30

348 5 0
                                    

Cizar baki tayi bak'in ciki ya turnik'eta jin k'ofar a kulle take gam da alama sai da ta murza key d'in sau biyu. K'arar bugun k'ofar ne ya farkar da Hammad da guntun barcin da ya fara surarsa. Da sauri ya mik'e yana isa corridor d'in mamaki fal fuskarsa da yaga Nanna ce a tsaye tana aukin buga k'ofar da alama ma kamar bata cikin hayyacinta "Wai Nanna meye haka ne? Kin san kuwa k'arfe nawa yanzu ki ke aikin buga k'ofa. Idan ta bud'e me zata miki me yasa ba kya son zaman lafiya ne?" Jijjaga jiki take tana masa kallon sama da k'asa "Eeh mana, ka ce haka ni kuwa na san k'arfe nawa. Uku har da Rabi na dare ko ba haka bane? Kuma ina sane nake buga k'ofar so nake ta fito ta sanar da bi uban me ku ke aikatawa a b'oye? Don haka siddan ba zata dinga wannan karairayar jikin ba, da duk wanda ya gani ya san da wata manufa take aikataw so take ta ja hankalinta kanka ko ma ka riga ka kai kanka wajenta idan ban da haka ta yaya da aurenta zata dinga maka d'abi'ar karuwai. Ko da yake uwarta ma da auren ubanka a kanta ka nemeta har ka yi cikinta...." Wasu taurari da ta gani shi yasa ta shanye maganar ta tsaf a mak'ogaro mari fa? Sosai ta dinga shafa wajen tana jifansa da kallon mamaki yaushe rabon da ya mareta tun farkon aurensu lokacin yana kan ganiyar cutar da bata tantama hauka ya yi a lokacin. Sai ga shi yanzu a cikin hayyacinsa ya sake marinta. Idanunta a jirkice ta d'ago tana kallonsa "Ni ka mara?" "Na mareki d'in, kuma ko yanzu kika sake alak'anta ni da waccan maganar zan sake zuba miki mari. Tunda ke ba ki san kara da kawaici ba. Sau nawa na ja kunnenki akan maganar amma kin yi burus da jan kunne na kullum sai sake maimaita min zance mafi muni a kunnuwa ki ke." Da kyar ta janye jikinta daga wajen ta shige d'akin zuciyarta tana tunzira da b'acin rai gani take idan ta cigaba da tsayawa a wajensa komai ma zata iya aikata masa.

Shi ma tsaki ya ja ya koma falo. Ya zube a kujera madadin barcin ya yi gaba da shi sai ya ji tas idanunsa sun washe. Dama da ya ya samu
Ya yi barcin tunanin Hamda ya hana shi sak'at sannan ta zo ta sake caza masa kai da kalamai mafi muni da ya tsani ya ji a kunnuwansa alak'anta shi da matar ubansa. Ya runtse idanunsa gobe dai zai fasa b'aragurbin k'wan zai ga da wani ido Nanna zata dube shi, yana zaune anan har ya ji kiran sallah ya tashi ya fara nafilfili kafin shigar lokacin Sallah.

Daidai lokacin itama Hamdan sallah take ga yunwa ta addabeta kuma bata san fita falon balle ta had'u da Nanna ko d'azu duk masifar da aka buga tana juyo su daga cikin d'akin bud'ewa ne ba zata yi ba don bata shirya karb'ar tijarar Nanna ba. Idan ta matsu da son jin amsoshin tambayoyinta ta rutsa mijinta ta tambayeshi ita ba ruwanta.

Sai da ta ji wajen ya yi tsit alamar sun kwanta bayan sun yi sallah sannan cikin sand'a ta fito daga ita sai y'ar riga iya cinya cikin sand'a ta bud'e kitchen d'in bata san ta yi dogon motsin da wani zai ji ta. Sai dai ina duk abinda take yi idanunsa a kanta. Ya saki murmushi kawai ganin yarda gashinta ya mimmik'e sai ka yi zaton aljannah ce.

