25

384 3 0
                                    

25 Ya dad'e a bakin k'ofa yana knocking kafin Nanna ta mik'e zuciyarta a tunzire ta bud'e k'ofar. Idanunsa cikin nata ya hango tsananin b'acin rai kwance a fuskarta.
Ko kallo na biyu bata sake yi masa ba ta juya da sassarfa zata shige ciki da sauri ya jawo hannunta ya damk'e sosai ta yarda ba zata iya gudu ba. Ya rutsa ta a bango sosai ta yarda ba zata iya wani motsi ko gudu ba. Ya kuma kakkafeta da ido kaifin idanunsa da suke yawo a jikinta ya sa ta runtse idanunta tana jin hakan yana tasiri a ranta ya kuma sauya bugun zuciyarta a lokaci guda. Hammad ya san ta kan zuciyar mata yana siye zuciyar mace ko bata shiryaba balle ita da soyayyarsa ta game zuciyarta gaba d'aya bata jin zata iya sharing d'insa da ko wace mace shi yasa da ta kwana ita kad'ai a gado d'aya lamarin ya gigita ta dan hakan sabon abune a wajenta. Bai tab'a faruwa ba a tsawon zamantakewar su ta aure. Ganin ya kwantar da b'acin ranta ta hanyar da ba ta zata ba ya sashi sakinta yana mayar da
Numfashi kad'an ya ce "ina yaran su fito na yi dropping d'in su kada su yi late." Ta so ta sake yi masa mita sai dai ta san shi mutum ne da baya son ya lallab'aka ka botsare don shi idan ya tashi rigimarsa ta fi tata. Jikinta a sanyaye ta juya duk da hancinta ya juyo mata k'amshin turaren da ba nasa ba a jikinsa. Amma ta bar abin a ranta don ba yanzu bane lokacin magana zata yi bincike da kanta idan kuwa ta tabbatar da wata ce take tarayya da mijinta a waje tabbas mai raba da ita sai lahira. Ta fad'a zuciyarta na matsanancin bugu saboda tsananin kishi. Ganin irin kallon da
Take masa ya tabbatar masa rigimar tana nan jira take ya dawo ta sauke masa ita kwando-kwando murmushi kawai ya saki a zuciyarsa ya ce dama kin adana rigimarki nan gaba kad'an zata yi miki amfani.

____________________

Cikin dare ta gama shirinta tsaf cikin wasu irin sihirtattun turaruka masu gigita d'a namiji ko bai shirya ba. Wani chewing gum mai masifar k'amshi ta cilla a bakinta ta tsaya gaban mudubin d'akinta tana sake turare sussulb'an gashin kanta da abin turara ga shi. Ita kad'ai take sakin murmushi bayan ta bi jikinta da kallo ta ga irin yarda yauk'akkar rigar barcin ta bi lafiyar jikinta ta kwanta luf iya kacinta gwiwa ta kuma fitar da duk wani shape d'in ta na halittun Y'a mace. Har a wannan lokacin saboda gyara da take wa jikinta halittunta suna nan tsaf kamar na wata budurwar shape d'inta da surarta sam ba su jirkita ba saboda yarda take maintaining d'in su.

Tattausan silifas d'inta ta saka sannan ta kawo dogon hijabi ta saka tana murmushin mugunta don tabbas yau mai kwatar Abbu a hannunta sai ya shirya. Ita kad'ai ta san bam d'in da ta had'a masa ta yarda duk umarnin da ta ba shi zai bi ba wani musu.

A falo ta sameshi yana kallon BBC london. K'amshin turarenta ne ya sanar da shi zuwanta ya d'ago yana sakar mata tattausan murmushi. Kafin ya yi aune ta cire hijabin ta hullar guntuwar rigar barcin da kad'an ta wuce gwiwa ta bayyana Santala-santalan cinyoyinta. Abbu kusan sumewar zaune ya yi don ta dad'e bata yi masa wannan shigar ba sai ya ganta tamkar ranar da suka fara tarewa a matsayin amarya da ango. Cikin tafiyar jan hankali da lank'wasa jiki ta k'arasa wajen sa tana sakar masa wani irin murmushi had'e da kallo mai rikitar da y'an maza sam bai san sanda ya yi mata masauki a cinyarsa ba bayan ya ji sunan da ta rad'a masa a kunne k'albeey barka da dare.

