41

313 4 0
                                    

Dariya sosai Didi ta bawa Asma'u, ita dai ta yi farin ciki da Didin ta amince da Zaman Hamdan a wajenta, ba ruwanta da abinda za ta yiwa Hammad wannan tsakaninsu ne su gyarota a can. Lauratu kuwa haushi abin ya bata, sam bata so Yayarta tata ta jajib'o musu Hamdan ba, ta so a barta a hannun uwarta ta ga yarda zata yi da ita sai dai bata furta ba ta ja baki ta tsuke ganin sam Asma'un ba wasa a fuskarta.

***********

Sadiya ce zaune a gefensa yana kwance a d'akinsa fuskarsa na bayyanar da damuwa b'aro-b'aro, so yake Yace Sadiyan ta matsa masa k'afa tunda ya tabbatar da Sakna tana nan da ba sai ya rok'a ba ma da kanta zata ja shi jikinta ta dinga matsa masa k'afar tana kuma lallab'ashi har sai ya yi barci, amma ji yarda Sadiya ta saka shi a gaba kawai da kallo fuska ko alamar murmushi babu balle ya hango tausayawa a cikinta, don haka yake ganin da kyar idan zai karb'i shawarar da zuciyarsa take ba shi na rabuwa da Sakna, duk da dai ya san ta yi laifin da dole ya bata saki ko d'aya ne. Ba ya azimi amma Sadiya bata damu da tambayarsa me yake son ci ba, da Sakna ce kuwa sai ta jere masa abinci kala-kala wanda ta San Zai ji dad'in cin su a matsayinsa na mara lafiya.
Ya saki nauyayyiyar ajiyar zuciya idanunsa cikin na Sadiya ya ce "Taimaka a samo min abinci kuma jikina na d'an ciwo ina buk'atar a matsa min." Ba tayi musu ba ta mik'e dama ita haka take dole sai ya ce ta yi masa abu take yi ba ta san ta yarda zata kula da shi ba, shi kuwa mutum da duk da shekaransu har a yanzu yana son soyayya yana son kuma tarairaya daga wajen matarsa. Ya lunshe ido yana sakin tsaki kad'an zuciyarsa na tunano masa Sakna da halin da take ciki, ya tabbbata duk a inda take tana cikin damuwa.

*****
A d'akinta ta tsantsara had'ad'diyar kwalliya, sai baza k'amshin had'addun turarukan humra take da wanda ta turara jikinta da shi. Buk'atar shiri take da Umar ta kowane hali, ta kashe d'auri sosai irin d'aurin da ta san Umar ya fi so sannan ta jefa k'amsassan chewingum a bakinta, ita da kanta ta san lafiyayyen d'inkin ya zauna a jikinta. Tana gamawa ta d'auki tray d'in peppe soup d'in da ta yi masa na kifi ragon ruwa da ya sha kayan k'amshi. Sai kunun mard'am da ta yi masa.

Daidai lokacin shan ruwa ne ta san ba wanda zata gani a sashen nasa, don haka hankalinta kwance ta murd'a k'ofar tangamemen falon nasa. Shiru falon alamar yana cikin d'aki.

