*PHTEENJIDDAH*
*MALLAKAR*
*_Ƴar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
38Hajiya Maryam kallanta tayi tana nazari, tace "Jiddah nifa ba cewa nayi kizonan kimin kuka ba, kawai dai na tambayekine"
Jiddah ta bude baki zata kara magana a karo na biyu sai sukaji an turo kofar, dukkaninsu kallan kofar sukayi sai sukaga Dausayi ya shigo cikin dakin fuskarsa ko kadan babu alamun dariya, daidai inda Jiddah take yaje ya dagata, kallan Hajiyarsa yayi yace "Hajiya bari na kaita gida kar Mom dinsu taji ta dade kuma yamma tayi" Mikar da ita tsaye yayi ya kamo hannunta ya kalleta yace "Muje ki"
Jiddah duk kunya ta isheta ga fargaba datake fama da ita, cikin dabara tana kokarin kwace hannunta taji yayi nata ruko bana wasa ba.
Hajiya tsayawa tayi tana kallan ikon ALLAH dan yadda Dausayi ya hade girar sama data kasane yasata kasa cewar Jiddah karta tafi, tana kallansu sukabar dakin suka fita.
Dausayi yana kai Jiddah cikin mota ya sakin mata murmushi yace "Bari nazo na manta abu acikin gida" Itadai Jiddah shiru tayi tana faman godema ALLAH yau ALLAH ya taimaketa.
Dausayine ya tura dakin Mom dinsa ya ganta a tsaye tana faman zirga-zirga, yana shiga yace "Haba Mom ya zakimin haka dan ALLAH, abunda kikema Jiddah kamar baki yadda da ita bane kuma kamar baki yadda da irin tarbiyarta bane, tunda mukazo naga take-takenki akanta kina mata abu kamar wacca bata farin ciki da auranmu, yanzu tsakani da ALLAH taje gida ta fadama Mom dinta abunda kikai mata kina tunanin Mom dinta zataji dadine, kuma kinsan yadda ta daukeki tamkar yar uwarta haka ta maidaki, wallahi idan kawayene sukeson shiga tsakaninku da ita ina mai tabbatar miki nan gaba kece dajin kunya, kuma ni Jiddah nina ganta nace inaso kome takeyi na yadda na amince ni Dausayi zan aureta, dan haka dan ALLAH Hajiya ki daina irin haka, kiyi hakuri inna bata miki rai, ina kaunarki, bari naje na dawo yanzu zan kaita na dawo".
Fita yayi yaje ya samu Jiddah, kallanta yayi ya sakin mata murmushi, itadai yake kawai take, dan yanzu ta yanke shawarar gwara ta fada mai gaskiyar rayuwarta kardaka baya yaji azo asamu sabanin, Dausayine keta faman yin magana amma Jiddah ta lula duniyar tunani, a haka har suka karasa kofar gidansu amma Jiddah bata sani ba, saida Dausayi yayi nata magana sannan ta ankara, duk yana ganin yanayinta yadda ya canza, cikin muryarsa mai dadin sauraro yace "Yaka mata ki tafi gida ba coz naga magrib harta karato"
Jiddah kallan Dausayi take babu kiftawa, shima kallan nata yake, ruko hannunsa tayi tace "Yaya, zan fada maka tarihin rayuwata karkazo kaji a wani wajan kace ni maciya amana ce, zan fada maka gaskiyar abunda nasani game dani saboda gudun wataran, agaskiya yaya...."
Yatsuntsa guda biyu yasa akan labbanta yace "Karki fadamin komai, bansanjin komai, kome ya sameki arayuwarki ni naji kuma nagani nace inasanki a haka, dan haka karki damu kanki, kuma dan ALLAH karki fadama Mom abunda ya faru nasan bazataji dadi ba"
Hawayene masu zafi suka sauka kan kuncin Jiddah cikin muryar kuka tace "A'a yaya ba komai ba, ni nasan ban kyautama rayuwata ba, sannan kuma banma kaina adalci ba, basan akwai ranar kin dillanci ba sai yau, ban taba tunanin irin wannan ranar zatazomin ba, wallahi ban kyautama kaina ba, nayi gurbatacciyar rayuwa, sai yanzu danasi ya fara sauka akaina"
Dausayi kallanta kawai yakeyi kwarai da gaske ta bashi tausayi, ruko hannunta yayi ya mika mata handkerchief yace "Karki damu kanki, tun kafin ki mallaki hankalin kanki nake bibiyarki, nasan komai game da rayuwarki, nasan akan zuwanku club keda yar uwarki nasan duk shiga da ficanku, kuna Alhamdulillah mutane da dama sun miki shaidar azziki, kuma naji dadi har cikin raina danaji haka, kuma kinsan ko wani bawa da irin jarabawar da ALLAH yake aiko mashi da ita, kisa a ranki wannan jarabawace daga ubangijinmu ALLAH yasa mu iya cinye jarabawarnan, sannan kuma ya kare zuri'armu daga fadawa halaka, karki damu, zan samu Hajiyata nai mata bayani yadada zata fahimta, kinsan kowa da irin kuruciyarsa, wannan itace kuruciyarki ta zuwa party, kuma ai naga kin dade bakije ba, hakan na nufin kin saduda kenan, kodai yau zamu dana zuwa FIRE CLUB ne" ya karashe maganar cikin sigar wasa da zolaya.
YOU ARE READING
PHATEENJIDDAH
ActionYana maganane akan yara guda biyu Wanda suka kasance tagwaye, gashi Allah yayi musu rashin basajin magana ko kadan, sannan kuma ina gargadin iyaye da su runka jan 'yayansu a jiki basu wancakalar dasu ba akan wani dalili nasu na daban,👭