*PHTEENJIDDAH*
*MALLAKAR*
*_Ƴar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
*Please Subscribe My Channel*https://www.youtube.com/channel/UCWyfuDW1EWCBqzOrwaCnq3Q
Domin kawu muku Audion littattafan Hausa
9Waigawa wurin umar tayi, ya d'aga mata gira yace, "yadai mu wucene?". Phaty batada za6i haka ta hak'ura umar ya jasu, bai direta a ko inaba sai a harabar hotel din, amin's kuwa taci gayu harta gaji, tayi kyau over, tana hango Phaty acikin mota ta tafi da murnarta dan tarota, amin's tace,
"Beb kinso fa ki yarfani, anata jiranki, amma shiru kawai nakeji, wasuma sun d'auka antaya masu k'arya nayi"
Dariya Phary tayi tace, "Big gurl kamarki ace kina k'arya ai suma sunsa yawane, sharesu kawai, i hope dai komai ya kammala casu kawai za asaka mana?", daria Amins tayi tace, "Zanso naga ranar dazaki daina son rawa da wak'a"
"Anya kuwa zakiga ranar?, kaiii ina bana tunani" cewar Phaty, Umar kuwa yana mota duk abunda Phaty da Amins suke yana kallonsu, Phaty kuwa tama manta da wani Umar harga ALLAH, Amins ce ta dafa mata kafad'a kee Beb wancan bashi bane ya kawoki ba?, naga sai kallon nan yake, dukda bana hangosa dakyau",
"Oh my God wlh na manta, shaaf, bari naje naimai godia sai mu shiga ciki ko".
"A haba k'awata ai nima ya cancanci naimai tawa godiyar ta musamman tunda ya kawomin ke lafiya, muje kawai"
Phaty ce tai gaba Amins ta bita, k'wank'wasa glass d'in motar tayi, zugewa yayi a hankali, yana kallonta murmushi yayi mata mai k'awatarwa yace,
"Sai yanzu aka tuna dani kenan?, kinga k'awarki kinma manta dani"
Yak'e tayi masa tace, "dan ALLAH kayi hak'uri wlh mantawa nayi" juyawa tayi gun Amins taga bata tare dasy, Amins ta tafi duniyar tunanin Umar, ta6ata Phaty tayi tai firgit ta juyo, Phaty bata gane yanayin da Amins take ba, tace,
"Beb gashinan ku gaisa,"
ajiyar zuciya Amins tayi wanda har saida Phaty da umar sukaji, yak'e kawai takeyi domin kuwa Umar ya tafi da itaba kad'anba, tunani kawai tayaya zata samu wannan guy d'in, ta samu wanda zata more rayuwarta, maganar Umar ce ta dawo da ita cikin hayyacinta, murmushi ya k'ara sakar mata yace, "kawarmu ba magana ne"
"akwai magana mana, Beb a ina kika samo mana wannan guy d'innan haka?" cewar Amins, yatsina fuska Phaty tayi tace,
"A hanya wlh, auuu na manta ban baki labari ba, in komai yayi normal zan fad'a maki"
"Ohk ba damuwa, friend nagode sosai da taimakon k'awata ALLAH ya saka da alkhairi"
"Ba komai ai, mun zama d'aya tafi k'arfin haka inhar agunane"
yatsina fuska Phaty tayi tace, "Beb yaka mata muyi gaba coz naga mufa ake jira"
"Owk muje, amm yama sunanka"
"K'awarki ta fad'a maki ta sani"
"owk ba damuwa sai gani na biyu"
Amins harta kama hannun Phaty zasubar wurin, sai umar yace "FATIMA". Cak ta tsaya amma bata waiga ba, amins cewa tayi "saikin taho" tayi gaba, please kizo yanzu zaki tafi, juyowa tayi taje inda yake, gani ta tsaya, please ki shigo yanzu zaki tafi dan ALLAH, kallansa tayi ido cikin ido ta zum6uro baki tace.
"nifa wlh ka fara takuramin, me zan maka kuma?"
haka ta bud'e k'ofar motan tanata k'unk'une ta shiga motar, "gani" tace mai taanata kumbure-kumbure, sosai tabashi dariya amma saiya dake,
"Wai mai yasa kike hakane, saikace k'aramar yarinya". Still banza tayi dashi, sannan tace,
"Nidai ka fad'a abunda zaka fad'amin na kama kaina"
"Kinsan abunda nakeson dake?". Shiru Phaty ta kumayi, yace, "dake fa nake magana", still shiru tayi, hannunta ya ruk'o tayi saurin fizgewa tace,
"halan baka iya hak'uri da mace inhar kaganta?, bini-bini kace zaka ta6a mutum wannan bayi bane wlh"
"Wow tayaaya kikasan halina haka?, ai inhar akanki ne to ki tabbatar namafi haka"
"please ka fad'amin abunda zaka fad'amin zan fita"
Ruk'o hannunta ya k'arayi, tai-tai ta fizge ta kasa, idanuntane suka ciko da k'walla "please me kakeyi haka banaso wlh, bana k'auna, dan ALLAH kasakeni"
"Naji zan sakeki amma ki tsaya ki saurareni, dan ALLAH Phaty karkisa k'ananun kayannan dana gani cikin jakarki, domin girman ALLAH ba danni ba"
"Why! whyyyy kakemin hakane?, yaushe kasanni da irin wannan zai runk'a shiga tsakaninmu?, yaka mata ka farka idanma mafarki kake". da k'arfi da fizge hannunta ta fice daga motar, muryanshi ta jiyo a bayanta yana cewa "please Phaty, domin darajar iyayanki da 'yaya dazaki haifa nan gaba, nasan bazakiso suyi irin wannan rayuwar taki ba". Sosai muryar Umar tai rauni da yake maganar, bata waigoba ta shige warta cikin hotel d'in..