Karfe biyun dare ta sake gyara kwanciyarta a jikinsa tana rik'e da hannunsa ta ce "K'albeyy akwai fa abinda yake damuna." Gashinta ya shafa sosai yana jin kamar ya mayar da ita cikinsa "Gaya min damuwarki ko ta mecece kin ji Dearling." Ta sake narkar da idonta cikin nasa "Kalbeey me yasa Asma'u ta takurawa rayuwata? Ban san me nayi mata ba yanzu fa zuga Didi take a zuwan ni na yi mata asiri. Fisabilillah in rasa wacce zan yiwa asiri sai matar da nake wa kallon mahaifiya. Ni ban san me yasa y'an uwanka basa sona ba ko don na zamo bare a cikinku ni ba k'abilarmu d'aya ba." Ta fad'a tana sakin wani irin kuka na tashin hankali. Ran Abbu kam ya kai k'ololuwar b'aci. Don ba abinda yake d'aga masa hankali irin ya ga Saknansa tana kuka. Ji yake kamar ya mik'e a daren ya je ya ci mutuncin Asma'u. Cikin takaici ya sake janta jikinsa sosai ya fara aikin lallashi ita kuma ta samu abinda take so ta shiga jera ajiyar zuciya a hankali tana sake masa mita da yi masa famfo akan y'an uwansa tuni ya hau kai ya zauna ya k'addara tilas ya yi maganin Asma'u da safe. Murya a k'asa ya rad'a mata a kunne ki yi hak'uri dearling da safe zata tattara ta tafi gidan mijinta ai Didin ta samu sauk'i. Babu mai tab'a min ke wallahi na k'yaleshi yau na sake amicewa da har abafa kece mahad'in zuciyata." Dad'i ya shigeta da farinciki ganin yarda ta juya shi ba boka ba malam sai zallar iya sarrafa shimfid'a ta shiga wasa da gemunsa tana jaddada fad'in "Thanks Kalbeey zaman Asma'u ai masifa ne a gidannan." Burinta ya cika Asma'u na tafiya zata zuba guba a abincin Didi kuma a na gidan Sadiya zata zuba mai aikinta zata siye da mak'udan kud'i ta bata ta zuba gubar. Ta saki murmushin tarin farin cikin samun nasara a lokacin da ta sare.
Dama sau tari shi yasa bata fiye yarda da malamai da bokaye ba da kanta take sarrafa mijinta son ranta.

_________

Da sasafe suna gama shiryawa da Abbun ta had'a masa lafiyayen breakfast cikin tarairaya ta dinga bashi abincin a baki tana yi tana sake ingiza shi game da Asma'u da Lauratu k'annensa. Shi kuma hakan yana sake tasiri a ransa ya tabbatar shine basa so tunda ba sa son Saknarsa mai ba shi farin ciki a ko da yaushe. "Tashi muje dearling a yi komai a gabanki." Ta mik'e cike da farinciki ta manna masa sumbata a gefen kumatu ya saki murmushi ya ja hancinta a cikin kunne ya rad'a mata "Shi yasa a ko ina nake alfahari da samun mace kamar ki." Ta lumshe idanunta suka fita tana sakin shashshek'ar dariya ta tabbata yau lamarinsa da Asma'u ba mai kyau bane.

