20

555 15 17
                                    

YA ABIN YAKE?

LAST FREE PAGE INSHA ALLAH

Normal group 300

Vip 500

Special people 1000 sending privately.

Payment via 2118666253 U B A

Sai a tura shaidar biya ta (08033748387. Ga wanda suka biya akwai kyautar free book d'ina Na Zumuncin Zamani.)

_____________________

Kallonsa kawai take tana mamakin furucinsa, shin da gaske auren zai yi mata, me yasa ya taho da ita k'asar da bata san kowa ba alhali ya san matarsa ba zata iya rik'eta ba? Aure dama an tab'a aure haka ba tare da matar ta san mijin ba, ko kuwa don k'addara ta hau kanta sai a samu koma waye a lik'a mata shi a matsayin miji? Shikkenan ita bata da damar soyayya kenan? Ta ina mijin zai ga k'imarta da mutuncinta. Hannu tasa ta share hawayen da ya kwaranyo kan fuskarta da gaske lamarin ya yi mata zafi k'warai da gaske. Shikkenan duk mafarkinta na tsalelen mijin da take so ta aura ya bi iska, ko zunnuraini da ta amince zata aureshi ne kawai ba don ya zama irin mijin da take so ba. Irin mijin da take so sirri ne a zuciyarta da kuma tunaninsa take kwana a koda yaushe.

A fili ya ja tsaki "Idan ba kya son auren ba sai ki fad'a ba me ye na zama kina min kuka. Kin san da yaya ya amince zai aureki ma tukun?" Ya fad'a daidai yana parking a k'ofar gidansa "Aurenki shine abinda yafi alheri a yanzu a rayuwarki, ko bakomai za kiyi karatunki cikin nutsuwa, don haka ki share wannan hawayen idan kin amince gobe zai zo ku ga juna zai kuma kawo miki sadakinki da duk wani abu da za ki buk'ata, Nan da kwana biyar za muje masallaci da su a d'aura miki aure ki tare a gidan sa." Tana shashshek'a ta share hawayenta had'e da d'aga kanta cikin wata irin murya ta ce "Shikkenan bakomai Allah yasa haka ne yafi alheri a gareni" idanunsa cikin nata ya ce "Haka ne ma insha Allah, kina da suffa da halayen da za ki saka namiji ya so ki ko bai shirya ba, don haka ki k'addara za ki zama star a zuciyar abokina." Yatsun hannunta kawai take wasa da shi kafin ya mik'a mata jakarta ya ce "Mu je gida." Ta fita daga motar jikinta a salub'e haka kawai kuma gabanta yake dukan Tara-tara. Tana mamakin yarda lamarin auren nata ya zo kamar auren y'ar tsana.

A parlour Nanna take zaune cikin hamshak'iyar shiga, fuskarta sam ba walwala take jifansa da wani kallo ganin yarda suka shigo gidan. Ba tare da ya kalleta ba ya zauna yana d'iban lemon tataccen inibin da yake gabanta a jug. Ta d'ago tana kallonsa kafin ta ce "Ban da dai yarinyar nan y'arka ce da sai nace ko soyayya ku ke?" Fuskarsa a had'e ya d'ago tare da zuba mata wani matsiyacin kallo, sai kuma ya girgiza kai kawai ya cigaba da kurb'ar juice d'insa "Ka kalleni ka yi shiru, na lura kular da kake bawa yarinyar nan ta na nema ta wuce muhallinta don ko ni matarka ban samu kwatankwacin kular ba, kada dai bayan an gama da uwa a zo a koma bibiyar y'a." Ji ta yi kawai ya yi cilli da Glass tumbler d'in hannunsa cikin matsanancin b'acin rai ya dubeta "Na rantse da Allah idan kika sake min kwatankwacin wannan furucin I will show You who I am. Wani irin iskanci ne wannan kawai don na zuba miki ido kina duk abinda kika ga dama doesn't meant kin fi k'arfina ne." Daga haka ya fice daga gidan zuciyarsa a tunzire har hakan ya d'an firgitar da Nannan ta tabbatar yau ta kaishi mak'ura amma zuciyar shaid'an na sake tunzirata. Ta mik'e da sauri ta nufi d'akinsa inda Hamda take.

Tana zaune a gefen gadon hannayenta zube a k'uncinta, gaba d'aya zuciyarta ta ruga tunani. Mamakin yarda rayuwa ta yi mata juyin waina take. Turo k'ofar da aka yi da k'arfi ne ya sata saurin d'aga kai, idanunta suka sauka cikin Na Nanna da take tsaye tana huci tamkar zakanyar da ta kwana da yunwa "Ki tattaro duk wani kayanki ki koma d'akin yara, duk da babu space ki dinga bajewa a k'asa, haba yarinya kin shigo rayuwata kin zame min bala'i ina zaman lafiya da mijina yanzu abu ya gagara shegiya kawai, na tabbatar uwarki ce ta yiwa mijina fyad'e saboda jarabarta ta son haihuwa d'a namiji amma aka tattare laifin duk aka jibge masa." Ganin Hamda ba ta ce komai ya sa ta cigaba da zabga mata masifa "Kuma last warning da zan miki ba ke ba shirgin yara ne ki tsaya a matsayinki na shegiya su ma su tsaya a matsayinsu na y'ay'an Sunna da aka haifa da aure. Sai na bi na sanar da kowa matsayinki wallahi idan ba ki bar gidan nan ba, sai na goga miki bak'in fentin da zaki kasa auruwa ki fito yanzun nan na gaya miki." Daga haka ta fice daga d'akin ta bar Hamda tana wani irin kuka tabbas Yaya Hammad ya yi gaskiya da ya ce aurenta shine abu mafi alheri a gareta. Ta lura idan har zata cigaba da zama a gidan nan Nanna sai ta saka mata ciwon zuciya da bak'ak'en kalamanta. Ta rasa me ta yi mata da har ta tsaneta haka? Duk abinda ya faru itama fa ba laifinta bane.

Ya Abin Yake?Where stories live. Discover now