2

642 18 2
                                    

_~ALƘALAMIN JIKAR NASHE

YA ABIN YAKE ?

LIttafin Nazeefah Nashe.

08033748387

Paid book

Follow me on wattpad

Nazeefah381

ELEGANT ONLINE WRITERS

(Haɗin kai shine takenmu.)
_2

Free Page






Tuni hawaye ya b'alle daga idanun
muneerah jin Abbu ya ce cikin zafin rai "Da izinin ubanta, kin ga sakina ki kiyayeni wallahi, ke Muneerah zo ki wuce kije kinji Allah yayi miki albarka." Fuskar Ammi a ɗaure take jifa masa kallo mai cike da bala'i Ai kuwa Muneerah na fita ta sauke kwandon masifarta a kansa. "Na fa gaji da wannan rainin hankalin naka ba zaka dinga juyani kamar wata Ƴarka ba,ban maka dole ka zauna dani ba, haba ina dalili kayi ta sakin nawa mana sai me? Daɗin abin ba cusa maka ni aka yi ba, har ƙasar mu kaje ka yaudaro iyayena ka auro ni." tsaki yaja kawai ya fice yana jinta tana sake faɗar aikin banza, kuma wallahi ba wata shegiya da zan bari ta riƙe min ƴa, a barni idan ma kasheta zan yi na kasheta ai ta wace." Abbu girgiza kai kawai yayi yana mamakin Sakina da ko kaɗan bata jin nauyin furta masa duk maganar da tazo bakinta. A kullum kuma sai tayi wannan zancen na ba cusa masa ita aka yi ba wanda yasan gori ne kawai take wa Sadiya tunda itace aka yi musu auren haɗi. A zahiri ya ce "Ai fa, ko baki faɗa ba da zan iya nima da na sahhale miki, saboda na gaji da matsalolinki matsalar ɗaya ba zan iya ba, duk wannan hargagin a baki ya tsaya Allah ya riga ya jarrabeni da tarin ƙaunarki da ya riga ya zama jinin jikina, bana jin ma zan iya rayuwa babu ke, amma shi kaɗai ya san wahalar da take bashi wanda take rufe idonsa daga aikata adalci tsakaninta da kishiyarta duk da tarin haƙuri da biyayyar da Sadiya take masa amma sam baya mata so koda kashi ɗaya cikin goman da yake yiwa Sakina ya rasa irin wannan masifa ko fushi tayi dashi yana rasa sukuni har sai ta sauko yaga murmushinta sannan ya ke sakin ajiyar zuciya ta samun kwanciyar hankali. Bai sani ba ko don kasancewarta daga jinsin larabawa,shi yasa ya ke mata kallon tafi sauran mata?


_________________________________

Da sauƙi sosai a yanayin da ta samu jikin ƴar uwartata Muneerah ta sakar mata cute smile kafin cikin tsananin ladabi ta durƙusa ta gaida Mahmah, ita dai tana ganin mutuncin matar nan duk da ƙoƙarin cusa musu tsanarta da Ammi take. Sadiya ta shafa kan Muneerah kafin ta furta "ƴar albarka yau ba'a tafi Islamiyyar ba?" murmushi ta saki tana ajiye basket ɗin hannunta ta ce "Zuwa nayi na zauna kije gida ki huta kada su Humaid su buƙaceki don na jiyo rigimarsa ma da zan fito da na tambayi Saliha mai aiki sai ta ce wai Islamiyya ce ba zai je ba." Riƙe haɓa Mahmah tayi tace "Kiji min ja'irin yaro amma Humaid akwai ɗan kirki shikkenan bari naje na dawo bayan la'-sar sai na kwana da ita, kinga ai ba za'a barki ke kaɗai ba naga ma jikinnata da sauƙi ƴar nema ta sha allurai." Ta faɗa tana shafa gefen kumatun Hamda da haka kawai take mata wata irin ƙauna ji take kamar jininta kamar kuma daga tsatsonta ta fito. Hamda ma rintse ido tayi tana ayyana da ana shawara da mutum kafin yazo duniya da tace ita tafi son zuwa a tsatson Mahmah mace saliha mai kyautayi jin ƙai da bata ɗau duniya a bakin komai ba. Banda tata uwar da ta tattara duk saɓanin halayen Mahmah a hankali ta ce "Nagode Mahmah sai kin dawo." Haɗe rai Mahmah tayi tace "Kul na sake ji, ba godiya tsakaninmu yarda na ɗauki ƴaƴan cikina haka na ɗaukeku zan iya yi muku duk wata hidima da ta kama uwa zata yi ga ƴaƴanta Ubangiji Allah yayi muku albarka gaba ɗaya." suka amsa da ameen gaba ɗaya suna bin bayanta da kallo har ta fice daga bigiren da suke. Muneerah ta saki ajiyar zuciya a fili ta furta Mahmah Uwace ta nunawa ayi alfahari da ita ubangiji ka shiryi Ammi itama. Hamda runtse ido tayi kafin ta ce ameen cikin rawar murya da gaske tana jin raɗaɗin da ya ninka na Muneerah a ranta.

