Cikin gaggawa Dija ta tashi ta d'auko key d'in motarta, basu wani 6ata lokaci ba suka fito harabar cikin gida, suna fitowa sukayi karo da Alhaji, Hajiya Aina'u kuwa had'e rai ta k'arayi, Alhajine ya dubesu sama da k'asa sannan yayi gyaran murya yace "Hajiya ina zuwa haka da ranar ALLAHn nan?"
Banza tayi dashi tacema Dija "Ke maza zo mu wuce tsayuwar me kikeyi anan"
Hajiya Aina'u ji tayi ance "Tsayuwar ubanki takeyi anan, dama wannan iskanci kikeyi a gidan auran naki?, mijinki na tambayarki ina zaki amma kinyi banza dashi kamar yana magana da dutse, to wallahi nidakene dama goggoce mai d'aure miki gindi to wallahi zance na sameta naci mata mutunci"
Alhaji ne ya dafa kafad'unsa yace "A'a Imrana kar muyi haka dakai mana, kaima kasan inkaje kaima goggo fad'a akaina zatazo ta saukeshi tace na had'ata da yayanta dukda tana surukata, dan haka ka kyaleta kawai"
Imrana kallan Hajiya Aina'u yayi a wulak'ance sannan yace "Ubanwa ya baki izinin fita a cikin gidannan?"
Hajiya Aina'u shiru tayi kanta a k'asa dan kuwa tasan halin kawun nata tas zai zaneta dukda yawan shekarunta.
Tsawa ya daka mata yace "Ba dake nake ba?, ko nima zakimin iskanci da kikema mijin nakine? waigowa yayi wajan Alhaji sannan yace "Idriss wallahi hak'urinka yayi yawa dole wannan yarinyar ta rainaka da yawa gaskiya yaka mata ka zauna ka k'ara gyara gidanka" kallan Aina'u yayi yace "Kun wuce ko saina tattakaki awajanan"
Ai tuni Dija ta kama hanyar cikin gida, hakama Aina'u ta bita, tana zuwa falo ta fara zabga ruwan tijara da ashar tare da fad'in "Ai zaizo ya sameni wallahi, agabansa aka zauna ana cimin mutunci koya tanka, gashi wannan banzan yazo ya 6atamin shirina banzaaaa" ta k'arashe maganar a fusace, ruwa mai sanyi tasha sannan ta tashi ta shiga bedroom d'inta tana ta safa da marwa.
Wayan Phaty ne yaketa ruri, zuwa tayi ta duba taga ba suna, sai tak'i d'auka ta cigaba da abunda take, kira ake amma Phaty bata d'auka ba, dataji kiran yayi yawa ta d'auka a fusace "Wai wani mayene haka, mutum idan ya kira so d'aya yaji ba'a d'auka ba ai sai a k'yale mutum ko" shiru taji ba'ai magana ba, sai Phaty ta k'ara kara wayar a kunnanta tana fad'in "Hello, who is online?"
Dariya mai sauti aka saki a d'ayan 6angaran sannan yace "TEEMALASH uwar tsoro, yanzu dan baki da numbern mutum shine bazaki d'aga ba saboda yanzu kin zama babbar yarinya, bakya harka da k'ananan k'wari irinmu ko"
Phaty wani ihun jin dad'i ta saki tace "Oh my God sweetheart, bash, are you the one?, wallahi na kasa gasgata kaine fa, waceni ai kaine babban yaro kuda baka neman mutane, rabona dakai tun lokacin da amins ta had'a wani casu tace zan biga ta flight kuma time d'in aka samu akasi sai bamu tafi tare ba, but in ban manta ba ai nayi attending d'in chasu amma kai ban ganka ba, maiya hanaka zuwa a lokacin, kasan kwana biyu nayi missing d'in chasu"
Dariyar jin dad'i Bash yayi yace "Amma bazan 6oye miki ba naji dad'i k'warai da gaske da kika ganeni sharp-sharp, lokacin wallahi tunda naji Amins tana k'ila wa k'alan zuwanki kawai sai naji zuwan ya fitanmin araina, coz ni kinsan idan dake awajan komai yakemin dad'i wallahi, amma fa karki damu, akwai wani gagarumin party dana had'a kuma kece mutum ta farko dana fara inviting, shiyasa na nemo numbernki dukda nasha wahala kafin na sameta danna sanar dake da gaggawa, sannan kuma nidakene zamu farayin gaba dan nai mana booking d'in komai kece kad'ai nake jira"
Phaty shiru tayi nad'an wani lokaci, zuciyarta na zugata ga dama ta samu d'ayar zuciyar kuma tana hanata da wannan mummunar lamarin tana fad'in -"Kinsan halin Bash karr dan mugun d'an a hutane, ke kanki kinsan mane min matane ba kad'an ba, sannan kuma yasha alwashi saiya d'and'anaki kota wace irin hanya ce, gashi kinsan kina da rauni, da zarar Bash ya ke6e dake to mai k'watanki sai ALLAH, dukda nasan bazai miki dole ba amma gaskiya Bash shu'umi ne akan harkar romance, kul Phaty karki sake kije inda Bash yake, kin manta akan dole sai yayi romance d'inki kuka 6ata?, shine yanzu zai miki dad'in baki ya kaiki ga halaka, karki manta a ko wani lokaci Umar zai turo kinaso kijema da Umar unvirgin ne?"_
YOU ARE READING
PHATEENJIDDAH
ActionYana maganane akan yara guda biyu Wanda suka kasance tagwaye, gashi Allah yayi musu rashin basajin magana ko kadan, sannan kuma ina gargadin iyaye da su runka jan 'yayansu a jiki basu wancakalar dasu ba akan wani dalili nasu na daban,👭