Umar sa kansa yayi a sitiyarin motar, zuciyarsa na masa k'una, "ALLAH ka bani ikon cinye wannan jarabawarka, ALLAH ka taimakeni kasa na shawo kan Phaty," sosai yakejin ba dad'i ga kishi ya turnuk'esa, wayarsa ce ta fara ruri, janyo wayar yayi ya d'auka, daga can 6angaran jafar ne ke cewa, "Oga ina ka shigane munata nemanka, gashi shugaban k'asa sai jiranka yake, da alamu ma ransa ya 6aci, kuma bai kamata kana fita kai kad'ai ba""Jafar kazo England hotel kazo ka tafi dani yanzu, please kayi sauri banajin dad'ine, zazza6i na k'ok'arin kamani, dafatan an gyara motarnan?, katahomin da ita nan"
Nan take Jafar ya kashe wayar, tuni yahau motar da Ogansa ya umurcesa yazo mai da ita, bai tsaya a ko inaba sai a England hotel, yana zuwa harabar hotel d'in ya hango motar Ogan nasa, tuni ya nufa inda yake, yananan yadda yake, da sauri yaje gunsa yace,
"Subhanallah Oga maike damunka haka naji jikinka da zafi". Umar lumshe idanuwansa yayi yace "Ina key din waccar motar?". Da sauri Jafar ya curo key din a aljihunsa yace "Oga gashi"."Ka kira Usman kace yazo, ina fatan zai gane yarinyar da kuka wulak'anta d'azu, kace, idan yazo ya shiga cikin hotel d'in ya nemeta idan yaganta ya jirata harta gama abunda takeyi sannan ya dank'a mata key d'inta tare da bata hak'uri, kagane ko"
"Yes sir" cewar Jafar, "amma Oga yaka mata mu wuce hospital, jikinka da zafi sosai"
"ba damuwa Jafar kaini masaukina kawai, ina tunanin gajiyace kawai". Jafar ji kawai yayi amma bai yadda ba, domin rabonsa da ganin Ogansa a irin wannan yanayin tun rasuwar mahaifiyarsa, "ALLAH sarki Oga ALLAH ya baka lafiya". da taimakon Jafar Umar ya koma seat d'in mai zaman banza, shi kuma ya kira Usman ya bashi umarnin Ogansu, sannan ya jasu suka tafi, bai zarce ko inaba sai masaukinsu.
_Wow kawai nace, wurin ya hadu overr yadda mai karatu baya tunani_
Phaty kuwa tana shiga cikin inda suke taro taji jikinta ya mutu, kalaman Umar sai yawo yake mata a kwakwalwar kanta, acikin zuciyarta tace _"tabbas wannan guy d'in baiyi k'aryaba bana fata na haifi yaron dazaiyi halina, tukda dai ba iskanci nakeyi a waje ba, amma sai kiga ALLAH ya bani yarinya mai zuwa party harma da bin maza, ya ALLAH ka shiryeni, ALLAH kasa nagane gaskiyar abunda nake"_. Sosai zuciyarta ta karaya, Amins ce tak'araso kusa da Phaty tace, "Beb yaka mata kije ki cire kayannan na jikinki coz yanzu casun zai fara". Phaty kallan Amins tayi tace, "k'awata banajin dad'i kwata-kwata wlh ba abunda zan iya, ni hayaniyarnan ma ta isheni waje zan fita idan, kun gama ina jiranki ki maidani gida kinsan banda mota balle na tafi gida". Amins d'an ta6a jikin Phatyn tayi taji da zafi rau, tace, "kai beb kinji zazza6i na neman rufeki kuwa?, ki shiga motana ki huta idan komai ya kammala sai mu tafi kinji, sorry". 'Daga mata kai kawai Phaty tayi ta fita daga cikin wuraran, samun wuri tayi ta zauna ta shiga duniyar tunani.
YOU ARE READING
PHATEENJIDDAH
ActionYana maganane akan yara guda biyu Wanda suka kasance tagwaye, gashi Allah yayi musu rashin basajin magana ko kadan, sannan kuma ina gargadin iyaye da su runka jan 'yayansu a jiki basu wancakalar dasu ba akan wani dalili nasu na daban,👭