Da siririyar muryarta ta yi sallama kafin ta shiga cikin d'akin, kamar yarda ta yi hasashe kuwa shi kad'ai ne zaune a tsakiyar gado ya yi jigum da alama ya zurfafa a cikin tunanin da yake. K'amshin turarenta shi ya ankarar da shi wanzuwarta a cikin d'akin, da sauri ya d'ago ya sauke idanunsa a kanta. Wani sanyi ne ya ziyarci zuciyarsa sai dai bai bayyyana hakan a saman fuskarsa ba, madadin haka ma had'e fuskar ya yi ya d'auke kansa daga kallonta. Ta saki d'an guntun murmushi had'e da isa gefen side bed drawer ta d'ora abincin, tana zama daf da shi. Bai yi auneba ya ji hannayensa cikin nata taushi da santsin hannunta yana ratsa shi, murza hannun take a hankali cikin kwarewa tana sake luguiguta shi, duk da k'ok'arin k'wacewa da yake ta hanashi damar hakan. Sai ganinta ya yi zube a k'asa ta d'ora kanta bisa cinyarsa cikin wata iriyar salon murya ta fara bashi hak'uri "Ka yi hak'uri sweetheart na san ni mai tarin laifi ce a gareka don girman Allah kada ka yarda a raba mu, tunda dai ba zina na yi ba ko mai ma na aikata da aurena na aikata shi please don Allah ka yafe min wallahi zuciyata ta kasa sukuni sharrin shaid'an ne." Ta sake sakin wani irin kuka da yake jinsa har tsakiyar zuciyarsa, ji ya yi kaso hamsin cikin d'ari na b'acin ran da ta sabbaba masa yana zagwanye so yake ya kamota ya sanyata a k'irjinsa amma wata zuciyar tana hana shi, ita da kanta ta yiwa kanta masauki a jikinsa tana ba shi wani irin zazzafan kiss a k'uncinsa murya a dashe cikin kunnensa take sake rad'a masa please ka yafe min ka san kai ne rayuwata wallahi ba zan iya rabuwa da kai ba, son haihuwar d'a namiji ita ta jawo min gurb'acewar tunani. Luf ya yi a jikinta cikin wani irin yanayi na kissa da bata tab'a yin amfani da shi ba ta saukar masa da b'acin ransa. Daidai lokacin da Sadiya ta turo k'ofar ta shigo idanunta ya yi kyakykyawan gani, da sauri ta saki tray d'in da yake hannnuta hakan ya jawo Sakna ta janye bakinta daga cikin na Abbu idanunta cikin na Sadiya da take tsaye ranta a matuk'ar b'ace. Sakna ta yi murmushi tana cewa "Ki yi hak'uri don Allah." Daga haka ta saka kai ta fice.
Sadiya cikin tsananin b'acin rai ta juya zata tafi sai ji ta yi Abbu ya kirata "Zo nan SADIYA." Ya fad'a cikin wata iriyar murya da ta tabbatar tsananin matakin sha'awa da yake kaine ya sanya muryar ta shi jirkicewa ta sauya launi. Tsananin kishi ya sa ta ji kamar ta zunduma uban ihu, da kyar ta had'iye abin da ya tokare mata a k'irji ta ce "Ba sai na zo ba, da na san ma ka samu lafiya har kana iya kusantar mace da ban dawo ba." Ya lumshe idanunsa yana jin takaicin Sadiya a ransa sam bata iya kula da miji ba. "Ta yarda y'ar uwarki ta fiki kenan, me yasa ba zaki yi koyi da ita ba? Laifi ta yi min ta zo bani hak'uri ta hanyar da ta san duk girman laifinta Zan hak'ura na yafe mata. Tana kula da ni fiye da ke ta san soyayya kuma kullum a cikin nunan kulawa take fisabiliallahi ta yaya kike zaton Zan iya rabuwa da ita? Alhali ko da yaushe akwai salon kulawa da take sabuntawa ta ba ni, ko zuciyar k'arfe ce da ni ba dole ta narkar da ita ba, Zan gaya miki gaskiya ki canja halayyarki, ki na min biyayya sau da k'afa ta nan kam kin fi Sakna amma zan gaya miki gaskiya Sakna ta fiki sanin sirrin shimfid'a ta san ta yarda zata kautar min da duk wata sha'awar y'a mace, don haka zuciyata take kasa rabuwa da ita.... Yanzu tunda ki ka saka k'afa kika fice ba ki sake dawowa ba sai yanzu kuma tun safe kayan nan suke jikin ki haka ki kaga ita Saknan tana yi? Da an yi magana ace asiri.."
