_~ALƘALAMIN JIKAR NASHE
YA ABIN YAKE ?
LIttafin Nazeefah Nashe.
08033748387
Follow me on ArewaBooks
@nazeefah
https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378eELEGANT ONLINE WRITERS
(Haɗin kai shine takenmu.)
_4*******************************
Da asubar fari, da tayi sallah bata
koma ba, tana zaune gefen Didi suka yi azkar kafin ta karanta abinda ya sawwaƙa daga Alƙur'ani mai girma. Bata koma barcin ba, kasancewar ta ɗan ji sauƙin jikinta gyara sashen Didin tayi tas. ta wanke toilets uku da suke sashen ɗaya a Parlour biyu a sauran bedroom ɗin da suke sashen Didin inda ta mayar da ɗayan bedroom ɗinnata duk da dai Didin bata yarda su raba ɗaki ba tare suke kwana. Tas gurin ya fito sai zabga ƙamshi yake farin ciki ya lulluɓe Didi yana daga dalilin da yasa take son Hamda, sam bata da ƙiwa ko kaɗan. Wanka Didi ta shiga tana faɗin kema sai ki shiga kiyi wanka ga sabbin kaya nan da na ɗinko miki don na san waccan gallafirin uwar taki ko kayan ubanku yayi muku ba bari take ki saka ba, ta gwammaci ta haɗaki da gwanjo ina nan Ina jiran ranar da zata zo tana neman gafarar ki, to ko cikin shegen Ki tayi ai iya ɗiban albarkar da zata yi kenan, balle laifinki ɗaya wai kinzo a mace, shikkenan tun ranar da aka haifeki ake gumurzu da ita bari muyi walaha mu karya na baki labarin da kika daɗe kina son ji na san yanzu shekarunki sun kai sha bakwai tsab kwanyarki zata ɗauki labarin takaicin uwarki mai hali kwatankwacin na jahiliyya, na tabbata ita da kanta banda an saka mata ido tsaf zata iya hallakaki a lokacin, kai mun ga tashin hankali Ƙiris fa ya rage ta zauce sabida masifa.Daga haka ta shige wanka wannan damar Hamda ta samu tayi saurin ficewa tana mamakin surutun Didin.
Sashen mahaifiyarta ta shiga, dama da spare key a hannunta ta buɗe a hankali, shiru ta tarar da parlourn da alama barci suke tabi gurin da kallo duk datti ɗan kwana biyun da tayi bata yi shara ba. Dama ita Ammi sam taƙi yarda ta ɗau mai aiki don tace gata bata buƙatar wata mai aiki. Ta ɗaure Hijabinta a ƙugunta ta shiga wanke kwanukan kitchen ɗin ta gyarashi tsaf burinta ta faranta mata ko ta samu ta goge tabon ƙiyayyarta a zuciyar Ammin.
Kan kace me? Ta gyare gidan tsaf banda ɗakunan barcinsu ta wanke har toilet ɗin parlourn sannan ta saka turarukan wuta a burner da humidifier tuni gidan ya ɗau wani irin Ƙamshi daga haka tayi sauri ta fice ta koma sashen Didi.
A saman sallaya ta tarar da Didin da alama sallahr walaha tayi, ita kanta Didin ita Ta koyar da ita sallahr walahar, tana sake jaddada mata ɗimbun ladan da yake cikin Sallahr walahan da tarin nutsuwa da mai yinta yake samu a zuciyarsa, ga shi Allah yana amsa addu'arsa ba da jinkiri ba.
Wankan itama ta shiga ta yiyo sannan ta ɗauro alwalarta ta saka tsaleliyer atamfarta da Didin ta ɗinko mata kaya ne kala goma dama ta saba duk sanda zata zo sai tayi mata don ta san kafin tazo nata sun mutu tunda ba wata sutturar arziki uwar take barinta ta saka ba.
Idan ka shigo gidan ma zata zaka yi ƴar aiki ce, Saboda tsabar yarda zaka ga kayan sun ƙojale don tsufa ga kanta da baya samun cikakken gyata fatarta ma don dai Allah yayi ta cikin jinsin mutane masu taushin fata ne, da duk wahala bata jemewa tabbas da ba ta kai haka kyauba.Tayi kyau sosai ɗinkin kuma ya zauna a jikinta tamkar ba daga ƙauye aka ɗinko mata su ba. Ta cukuikuye gashinta ta danna cikin ɗankwali don rabon da ta tajeshi har ta manta balle ta saka man kitso, ko wanke shi tayi haka take barinsa.
A gefen Didi da take lazimi da jug ɗin furarta a gefe ita ma ta tada sallahrta cikin nutsuwa. Sai da ta idar tayi addu'ointa Didin Ta tura mata cup cike da fura tace "Maza kwankwaɗeshi tas ki bani cup don na san waɗannan mashiriritan kafin su kawo abin karyawa sai goma ta gifta shi yasa wannan karan zan saka ya kawo min kayan abincina kaf da kaina zan dinga girki ba zan iya zaman jira ba, girkin da sai an ga dama sannan ake yin mai daɗi ko a zabga mai da maggi to bana ba dani ba kowa ta riƙe banzan abincinta."
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.