ALK'ALAMIN JIKAR NASHE
YA ABIN YAKE?
BONUS PAGE 17
08033748387
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
Ajiyar zuciya kawai Hamda take saki, jin zantukan Nanna da suka zo mata a bazata, sam bata tsammaci haka daga bakinta ba, Lura da cewa ta nuna wa yaranta k'auna, amma a yau ta wanke idonta tana furta muggan kalamai a kanta tamkar ma bata tab'a saninta ba, kawai don k'addara ta hau mata. Me yasa ba za su yi mata uzuriba? Dubi da cewa itama ba laifinta bane da bisa son ranta ne da bata amince ta zo duniya ta wannan k'azantacciyar hanyar ba. Ta sake rintse idonta gam jin cece kuce yana sake yawaita tsakanin Nanna da mai gidanta. "Wallahi Mahmah ki yi masa magana muddin ya ce sai ya tafi da ita to tabbas sai dai ya san yarda zai yi da ita ba zata zauna min a gida ba."
Fuskarsa a tamke ya dubeta had'e da furucin "San da na siyi gidan ko aurenki ban yi ba, balle ki ce da kud'inki na siya, idan kin san tashin hankali za ki koma min da shi you better stay at your father's house." Zata sake magana cike da zafin rai Dida ta daka mata tsawa "Nanna bana son rashin hankali ki bari a yi komai a nutse. Duk wannan maganar ba ta da amfani." Kuka ta sake fashewa da shi "To ku gaya masa kada ya tafi da yarinyar nan, wallahi zan iya aikata komai idan na ce komai ina nufin komai." Cikin b'acin rai ya mik'e zai fice har ya kai k'ofa ya ji Mahmah ta daka masa tsawa. Tsak ya tsaya had'e da juyowa yana facing d'inta. "Me kake nufi da tafiya da ita? Ko kana nufin da gaske ka karb'eta a matsayin y'ar cikin ka, Hammad kada kace min da gaske yarinyar nan jininka ce?" Ya d'ago kai yana kallonta cikin tafasar zuciya sai dai lab'bansa sun gaza furta furucin komai illa idanunsa da suka jirkita launi zuwa ja. Ya sunkuyar da kansa kawai. Har zuwa san da Dida ya fuskanci tabbas ba zaida ce komai d'in ba, ta dafa kafad'ar Sadiya cikin taushin murya ta ce "Yaya mu bi komai a hankali, insha Allah komai zai bayyana kansa, a yanzu na fuskanci halin da Hammad yake ciki sam ba zai iya furta komai ba." Sadiya ta bud'e baki zata yi magana Dida ta yi saurin girgiza mata kai, don ta lura idan har aka cigaba da kucincina maganar tsaf Hammad zai iya datse igiyar auren y'arta, ko ba haka ba ita Hamdan ce ma ta bata tausayi, ta lura ba a k'aramin rud'ani da firgici take ciki ba, kada a je ta rasa hankalinta ko zuciyarta ta buga haka kawai an saka ta a halin ban ji ba ban gani ba. Idan har Hammad ya matsa sai ya tafi da ita, ita zata rik'e ta madadin a had'a ta da Nanna a zo a haifi d'an da ba shi da ido. Don haka ta girgizawa Sadiya kai alamar kada ta ce komai, ta kuma k'arasa gaban gadon murya a tausashe ta dafa kan Hamda da ya d'au zafi rad'au ta ce "Ki yi hak'uri kin ji, komai zai daidaita ubangiji Allah ya ba ki dangana, duk abinda kika ga ya faru ga bawa muk'addari ne daga Allah kuma bawa ba zai iya goge k'addararsa da Ubangiji yada rubuta masa ba, ki yi ta addu'a a zuciyarki ubangiji Allah ya baki ikon amsa jarabawarki Allahumma la sahla illa ma ja'altuhu sahlan wa anta taj'alal Hazna iza shi'ita sahlan. Tana yaye duk wata damuwa da nauyi zuk'ata." Daga haka ta yi mata sallama suka fice. Hamda ta bi bayanta da kallo, tana jinjina kyakykyawan hali irin nawannan mahaifiyar Nanna, tunda abin ya faru ita kad'ai ce ta fad'a mata abinda ya kwantar mata da hankali kad'an, ita ce matar da ta lallasheta da furuci mai warware fushin zuk'ata, wani abu kad'an daga cikin abinda yaaka tokare k'irjinta ya sauka, a hankali wasu siraran hawaye suka fara biyo k'uncinta. Ta shiga nanata waccan addu'ar da Dida ta gaya mata. Sai ga shi a hankali barci duk da ba za'a kira shi mai dad'i ba yazo ya d'auketa. Tana sakin ajiyar zuciya akai-akai. Hammad da yake zaune ya zuba mata ido, wani abu mai kama da tausayi yana tsirga masa cikin zuciyarsa, da gaske yana jin tausayinta, idan kuma ya tuna ta hanyar da aka sameta sai ya ji zai iya sadaukar da Duk wani farin cikinsa matuk'ar ita za ta yi farin ciki.Kusan awoyi biyu yana zaune kamar maigadinta yana kallon yarda take sauke ajiyar zuciya cikin barci. Ba ya son ya tasheta duk da kuwa za suje wajen passport, ya fi so ta tashi da kanta. Sai da ta k'ara mintuna talatin akan awa biyun sannan ta farka. Idanunta cikin nasa da ya kafeta da su, da sauri ta d'auke na ta idanun tana tattare gashin kanta da ya kwanto a
Saman fuskarta. Da kyar ta mik'e zaune tana dafe pillow, tana mamakin yarda ta yi barci sosai haka. Fuskarsa a d'an d'aure ya mik'e yana gyara wristwatch da yake hannunsa "10 minutes na ba ki, ki yi alwala ki yi sallah za mu je wajen passport kuma kada ki yi taking time sauri nake." Bai saurari amsarta ba ya fice da sauri. Sai da ta fi minti d'aya a zaune kafin ta mik'e cike da kasala ta shige toilet d'in d'akin. Ita dai da zai bi ta tata da ya kyaleta ta shiga duniya tunda zamanta tare da su a gareta ba shi da wani amfani, musamman da matarsa ta nuna mata k'iri-k'iri bata son zamanta tare da su. Sam ba taga laifinta ba, dama y'ay'a irinsu haka mutane ke gudunsu ba sa son sam su rab'e su, duk da kasancewar ba laifinsu ba ne.
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.