Cikin takaici take kallonsa wasu hawaye suna zubo mata, ya dad'e yana fad'a mata kuskurenta amma na yau yafi tsaya mata, ita kunya ce take mata dabaibayi ta hanata aikata wasu abubuwan, magungunan gyaran jiki kuwa gani take asarar kud'i ne siyansu, ita sam ba zata iya wannan zubin dashin da ba biya ba, akan me ma girma ya riga ya kamasu. Bata san shi Abbu ba ruwansa da girma ba, kullum jinsa yake kar in dai akan wannan harkar ce. (Don haka wallahi mata a dage da gyara, a kuma dage da sanin sirrin kwanciya, domin sune maganin mallakar miji sadidan ki dinga juya abinki son ranki sai ki ji ana ai wance asiri ta yiwa mijinta ga shi nan ta mallakeshi. Mhmn ba su san abin ba anan take ba, shi namiji yana son a kula masa da b'angaren shinfid'a ga dai Sadiya nan ta mayar da kanta borar k'arfi da yaji a wajen miji, Allah yasa mu dace.)
Muryarta na rawa ta ce "Yanzu duk girman laifin da ta yi maka ka yafe mata kenan?" Ya girgiza kai cike da takaicinta ga maganar da ake mata ita kuma ga zancen da take masa "Ban ce miki na yafe mata ba, amma kaso mafi yawa daga haushinta da nake ji ya zagwanye. Hukunci kuma ina nan ina tunanin hukuncin da ta dace da shi. Zo ki zuba min abinci yunwa nake ji." Ta bi abincin da Saknan ta kawo da tsaki kafin ta janyo nata abincin ta fara k'okarin zuba masa, duk da yana son cin abincin Saknan haka ya hak'ura ya dinga cin na Sadiya wanda sam bai zama daga cikin irin cimar da yake so ba. Har yanzu ta kasa gane kalar abincin da ya fi so, tsawon shekarun da suka d'auka tare sab'anin Sakna da haddace tsaf a kanta, ta san cimar da yafi ci da safe, ta san ta rana hakanan ta dare. Kad'an ya ci abincin ya ce ya isheshi. Jira yake ya ga ko zata yi hankalin had'a masa ruwan wanka, sai ya ga ta yi zamanta kamar ma a k'agare take ta tafi, ya kau da b'acin ransa had'e da cewa "Diyayye saura ruwan wanka." Ta d'an kalleshi kawai had'e da cewa "Yau kuma wani sabon salon suna ne ya tashi menene kuma wani Diyayye kamar wata yarinya?" Dariya ya yi kawai ya lura har abada Sadiya ba zata canja hali ba, madadin ta d'an rungumoshi ta ce masa "Umaruru, nima na rama, kamar yarda Sakna take masa idan ya kirata da Saknene. A zuciyarsa ya ce MATA SUNA SUKA TARA.. ruwan kawai ta had'a masa ta fito had'e da ce masa na kai." Ta kamashi ta raka toilet d'in, tana k'okarin ficewa ya janyota "Ba zaki taya ni ba? Na ga kema ko wankan b kiyi ba tun na safe ne ko?" B'ata fuska ta yi had'e da cewa "Wankan zan je in yi." Ya k'ura mata ido "To mu yi tare mana." Ta yi saurin kallonsa kafin ta ce "Allah ya sawwake sai kace wata yarinya." "Sakna yarinyace kenan da muke yi tare?" Haka ya so yace mata sai dai ya gintse ta hanyar tab'e bakinsa ya kuma sakar mata hannu, a zuciyarsa ya raya ba ta yarda za'a yi ya rabu da Sakna alhali ita Sadiya bata waye ba, da an tashi zance kuma ace baya adalci a tsakaninsu ta ina kuwa zai yi adalci? Ya tabbata da Sakna ce tsaf zata wankeshi kamar yarda ake wanke yara har ma ta shafe shi da mai ba wani kunya, to dama ai ba kunya tsakanin mace da mijinta. Haka ya dinga wankan zuciyarsa fal da tunanin Sakna da Sadiya da suka zama masu mabanbantan halaye. Sakna irin matar nan ce da Hausawa kai tsaye suke kira karuwar gida yayin da Sadiya ta zama irin matan nan masu duhun kai da basu san komai ba a harkar auratayya.

