Na raunana ganina a kansa sosai, bisa son tilas na nuna masa ni d'in ma a cikin matsananciyar kewarsa nake "Ka yi hak'uri Umar, kamar yau ne zaka ga na haife cikin nan mun komawa auren mu cikin yardar ubangiji." Ya girgiza kai cike da sakin wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ya ce "Shikkenan, Allah ya raba lafiya, yasa wannan karan ki haifi namiji tunda na san shine burin zuciyarki." Na amsa da ameen cike da farin cikin jin addu'ar da nake so daga bakunan mutane masu albarka.
Daga lokacin na shiga rainon cikina, duk da kullum Umar a lissafe yake da watannin cikin, ganin yana son ya titseyeni akan ya kamata cikin ya isa watanni bakwai amma ya ga baya girma." Hankalina tashe na samu Kady da zancen ita ta ba ni shawarar mu samu wani likitan mu siyeshi ya gillara masa k'aryar cewa akwai matsalar da tasa dole watannin cikin suke komawa baya, don haka zai iya k'ara watanni uku ko fi akan lokacin haihuwarsa. Likitan ya tsara shi sosai ta yarda ba ta inda zai yi ya musa tunda ba aikinsa ba ne. Kady duk da haka ba ta amince ba, sai da tasa muka dangana gidan Malamai ta sa aka rufe bakin Umar akan zancen cikin, sannan aka rufe bakin Hammad ta yarda duk sanda ya tashi tona asiri zai ji ya kasa. Na amince da shawararta da tunanin duk duniya ba ni da aminiyar da ta zarce Kady, a dai wannan lokacin.
Tun cikin yana wata uku na je scanning, sai dai likita ya tabbatar min bai zama lallai a wannan lokacin a ga abinda Zan haifa ba, ma'ana jinsin mace ko namiji, na bari ya shiga wata na biyar tukun.
Munafukin likita shi ya dinga shirga min k'aryar namiji zan haifa tun bayan da yaga zuciyata ta d'anfaru da son haihuwar namijin. Na dinga shirye-shirye na sakankance da hakan a zuciyata. Har mafarki nake da suffar jariri namiji mai kyau da zan haifa.
Abin haushi, mamaki da takaici, ranar haihuwa da na tashi sai na haifi mace, duk da Didi ta b'oye min a sanda aka yi haihuwar. Sai cikin dare lokacin na farka daga barci ta isheni da kuka na yi tunanin pampers ne ya dameshi, ina zare masa na ga mace ce, Allah ne shaida ta k'iris ya rage ban yi cilli da ita ba. Zuciyata ta tunzira ban san sanda na saki wani irin kuka ba. Hankalina tashe na tafi da ita wajen Didi don bana jin zan shayar da ita.
Daga wannan ranar na tsani mai gadi na ji babu amfanin zamansa a gidan tunda ya kasa ba ni farin cikin raina, tabbas idan ina ganinshi wata rana zuciyata zata iya fashewa musamman idan ina tuno yarda muka had'a jiki da shi. Sai na ji na tsani kaina. A kashegarin ranar da na haihu ne na samu Umar da zancen mai zai hana a sirrance mu yi auren da Buzu sai ya sake ni a take a wajen ko kashegari idan ya so sai a sallameshi ya koma garinsu da alheri mai tarin yawa.
Abbu kuwa babu ja ya amince da buk'atata, dama yana tunananin wanda zai aura min a sirrance kuma ya amince ya sakeni ba tare da duniya ta ji ba.
Suka keb'e da Buzu ya sanar da shi k'udirinsa, Buzu ba wani jainja ya amince suka wuce masallachi na can wani gari aka sake mayar da auren mu da buzu, duk da dama da aurensa a kaina. Kashegari kuma ya dank'ara min saki Umar ya sallameshi ya tafi ba mu sake ganinsa ba, kuma ba mu san inda za'a same shi ba, abu d'aya na sani ya ce min shi mutumin Ethiopia ne wato k'asar Habasha. Ina rok'onku don girman zatin Allah ga duk wanda ya ji haushi ya yafe min sharrin zuciya ne da na shaid'an."