Tana tsaye a kitchen d'in tana warming d'in abinci da cup d'in
Madara a hannunta tana sha da sauri da alama yunwa take ji. Ji ta yi a jikinta alamar wani yana kallonta. Ta juyo a tsoarace zata saka ihu ya manna jikinsa da nata had'e da rufe mata baki ruf. "Ya jikin na mu?" Ya rad'a mata yana shafa k'asan mararta "Wannan babyn me yasa yake wahalar da mu ne? Tun ban gama cin amarcin ba. Mhmn" wani shock ne ya zuyarceta ta bud'e ido sosai alamar tsorata kafin ta juyo su yi facing juna "Baby fa na ji kace?" Ya d'aga mata gira yana jifanta da murmushi had'e da shafo mararta "Tabbas na yi ajiyar k'wai anan ko nace k'waya k'wayai baki ga yarda kika yi fresh ba?" Jikinta ta zare daga nasa "Ina ni sam ba ni da ciki ina y'ar yarinyata da ni zaka ce min ina da ciki." Gefen kunneta ya d'an ciza kad'an yana shafa kumatunta still a kunne ya sake rad'a mata "Y'ar yarinya kuma ta iya amsar sak'o ba?" "Ni dai ka tafi kada matarka ta zo ta ganka." Matsarta ya sake yi sosai "Menene don ta ganni ina ce halak d'ina ce sai
Na ce matata ce." Hamda ta tab'e baki "Ji sai ka ce gaske mutumin da ko magana baka iya yi min a gabanta." Hannunta ya murza sosai Kafin ya ce "Ba tsoro bane, zallar mamaki nake son na shayar da zuri'ar D'an Borno. Wanda labarin aure na da ke gobe zai girgiza su kin ga tilas Abbu zai tuhumi Ammi Uban da ya yi cikin ki.? Hawaye ya kawo idonta kafin ta shige jikinsa cikin kuka ta ce "Please Yaya Hammad Are you sure ni ba shegiya ba ce?" Bayanta ya hau shafawa "Da gaske ke ba shegiya ba ce da ubanki Hamda, kuma duk family sun San shi." Ta sake k'ank'ameshi "To wanene?" Ta fad'a da d'an shashshekar kuka Hammad ya saki hucin ajiyar zuciya a kunnenta kafin ya ce "Ko ma waye tilas gobe za ki Ji shi. Na riga na d'aukar mata alk'awari da bakina dai ba Zan tona mata asiri ba. Sai dai tun a lokacin na tabbatarwa kaina Zan aureki wannan dalililn shi Zai tona mata asiri tunda dai wa Ai ba ya auren k'anwarsa ko? Don haka tul fil azal da son aurenki da tarin k'aunarki na girma a zuciyata tun kina k''aramarki." Ya fad'a yana juye mata abincin "Maza ki je ki ci, ki tabbatar kuma kin koma barci gobe I yanzu na tabbatar ba shamakin da zai hana ni kwana dake a jikina ko?"
Sunkuyar da kanta ta yi ita kanta tana kewarsa sosai fiye da tunaninsa.
Ya rakata har d'akin da cup d'in shayinta sannan ya juyo ya koma falo makwancinsa.

_______________

Barci ne sosai ya d'aukesu don sai kusan sha biyun rana suka mik'e shima da kyar. Hamda ta samu kanta da wanka har da gyaran gashi ya kuma yi mata kyau sosai ta murza wet lips a bakin nata mai k'amshin strawberry.
Zama ta yi a gefen gadon sam ba ta son fita don haka ta yi zamanta tana aukin game a wayarta tunda ya ce sai after magriba za su je gidan. Yau fes ta tashi zuciyarta fresh take jinta. Ba mamaki hakan yana cikin farin cikin yau duniya zata san wacece ita? Ita kanta zata san wanene mahaifinta don haka take zakwad'in zuwanta gidan.

Nanna kuwa fes ta fito cikin hamshak'iyar shiga, zazzafan lace ta saka gold hannu da wuya sai zabga k'amshi take duk da zuciyarta ba dad'i tana jin haushin Hammad haka dai ta daure ta shiga kitchen don samar musu abinda za su ci su yi bud'a baki tunda ya kafe shigar dare za su yiwa gidan nasu.