Da yamman kuwa Sadiya ta yakice duk wasu tarin ayyukanta duk da yawan da suka yi mata, kasancewar Didi mahaifiyar mai gidansu a gobe ake saka saukarta daga ƙauyen Gwarzo kamar yarda ta saba duk shekara a watan azimin tsofaffi take zuwa sai kuma ta tafi bayan sallah babba bayan ta dawo daga aikin Hajji. Idan kuka lissafa zaku ga wata shidda take a kano tayi watanni shidda a gwarzo. Macece mafaɗaciyar gaske kuma idan tazo duk wani iya shegen Ammi sai dai tayi shi a bayan idonta kasancewar ta san ba ita bace ƴar gaban goshinta asali ma tun sanda ta bayyana muraran a matsayin matar ɗanta ta nuna mata tsana ba tayi farin ciki ba sam da auren nasu. Duk da dai bata nuna mata baƙin hali amma fa kaifi ɗaya ce kana yi zata kiraka ta gaya maka gaskiya ko mai zaka yi kuwa. Ga shi Allah ya zuba mata kwarjini da duk tsaurin idonka baka isa ka kalleta ka gaya mata magana ba sai dai a bayan idonta. Ba kuma ta son ƙazanta kuma duk sanda tazo dama janye Hamda take ta mayar sashenta.

Ƙyale Sakina kawai tayi ba don tafi ƙarfinta ba sai don tana son taga ƙarshen rashin mutuncinta, tana so kuma ubangiji ya shayar da ita ruwan mamaki shi yasa ma bata ɗauketa ba don idan ta ɗauketa tabbas Sakina taci riba a wajensu tunda ta bayyana ƙarara kenan ita take juya su.

Shirye-shirye da gyaran ɗakin ya hana Mahmah zuwa asibitin sai bayan ƙarfe biyar, sannan ta tafi bayan ta tura Humaid gidan yayansu na biyu Hamidan ya kwana, don idan ta barshi da Saliha wahala zai sha, da Hamood yana nan ne ma da sauƙi to ya tafi karatu can ƙasar Egypt.


Da Abbu suka tafi asibitin, suka bar Ammi a jikin window sai cizon yatsa take ganin yarda suke tafe cikin nishaɗi sai tuntsira dariya suke, wato ita ya mayar ƴar banza bai damu da ɓacin ranta ba tana sane taƙi fita gyaran ɗakin Didi, duk don ta samu ya kulata amma kamar ya san manufarta ya tattara ya watsar da ita da kansa ya zage aka yi aikin dashi da Mahmah don a dokarsa bai yarda ƴan aiki suyi masa aikin uwarsa ba don ƙarara ta nuna masa bata so kasancewarta mai tsafta da tsantseni.

