tana shewa kamar an mata bushara da gidan aljanna.
Umar kuwa basu tsaya a ko inaba sai a gidansu Phaty, kiranta yayi yace mata "Madam nafa k'araso, yanzu haka ina harabar gidanku"
Kasancewar Phaty tana cikin d'akin bak'i tana mai arragement d'in abubuwan data tanazar mishi, tace mai "Ko yalla6ai zai iya k'arasowa, yanzu haka ina d'akin bak'in"
Kashe wayan yayi Umar yacema guy d'insa "Kad'an jirani barina fita" Fita yayi ya taka har zuwa d'akin bak'i, sallama yayi ya shiga, Phaty ya hango sai shirya masa delicious take, dan ko kad'an bataji shigowarsa ba, "Masha ALLAH!" kawai Umar yace dan kuwa Phaty ta tafi dashi, tai masa kyau over, itakuwa Phaty sam bama tasan da wani Umar ya shigoba, kasancewar ta juyawa k'ofar baya, takawa yayi a hankali ya k'arasa inda take, k'amshin turaransane ya tabbatar mata daya shigo, kafin ta waigo har Umar ya iso gareta, k'ugunta taji an kama, zumbur ta mike dan harga ALLAH ta tsorata, waigowa tayi taga Umar yana kasheta da Murmushinsa mai matuk'ar tsada, had'e rai tayi kamar ba itaba tace "Gaskiya in kanamin haka wlh zan canza shek'a tunda kai bakajin magana"
YOU ARE READING
PHATEENJIDDAH
ActionYana maganane akan yara guda biyu Wanda suka kasance tagwaye, gashi Allah yayi musu rashin basajin magana ko kadan, sannan kuma ina gargadin iyaye da su runka jan 'yayansu a jiki basu wancakalar dasu ba akan wani dalili nasu na daban,👭