Ta na gama bada labarin ta saka wani irin kuka. Duk jikin mutanen wajen saki ya yi, tsananin mamakin cukurkud'dden lamarin ya sa suka gaza cewa komai illa sakin ajiyar zuciya. Hamda kuwa kuka take sosai kamar ranta zai fice, duk da ta ji dad'i da ya kasance ita d'in halastacciya y'a ce ba shegiya ba kamar yarda take tunani. Amma tunaninta ya fi karkata akan ta yaya zata ga mahaifinta, mutumin da a labarin da Ummanta take bata bata ji ta anbaci sunansa ba, sai kiransa da Buzu da ta ji ana yi, buzaye nawa ne a Habasha in dai haka ne? Didi da ranta ya gama dugunzuma da ta'ajibin labarin Sakna ta dinga dubanta tana jijjiga kai, ta kasa furta furucin bakinta, lamarin ba k'aramin girgizata ya yi ba, wacce irin soyayya ce ta rufewa Umar d'inta ido har haka? Da ya kasa bayyana mata ya tab'a sakin Sakna tsahon wannan lokacin. Ji take tamkar ta shak'o shi ta yi ta jibga, ta fi jin haushinsa fiye da Sakina da dama bata amince da tsarin tarbiyyarta ba, idan ban da haka ta ya za'a yi ace, kai zaka zab'a ma kanka abinda ka ke so ka haifa sai kace a lokacin jaliyya. Hammad ma ya shiga jerin mutanen da Didi take jin haushi sosai ta yaya zai b'oye wannan babban abu haka? Duk da dai da yarinta a lokacin amma me yasa da ya girma bai fito ya bayyana musu gaskiyar lamari ba, ai akwai hanyoyin da za'a gane tabbas Hamda ba y'arsa ba ce, ya ja bakinsa ya tsuke ya barsu suna bulayi cikin duhu.Fuskar Didi a had'e sosai ta zubawa Nanna da take ta kuka a wajen ido, duk da ta bi ta cika wajen da kwakwazon kukanta, cikin takaici Didi ta ce "Ke da halla yi mana shilu, mu ji da abinda ya damemu ke me ye ma na ki a ciki da za ki zauna ki b'are mana baki kina kuka? Wad'anda kuka ya kama ai bayan mu ne, da aka mayal y'an itka ba a damu da mu san komai a cikin gidan ba, kai Umalu ai te ka ja Takina ku yi gaba, a je a cigaba da Toyayya tunda Takina ta fiye maka ni Uwalka da na kawo ka duniya. Allah na gode maka da ka nuna min wannan lana tun kafin mutuwata. Ga dai Takina ga kuma tsiyal da ta shuka maka k'alshen Toyayya kenan, wanda na tabbata ba na haufi hak'kin Tadiya ne tun yanzu ubangiji ya fara mata takayya. Kai kuma Hammad ba abinda zan ce maka te Allah ubangiji ya yi maka abinda ka yi mana da ni da Uwalka, ka b'oye mana abinda ya kamata ace tun tuni mun tani ka bar mu muna ta yawon bin malamai muna a yi maka addu'a ashe kai lamalin da yake filgita ka kenan? Kai ka jiyo ka je kai da halinka."
Ta juya ta kalli Ammi da take ta kuka kamar ranta da zai fita, musamman ganin har a lokacin Umar bai ce komaiba, tun da ya d'ago kai ya kalleta da jajayen idanunsa sau d'aya, ba bu kuma abinda ta gani a cikin kallon sai tsantsar tsana da bata tab'a gani a cikin idanunsa ba, tsawon zamansu a matsayin ma'aurata.