Kamar ya san tana lafe a window tana kallonsu ta taga ya buɗewa Sadiya ƙofar motar yana jifanta da wani irin murmushi da ya tunzira zuciyar Ammi taji wani kishi yana katantawa da ita, har yau ta kasa iya danne kishinta akan Sadiya duk da ta fita da komai amma haushinta take ji sosai tana tunanin duk duniya ba wanda ta tsana sama da Sadiya musamman da tayi mata zarra wajen haihuwar ƴaƴa maza don ita kaf ƴaƴanta biyar maza ne ba mace ko ɗaya abinda yake sake baƙanta ran Ammi kenan musamman idan kalmar ' Sadiya taci gida'. Ta faɗo dodon kunneta da mafi yawan akasarin mutane suke faɗa musamman a wajen taron biki ko suna na dangin mijinta, kai har da ma na mutuwa ta sha ji ana mata gori ko don mutanen sunyi la'akari da yarda maitarta ta fito a fili na son haihuwar ƴaƴa maza ne shi yasa ake jifanta da zancen? Da sauri ta saki labilan tana runtse ido tuno da maganar da likita yayi bayan haihuwar Hamda ya tabbatar mata da ba zata sake haihuwa ba saboda mahaifarta ta taɓu dole aka juyata haka dole tana ji tana gani burikan ta suka bi iska, tayi burin haihuwar ƴaƴa maza ita ba don gado bama don son taje gidajensu ta shimfiɗa mulki kamar yarda Didi take shimfiɗa mulkinta a gidajen nata yaran. Tana jin tashin motarsu ta saki tsaki haɗe da furta zaka biyo dare ka nemeni ne wallahi kayiwa kanka sai nayi sati ban baka haƙƙinka ba, ta tabbata kuma sai ya kusa suma don idan tayi masa yaji ko na kwana ɗaya ne ranar girkinta zama yake yayi mata kuka yana roƙonta, don da gaske shi kaɗai yasan ruwan zallar daɗin da yake kwankwaɗa a jikinta balle sati! ta saki murmushi da ta tuna haɗaɗɗiyar zumar da ta siya da zata kusa zautar dashi a zahiri tace gidan ka tarar.



_____________________________

Da sauƙi sosai suka sameta don likita ya tabbatar musu zuwa safiya ma idan drip ɗin da ake saka mata ya ƙare za'a iya sallamarta. Mahmah da kanta ta zauna tana bata kunun gyaɗar da ta damo mata ta sha kuma sosai har sai da tayi gyatsa. Abbu murmushi kawai yake yana sake jaddada kimar Sadiya a zuciyarsa, da gaske ɗin ita ta dabance zuciyarta mai kyauce,Mai halin mutanen farko shi yasa kullum yake mata kirari da Hali dubu.

Kashegari kuwa aka sallamesu, ko kafin suje gida tuni Mahmah tayiwa Saliha waya ta ce ta gyara mata ɗakin da yake kusa dana Humaid nan zata saka Hamda a ciki, duk da bata da tabbacin uwarta zata yarda sai dai wannan karan Abbu ya. tsaya kai da fata ya ce dole nema ta yarda tunda ita bata sonta bata isa ta hana wani riƙeta ba.

Suna shigewa sashenta Ammi ta fito a sukwane cikin bala'i ta shiga ɓangaren Sadiyar tana zuwa ta shiga surfa bala'in sai an fito mata da ƴarta ai ba uban wanine ya haifa mata ita ba matar shige kawai borar gida" Sadiya murmushi ta saki kafin ta girgiza kai ta ce"Wallahi ba zata fito ba sai dai idan Ubanta ne yazo ya fitar da ita da kansa, kuma alhamdulillah borar gida ita ta zama uwar mazan gida mowa kuma ta haifi mata...... Wani kukan kura Ammi tayi, tayi kanta yasa na runtse ido don na tabbata ba za'a kwashe da daɗi ba.

Ku hanzarta biya Ya Abin Yake? Daban yake da sauran.

Ya Abin Yake?Where stories live. Discover now