_____________

Sanin cewa tana b'angaren Didi yasa kansa tsaye ya nufi sashen, jikinsa sanye da doguwar rigar jallabiya coffee colour da ta saje da fatar jikinsa. Fuskarsa tas da alama bai dad'e da fitowa daga wanka ba, hannunsa rik'e da carbi na dannawa yana matsawa a hankali. Sai zabga k'amshin turaren Miyaki d'an asalin yake.

Daga Didi sai Asma'u a falon suna baje tana shafawa Didin man zafi a k'afa. Suka tsinkayi muryarsa ya shigo. Baki sake Didi take kallonsa ya zauna a gefenta had'e da gaisar da Umma Asman, sannan ya juya yana kallon Didin da  ta yi kicin-kicin da fuska, "Tsohuwa mai lan k'alfe an sha luwa lafiya?" Harara ta watso masa jin yarda yake kwaikwayan maganarta. Cike da shak'iyanci. Ta yi k'wafa a ranta ta ce "Zaka ci ubanka ne zan lama, ba dai matalka tana nan ba." A fili kuwa cewa ta yi "Umalu dai ya haifo mana jalaba, ko da yake duk wani iya shegen da ya yi kwatankwacinsa ka ke yi, ga shi nan kai ma baka damu da b'acin lansa ba, kamal yalda bai damu da nawa ba, ka je ka yi aule bai tani ba, tannan ka b'oye ma ta abu mai mahimmanci. Ai idan bai yi wata ba te ka taka mata hawan jini." Daga haka ta mik'e d'akin Hamda ta je ta kulle ta zare mukullin ta tura cikin bujenta "Ban ga dalilin biyo ta nan ba, tunda uwalka ta ce bata ton aulen to wallahi ba zan bali ka tumulmusheta ba, ni ce nan gatanta wallahi, kaje ka shilyota da uwalka idan ta amince da aulen falillahi hamdihi a had'o lefe a zo ayi biki kowa ya shaida tannan a kai mata ita gidanka ka je ka tumulmusheta a can jalababbe kawai." Sunkuyar da kai ya yi yana murmushi kunyar Umma Amsa ya hana shi k'watar key d'in ta k'arfin tsiya don da gaske a matse yake da son jin d'umin Hamdan a jikinsa ko da ba za su aikata komai ba. Ya mik'e ya fice kawai yana tuna wunin yau sir bai ganta ba bai san a wani hali take ba, ga shi ba waya a hannunta ya zama dole ya siyo mata waya ko muryarta ya dinga ji.

Direct b'angarensa ya nufa dole ya je ya nemi sulhu da Nanna tunda Didi ta rufe masa waccan k'ofar. Tana zaune a d'akinta ya shiga ta d'ago tana mamakin ganinsa a d'akin kafin ta tab'e baki ta ce "Lafiya?" Ya k'arasa wajenta ya zauna daf da ita yana shiga jikinta sosai. Da sauri ta mik'e dama wannan damar take jira, ya d'ago yana kallonta "Me ye haka Nanna?" "Kai zan tambaya meye haka? Ina matar taka da zaka zo jikina ai gwara kaje can ta baka abinda ni bana baka da yasa ka aureta." Fuska a had'e ya ce "Na san da itan ai na zo nan." Ta yi wata iriyar shewa kafin ta ce "Amma kuwa Hammad ka sha haushi don ina tabbatar maka wannan jikin nawa k'walelenka matuk'ar zaka dinga had'a jiki da waccan sannan ka zo ka had'a da ni, idan zaka yi gaggawar sakinta ka saketa kafin zuciya ta ta tunzira na sanar da Mahmah sirrin da kake b'oye mata game da Kamla..." zancen da ya shiga kunnen Sadiya kenan kasancewar ta shigo neman Hammad tana ta k'wala kira ba su ji ba, tana sa kai zata fita ta jiyo kamar fad'a suke ai kuwa ta tsinci wannan maganar, gabanta yana fad'uwa ta zaro ido ta ce "Kamla kuma innalillahi wa inna ilaihirrajiuna mai kunnuwana suke shirin ji?"

Jikar Nashe✍🏽✍🏽📖

❤️❤️❤️❤️❤️🙏

Ya Abin Yake?Where stories live. Discover now