32

310 4 0
                                    

"Ka gafarce ni Umar, ha'k'ik'a na san na cuceka bisa son zuciya da sharrin shaid'an, sai dai hakan ya faru ne saboda d'amfaruwa da zuciya ta tayi na son haihuwar d'a namiji. Amma ina tabbatar muku Hamda d'iyar halak ce da aure na samu cikinta ba kamar yarda zuciyarku take hasashe ba."

A tunzire Didi ta zuba mata ido cikin b'acin rai ta ce "Takina bana ton itkancin banza da wofi ta yaya zaki ce da aule kika haifi Hamda an tab'a aule akan aule ne? Ko a garinku haka ake ni dai ina gidan nan ban ji san da Ummalu ya take ki ba. Don haka ki tanal da mu yarda kika tamu cikin tegiyar y'alki"

Shiru Sakina ta yi zuciyarta na dakan uku-uku ta kasa cewa komai illa murza wani zobe da yake hannunta. Razani da firgici ne a cikin ranta shi yasa ta kasa d'aga kai ta kalli kowa. Musamman yarda take jin sautin kukan Abbu har nan inda take zaune. Alamar lamarin ya gama gigita tunaninsa. Tunda zata iya k'irga sau nawa ta ga hawayensa amma bata tab'a ganin yana kuka da shashshek'a ba. Hakan ya sake d'aga hankalinta yanzu ma kenan ina ga ya ji gaskiyar abinda ya wakana.

Asma'u a harzuk'e ta kalli Hammad cikin tsawa ta ce masa "Kai don ubanka tunda ta k'i fad'ar abinda ya wakana kai tunda ka san komai sai ka sanar mana." Hammad ya hau girgiza kai yana tuno da ranar da zai iya kiranta bak'ar rana a tarihin rayuwarsa, a duk sanda ya tuna kuma sai ya zubda hawaye yake jin sanyi a ransa. Yanzunma hawayen ya share yana sakin murmushi kad'an ya ce "Ita zata fad'a muku da bakinta Umma, a tun lokacin da abin ya faru na tabbatar musu da ba zan fad'awa kowa ba alk'awari na d'auka bayan sun tursasani bisa son zuciyarsu, ta hanyar d'aukan hotona tsirara shimfid'e akan gadonta, da camera suka kuma wanko hotunan suka nuna min tare da tabbatar min idan maganar ta fito to wallahi za su alak'anta ni da cewa ni ne naje har d'aki na yi mata fyad'e. A lokacin hankalina ya tashi har aka dinga kaini asibiti kuna tunanin motsuwar k'wak'walwa ya sameni, da gaske ni kaina a lokacin gani nake kamar na haukace bani da nutsuwa ko kad'an. Shi yasa na uzzira sai da aka kaini Birmingham karatu saboda da zarar na rufe ido lamarin nake gani da kuma hotunana tsirara. Na san bani da mafita kuma ko na fito na fad'a alokacin suna nuna hoton nan ba wanda ba zai amince da cewa ni na haik'e mata ba. Shi yasa na bar maganar a ciki na har ta kusa zautar da ni banda Allah ya kiyaye Mahmah ta fahimci kamar sammu aka yi min ita da Didi suka dage min da addu'a. Na d'an samu sauk'in zuciya, ina kuwa barin k'asar na ji Nigeriar ma ta fice min daga rai baki d'aya. Amma na rik'e a zuciyata zan dawo d'aukan fansa ta hanyar aurar yarinyar na san idan na yi haka ne kawai zaku fahimci akwai lauje cikin nad'i, tunda kowa zai buk'aci jin me yasa na auri k'anwata da muke uba d'aya. Shi yasa ko da wancan karan ta jingina laifin a kaina zatonta ni na fad'a muku ban fito na kare kaina ba, duk da Abbu bai bani damar haka ba, na k'udirce zan b'ullo mata ta hanyar da bata yi tsammani ba. Wannan dalilin ne yasa na auri Hamda, kuma ina tabbatar muku aurena da Hamda halastaccen aure ne."

Yana kaiwa nan ya ja baki ya yi shiru, majority na mutanen da suke wajen sai da suka saki ajiyar zuciya jin cewa Hammad ba shi da alak'a da waccan kwamacalar da ake danganta shi da ita na kusantar matar ubansa. Didi a zahiri take "Alhamdulillah, na tabbata dama zuli'al Utmanu ba zata yi lalacewal haka ba insha Allahu, Takina yanzu ke muke jila ki fad'a mana uban cikin y'al ki. Kada ki mayal da mu shashashai ki ce wani da aule kika haifeta ba ta yarda aka tab'a aule akan aule don haka muna jin Ki ko ki magantu ko na saka Umalu ya take ki yanzunnan."

Sakina ta mayar da kanta kan Umaru har a lokacin still kansa a k'asa yake shi kad'ai ya san masifar da take ruruwa a ransa, tunanin cin amanar da Sakina ta yi masa yake duk da tarin k'aunar da yake mata ashe sai da ta bawa wani kanta bisa kawai dalilin son haifar d'a namiji. Tabbas ji yake zuciyarsa kamar ta daina aiki.

Ta mayar da kallonta kan Gadanga da shima fuskarsa ta nuna tana d'auke da matsanancin tashin hankali, musamman ganin yarda jijiyoyin kansa suka tashi rud'u-rud'u. Yana ta murza kan nasa da alama ya yi zurfi cikin tunanin da yake.

Ya Abin Yake?Where stories live. Discover now