Girkin cin mutum biyu kawai tayi. Yarda ta ke jin haushin Hamda bata jin zata iya yi mata abinci. K'amshin girkin ya ziyarci hancin Hamda ta ji babu abinda take son ci irin abinda aka dafa. Don haka cikin dakiya ta fito falon. Fuskarta ba yabo ba fallasa ta sauke ganinta akan Nanna. Da itama ta tsuke fuskarta tun bayan ganin fitowar Hamdan. Hammad dai yana zaune a gefe yana kallon yarda suke musayar kallo kamar za su amayar da wuta a bakinsu. Hamdan ta kalleta kamar an mata dole ta bud'e bakinta da kyar ta ce "Maman kamla ina yini an sha ruwa lafiya?" Idan kai da baka wajen ka amsa to Nanna ma ta amsa. Hamda ba ta damu da rashin amsawarba ta k'arasa dinning d'in saboda yawunta ya gama tsinkewa da abincin Nannan duk da ba wata tsiya bace illa indomie da k'wai ta sunkuci plate d'in da Nanna ta zubawa Hammad abinci ta yi hanyar bedroom d'inta. Da sauri Nanna ta ce "Kan uba, ke kin isa in dafa abinci ki ci." Zata bita Hammad ya rik'eta idanunsa narai-narai ya ce "Haba Nanna please mana, ki barta ta ci kina ga laulayin ciki ta ke." Idanu ta zuba masa murya a dashe ta ce "Kai ya aka yi ka san laulayin cikin ta ke?" Ya basar da maganar ta hanyar janyo plate d'in da ta zuba nata abincin ya d'ebo indomien da fork cikin salon da ya san yana gigita ta ya kuma saukar da fushinta ko wane iri ne ya ce "Ha, kin ji Sweetie na." Kamar k'aramar yarinya kuwa haka ta bud'e bakinta sai dai takaicin Hamda na nan a zuciyarta.

Sai da Hamda ta ci ta yi nak sannan ta saki hamdala tana murmushi hango idanun Nannan cikin masifa. Zamanta ta yi a d'aki ta k'i fita har san da Hammad ya k'walo mata kira. Tsaki ta yi ta mik'e tana nad'e mayafinta da d'aukan hand bag d'inta. Ta sake feshe jikinta da turare sannan ta maka Glass samfurin Gucci a idanunta wanda ake kira No respect.

A wajen gidan ta sameshi yana magana da mai gadi. Nanna kuwa ta hakimce a gaban mota. Hamda ta bud'e bayan motar ta shiga. Tare da cewa Nanna "Sannu Maman Kamla." A zafafe ta juyo zata fara mata masifa kenan Hammad ya shigo don haka ta had'iye fad'an nata.

Harabar gidan a cike take da alama ahalin gidan suna nan. Don dama duk yawanci da azimi goma ga azimi a gidan ahalin d'an borno suke shan ruwa. Sai a sannan zuciyar Hamda ta shiga matsanancin bugu. Ta kasa fita daga motar har sai da Hammad ya bud'e idanunsa cikin nata murya can k'asa ya ce ko sai na fito da ke?" Ta watsa masa wani kallo mai nuni da kamar zai iya? Ya girgiza kansa had'a da d'aga yatsansa d'aya daga yau ne dai gobe kowa ya san matsayinki a wajena."

Jikinta a sanyaye ta fito ta bi bayansa. Ahalin d'an Borno Nanna suka fara gani kafin Hammad ya yi sallama shima ya shiga sai Hamda. Aka kuma ci sa'a kowa da kowa yana falon Didin saboda ya fi kowane falo girma a gidan. Mutanen gurin cak suka yi da mamakin ganinsu musamman Ammi da cikinta ya yi wata irin hautsinawa cikin tsananin firgici ta sauke kallonta kan Hammad. Didi kuwa da fara'a ta dinga cewa maraba lale da mutanen bilningam maza Ku shigo. Inye Hamdede haka kika zambad'a kyau daga zuwanki k'asar mutane.... Abbu ya d'ago a zafafe ya sauke mugun kallonsa akan Hammad cikin tsawa ya ce....

Ya Abin Yake?Where stories live. Discover now