_~ALƘALAMIN JIKAR NASHE
YA ABIN YAKE ?
LIttafin Nazeefah Nashe.
08033748387
Follow me on ArewaBooks
@nazeefah
https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e
ELEGANT ONLINE WRITERS
(Haɗin kai shine takenmu.)
_3Ya abin yake?
Daban yake da sauran.
Da sauri Sadiya ta fincike wuyanta
haɗe rai sosai tayi ta ce "kada ki fara kada kiyi wannan kuskuren, ko ina yarinya ban yarda da dambe da kishiya ba, balle yanzu da nake da ƴaƴa da jikoki har da surikai."A zafafe Ammi ta ingijeta tare da ɗaga hannu zata zabga mata mari dai-dai lokacin da drivern Didi ya danno hancin motarsa cikin gidan tare da sakin gigitaccen horn, bisa bin umarnin Didi don sanar da masu gidan zuwanta, wanda hakan shine tambarinta.
Cak Ammi tayi da hannunta cikin matuƙar ɓacin rai da haushin bayyanar jarababbar tsohuwar, tayi tsaki ta fice daga sashen Mahmahn da sauri don ta san tabbas Didi tazo ta tarar da wannan tashin hankalin ranar na lahira ma sai yafi ta jin daɗi. Mahmah tayi murmushi kafin ta furta "Gaba da gabanta"da ki tsaya mana. Sannan tayi azamar fita don tarar Didin.
Fuskar Didin a washe take kallonta, da duk jama'ar gidan tana amsa gaisuwarsu cike da murnar samunsu lafiya, ahalin Sakina ne kawai bata gani ba. Bata damu kanta ba ta san dalilinsu na ƙin zuwa bai wuce ba sa son tayi musu gorin rashin aure ba, alhali ba mijin suka rasa ba suna dai jiran wanda ya ci ya tada kai.
Murya a cunkushe ta kalli Sadiya ta ce"Ita hakimar kishiyar taki tana ina?"
Mahmah ta ɗan yi jim kafin ta ce "Ina ji sallah take tunda baki ganta ba." ta samu kanta da gillara ƙarya duk don ta gyara lamarin. Didi ta kalli agogon hannunta kafin ta ce "Sallahr walaha take Kenan da sha biyun rana? Sadiya kenan kishiya kike karewa don kada nayi mata sababi? ai ba tun yau na san Sakina bata ƙaunar taga nazo gidannan ba, saboda bata son na sawa yaranta ido to wannan karan a shirye nazo tsaf wallahi ba zan bar gidannan ba sai na aurar da iyayen matan da ta girke a ɗakinta, su ba zawarawa ba su ba ƴan mata ba, shi kuma soloɓiyin mijinku ya saka mata ido sabida baya son laifin balarabiya."Sunkuyar da kai Sadiya tayi kafin ta ce "Kiyi haƙuri Didi ai aure lokacine da zarar lokacinsu yazo ko suna so ko basa so sai sun yi."
Dai-dai lokacin da Ammin ta shigo kuma duk wani sababin Didin akan kunnenta take yi ranta ya sake ɓaci shikkenan wannan matar zata zo ta ɗaga mata hankali.
Fuskarta ba yabo ba fallasa tayi sallama haɗe da faɗawa cikin parlourn. Didi ta zuba mata ido tana jijjiga kai ganin yarda Sakinan ta cono ɗankwali har gaban goshi,alamar dake nuni da cewa a shirye take da amsar duk wani rashin mutunci na Didin.
Murya a cunkushe ta fara gaisheta Didin ta yamutsa fuska kafin ta ce "Ai Sakina da kin bar gaisuwarki tunda ba dole nace sai kinzo kin gaisheni ba, ba buƙatar ta nake ba gaisuwar da za'a yiwa mutum ana faman ɗaga hanci dai-dai nake dake wallahi, ki bini a hankali kafin ki kaini bango." Sakina dai ɗan murmusawa tayi wanda direct zan iya kiransa dana rainin hankali ta miƙe cike da izza tace "A huta lafiya Didi" daga haka ta kaɗa zaninta ta wuce ta bar Hajja Didi da hangamemmen baki don kuwa ta hango raini tsagwaronsa a fuskar Sakina, girgiza kai tayi kawai tana kallon Sadiya tace "Shahara iyye! Cabd'i jam" girgiza kai itama Sadiyar tayi ita kanta tana mamakin yarda Sakinah ta fetsare har haka? Didin da ko ido mutane basa iya haɗawa da ita idan tana magana. Ita dai murya a sarƙafe ta hau bata haƙuri sannan ta miƙe don ta bawa Didin waje ta huta har ta kai bakin ƙofa Didin tace "Ina Hamda ne ban ganta ba ko bata gama gallafirin makarantar kwanar bane?" Sadiya ta girgiza kai ta ce tana ɓangarena bata da lafiya ne yau ma aka yi discharging ɗinmu daga hospital ai da tuni kin ganta ta fito."
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.