15

585 12 3
                                    

ALK'ALAMIN JIKAR NASHE

(Mai tak'ama da ikon Subhana)

YA ABIN YAKE?
08033748387

Follow me on ArewaBooks

@nazeefah

https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e

On Wattpad @Nazeefah381

Last free pages.

15
✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽
__________________________________

Da sauri Sakina ta fito daga bedroom d'inta, hankalinta a tashe dafatan Munira bata ji abinda take cewa mahaifiyarta a waya ba.

Turus tayi ganin Muniran a k'asa tana dafe da gwiyoyinta hawaye shab'e-shab'e a fuskarta, alamarta ya nuna kamar fad'uwa tayi. Sakina ta saki ajiyar zuciya kafin ta ce "Ke kuma lafiya cikin darennan kike kurma uban ihu?" Munirat ta tattaro duk wata nutsuwa Ta saka a fuskarta, bata son Ammin ta fahimci ta ji zancen da take, ta san idan har ta gane zata iya d'aukan ko wane mataki a kanta, don haka murya na rawa ta ce "Ciki na ke azabar ciwo, kuma na zo amsar magani sai na zame anan." Ammi ta saka hannu ta mik'ar da ita had'e da fad'in Ayya muje ki sha maganin to, ko dai period pain ne?" Ta girgiza kai jikinta a salub'e, kafin ta bi bayan Ammin zuciyarta na sake mamakin halayyar Ammin.

Tana shan maganin tayi saurin ficewa daga d'akin, nutsuwa take buk'ata gami da dogon nazari akan maganar nan da ta jiyo, tabbas biri yayi kama da mutum, amma waye uban Hamdan shine abinda ta kasa ganewa.

Ta dad'e tana juyi a saman gadonta dafatan barci ya kwasheta amma ina wannan dare kam tuni suka yi hannun riga da barci, ciwon cikin ma tuni ta neme shi ta rasa, k'wak'walwarta ta tafi dogon nazari, tunaninta ya tsaya cak zuciyarta na wani irin bugu bata son abinda take tunanin ya tabbata, bata fata ko kad'an idan hakan ta kasance ba Ammi kad'ai ba su kansu abin kunya ne a wajensu.

HAMMAD zuciyarta take ta bata a matsayin uban da yayi cikin Hamda, idan ba haka ba me zai saka y'arsa tayi kama kwabo da kwabo da Hamda, kamar da kana gani ko ba'a fad'a maka ba zaka san sun had'a jini d'aya. Ta runtse idonta wasu hawaye na zubo mata, ya zama dole ta fallasa sirrin nan, ko Ammi Ta hankalta ta nemi tuba ga Allah, Sannan zuciyarta itama ta huta da dogon tunani, idan ba haka ba kuwa tabbas zuciyatta zata buga. Ranar dai kam akan idonta aka yi kiran Assalatu abinda bata tab'a yi ba kenan a rayuwarta.

_________________

Sukuku ta tashi da safen, duk da barcin da yake rinjayar idonta, amma ba zata iya yi ba, Neman wanda zata tunkura da zancen take direct zuciyarta ta amince ta jewa da Anty Lauratu da zancen idan yaso ta gaya mata kada ta sake ta ce ita ta gaya mata.

Ko da ta fito parlour suna zaune suna karyawa gudun kada Ammin ta jefa ayar tambaya a kanta yasa ta zauna ta fara tsakurar abincin, tana turawa da kyar kafin ta mik'e tana zarar tissue, Ammi ta kalleta "Ke kuma sai ina ina ce yau baki da
Lectures?" Munira tayi saurin girgiza kai tana gyara farin glass d'in da ke idonta ta ce "Ammi ina da group discussion amma ba zan dad'e ba zan dawo." "Ai shikkenan ki dawo da wuri don mu zamu je gidan Kady yayunki suna da bak'i kuma kin san bana son barin shiyyata ba kowa." Da sauri ta d'aga kai tana ficewa daga parlourn tana jin Najma na cewa ta tsaya tayi dropping d'inta a motar Ammi amma ta zura da gudu, gwara ta shiga napep ba ta san kowa ya san inda zata, musamman Lauratu da bata shiri da Ammi, shi yasa ma Ammin bata bari suje gidanta.

A bakin gate d'in gidan mai a daidaita sahun ya ajiyeta ta zaro d'ari biyar ta bashi kafin Ta saka kai Ta shige had'e da cewa ya bar canjin.

Lauratun ce kawai a gidan duk yaran sun tafi makaranta, dama babbar y'arta sa'ar Hamda ce. Cikin mamaki take kallon Muniran ta ce "Ikon Allah yau kece a gidan amma dai Sakina bata san nan kika zo ba? Kuma fa yanzu da kika ganni mayafi nake shirin yafawa yau nace a wajen Didi na zan wuni"
Munira murmushin yak'e ta saki kafin ta ce "Ya naji gidan shiru?" Lauratu ta ce "Wa zaki samu duk sun tafi school daga ina haka?"
Tana murmushin ta ce "Daga gida mana" Lauratu ta sake gyara zama ta ce "Amma dai ba lafiya ba? Don haka kawai Sakina ba zata bari kizo gidan nan ba, haka kawai ta cusa muku k'iyayyata." Munira ta ja fasali kafin ta ce "Wallahi, Amma ba k'alau ba wata gagarumar magana ke tafe dani amma ban san ta yarda zaki d'auki abin ba, ko ma ta yaya kika d'aukeshi please kada sunana ya shigo." Nan ta shiga bata labarin da ya hautsina kayan cikin Lauratu kafin ta gama kuwa gumi ya jik'ata sharkaf duk da sanyin a.cn da yake parlourn, hankali tashe ta mik'e tana struggling a parlourn ta ma rasa abin cewa illa zuciyarta da take wani irin duka, fatanta da burinta a lokacin kada Allah yasa hasashenta ya zama gaskiya, duk da komai ya nuna kansa k'uruk'uru tun a lokacin da ace sun kasance mutane masu tsinkaye da sun fahimci abinda yake tsakanin Sakina da Hammad, kafin cikin Hamda ya bayyana, me yasa idanunsu suka rufe suka kasa gano dalilin takun sak'ar Sakina da Hammad, lokaci d'aya yaron ya juye ya zama mai bak'ar zuciya, ya kuma tsani had'a inuwa d'aya da Sakina Why? Lauratu ta fad'a da k'arfi had'e da rotsa wani verse da yake gefe a fili ta furta tabbas Sakina ta cucemu idan har hasashen mu ya zama gaskiya, tayi wa zuri'ar d'an Borno mummunan tabon da zai bi mu har kan tattab'a kunnenmu a ina aka tab'a yin haka?

Ya Abin Yake?Where stories live. Discover now