A falo suka samu su Didin da Asma'u suna karya wa. Abbu cikiciki ya yi sallama ita kuwa Sakna da alamar shak'iyanci a muryarta ta yi sallamar tana jifan Asma'u da kallon mugunta. A gefen Didi ta durk'usa murya cike da ladabi ganin Abbun ta shiga gayar Da Didi shi kuma Abbun yana lura da kallon banzan da Asma'u da Didin suke jifan Saknarsa da shi. Ya tabbatar da abinda Saknan ta ce don haka ransa ya yi k'ololuwar b'aci ya kalli Asma'u a fisge ya ce "Ashe abinda ake gaya min gaskiya ne, nema kike ki haddasan wutar masifa a gidana. Idan banda haka me baiwar Allahn nan ta yi miki tunda ta shigo kike wurga mata harara." Asma'u da Didi suka saki baki suna masa kallon mamaki ganin yarda yake masifa da kumfar baki son ransa. "To ni ba zai yiwu ba gaskiya Didi ta tattara ta koma gidan mijinta ai suna da masauki anan garin. Tunda dai Allah ya baki lafiya kuma zan samo miki abokiyar zama ko a cikin dangi ne amma dai Asma'u ta bar gidannan." Didi ta gyara zamanta ranta a b'ace tana girgiza kai da gaske lamarin nasa ya fara fitgitata ta shak'a sosai kafin ta gama jin tijararsa "Ba Takka, to tannu Utmanu don dai a wannan jallin ka wuce d'a te dai miji ko uba. To bud'e kunnenka da kyau ka ji babu inda Atma'u zata je har te tun tati tafiya, te dai idan har ni zaka had'a ka kora tatata kawai da mace ta riga ta gama da ti. Ina jiye maka lanal da na tani Ummaru ko hakkin Tadiya kawai ya iteka ya hanaka kwanciyar kabali." Didi ta dinga masifa sosai ya dad'e ma bai ga b'acin rai kwatankwacin wannan a fuskarta ba. Ta wurgawa Sakina harara a zafafe ta ce "Munafuka lana dubu da ta b'alawo ce lana d'aya ta mai kaya." Sakna ta fice jikinta a sanyaye idanunta suna Kawo ruwan hawaye na rashin samun nasara. Asma'u kuwa tana zaune mamakin d'an uwanta ya hanata magana ji take kamar ta fito da recording d'in nan amma tana tunanin akwai sauran lokaci.


______________

Yana zubesu a makarantar ya jiyo, ji yake kamar ya koma wajen Hamda amma ya San bai Isa ba. Dole ya koma wajen uwar gida sarautar mata ya goge mata abinda ya tsaya mata a zuciya.

Tas ya sameta ta yi wanka ta tsuke cikin kananan kaya. Gidan sai zabga k'amshi yake. Ga chicken peppe soup ta yi masa da chips da egg. Tana zaune zuciyarta sam babu dad'i saboda yarda take jin tamkar zargin mijin nata yana nema ya d'arsu a ranta. Ta sake bin jikin ta da kallo ta ganta tsaf a hasashenta.Tana son saka wando da riga sai dai k'ira da dirin jikinta ba na wando da riga bane. Kallonta yake sosai ganin duk don shi Tayi wannan kwalliyar sai dai da zai bata shawara da yace ta dinga shigar hausawa sun fi yi mata kyau akan wad'annan matsatstsun kayan da take sawa. Ganin kallon da yake wurga mata ne ya sata murmushi a tsammaninta ta gama gigita tunaninsa ne. Don haka ta mik'e tana kashe masa ido d'aya duk da tana jin haushinsa amma tana kewarsa sosai ta fad'a jikinsa had'e da sakar masa kyakykywar runguma cikin wani irin zak'uwa take furta masa "Me yasa kake neman canja mana farin Cikin da
Muka rayu da shi ne, kasan jiya kuwa a yanda na kwana jina ni kad'ai a gadonmu sai turarenka da ya bi ya addabeni please me yasa ka kwana a wajen aiki?" Kokarin zame jikinsa yake amma tak'i ba shi damar hakan sai sake narke masa take don dole ya biye mata a ransa yana ayyana ta matsanta masa.

Sai da ta samu nutsuwa sosai sannan ta bi shi da kallo suna kwance a gadon ta ce masa "K'amshin turaren da na ji a jikinka ya barranta da naka,Kayan da ka dawo da su ba da su Ka fita ba. Menene dalili?"
Ta fad'a tana jifansa da kallon da tuhuma.."

Ya Abin Yake?Where stories live. Discover now