Didi ta yi tsaki "Kuka ma ai yanzu ki ka fala shi Takina? Kin cuci yarinyar nan yanzu ina za'a gano wani Buzu mai gadi mutumin da ko cikakken tunanta ba wanda ya tani a gidannan da Buzu kawai ake kiranta, Garin Habasha da fad'i ta ina za'a fara lalubar wani gidan Uban maza ko ba Abu rijalun ki ka ce sunan mahaifin buzun ba? A Habasha wani gari? Wace jiha? Wace unguwa? Duk ba ki tani ba, kin cuci yalinyal nan, ki ka dinga gallazawa yalinyal nan akan laifin da ba nata ba, wallahi Allah te ya kama ki da laifinta, ko da ki ke uwa a wajenta ai ba 'a ce ki cuceta ba.Umal ka yi shilu ka balni ina ta magana ni kad'ai ban ji ka yanke hukunci ba?" Bai d'ago d'in ba, don ba ya jin zai iya musamman yarda k'irjinsa ya yi nauyi ga wani bugu da zuciyarsa ta keyi, idanunsa dishi-dishi suke gani, yana daga zaunen amma jiri yake ji. Sai gani suka yi ya zame ya kwanta idanunsa sun kakkafe gaba d'aya. Salati mutanen wajen suka saka musamman Gadanga, a rud'e shi da Hammad suka sungumeshi suka fita da shi. Zuwa lokacin Hamda ma ta saka wata iriyar k'ara sabida wani irin ciwon mara da ya turnuk'o mata, take a wajen jini ya b'alle mata. A rud'e Asma'u ta yi kanta tana kiran sunanta, amma ina tsananin azaba ya sa ta kasa motsi sai nuni da ta yi mata da jinin da yake zubo mata da sauri ta k'ark'ashinta. Umma Asma'u ta saka salati tana kallon Mahmah Sadiya ta ce "Taimaka min mana Sadiya ina ji fa b'ari ta yi." Sadiya fuska a cunkushe don dole ta kamata haka kawai ta tsinci kanta da rashin farin ciki da auren Hammad da Hamda. Suna fita Hammad yana k'ok'arin jan motar da zai kai Abbu asibiti shi da Gadanga, ya ga sun fito da ita da sauri ya tsaya yana tambayar lafiya?" Umma Asma ta ce "Je ka kawai, zamu taho da ita bleeding take ina jin ta samu miscarriage" Hammad ya runtse idonsa ya ja motar cikin rashin kuzari. Asma'u kuma ta shiga motar tana kallon Sadiya da take shirin juyawa ta shiga gida ta ce "Mahmah ya haka ne? Taimaka ki shigo mu kaita mana." Ta zubawa Asma'u ido kafin ta ce "Ko Abbun ban bi asibiti ba balle ita, ki kira uwarta ta kaita." Daga haka ta shige sashenta. Ta bar Asma'u sake da baki tana kallonta.
A sashenta ta samu Nanna tana ta wani irin kuka da take da tabbacin kukan takaicin Hammad ne yake nuk'urk'usar ta. Ta ja tsaki a fili ta ce "Nanna ki saurara min kada ki sake b'ata min rai, idan za ki kwantar da hankalinki ki kwantar, Hammad dai ni na haifeshi nake kuma iko da shi, don haka in dai Nono na ya sha ina tabbatar miki sai ya saki yarinyar nan, ba ta yarda za'a yi na bari ya zauna da y'ar Sakna bayan d'aukan tsawon lokaci da suka yi suna cutata ita da Umar, lokaci ya zo nima da zan rama Wallahi Hammad sai ya saki yarinyar nan, in dai kin ga sun cigaba da aure to tabbata bana duniyar nan..."
Nanna ta saki wata ajiyar zuciya kafin ta kumshe idonta, hawayen sauk'in zuciya yana ziraro mata, ta hango gaskiyar Mahmah ta cikin idaniyarta, alamar zancen da take har k'asan ranta. Ta saki murmushi na tarin farin ciki, ta yi alk'awarin Hammad na ta ne ita kad'ai har abada!
Jikar Nashe ce.✍🏽✍🏽
❤️❤️❤️❤️❤️🙏
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.