10

619 11 0
                                    

Alk'alamin Jikar Nashe.

Ya Abin Yake?

08033748387

Follow me on Wattpad

@Nazeefah381

ArewaBooks

@Nazeefah
https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e

Da safiyar ranar ta shirya tsaf, da azama ta ja motarta sai gidan Kady don sam kasa barci tayi jiya tambayar duniya kuma Abbu yayi mata sai ta ce Bata jin dad'i ne, shi yasa yau tana cewa zata Asibiti bai yi nawar hanata ba, don yanayin da ta kwana shi kansa abin ya yi matuk'ar rikitashi, sai ya ce tun bayan haihuwar Hamda bai tab'a riskarta a yanayi kwatankwacin na jiya ba.

Daga jin yanayin horn d'in motar Kady Ta tabbatar mutuniyartace ita kanta sam bata cikin nutsuwa don haka yau da wuri ta sallami mai gidan, tana shirin kiranta a waya sai gata ta bayyana. Da sauri ta bud'e k'ofar hasashenta kuwa ya yi dai-dai don Sakina ce cikin wani irin yanayi ta shigo parlourn, wullar da jakarta kawai tayi ta ce "Kina ganin kashe Hammad shi zai rufe b'aragurbin sirrina?

"K'warai kuwa." Kady ta masa mata cike da k'warin gwiwa "Rashin salwantar da rayuwar Hammad shi yake nuni da fallasuwar b'aragurbin k'wan da zai girgiza ahalin D'an Borno."

Sakina tayi tsai da ranta, kafin ta saki gwauran ajiyar zuciya, ta ce "Bana son salwantar rai, zan saka dai a sake masa gargad'i had'e da tabbatar masa da k'udirina na k'arshe idan har ya sake ya bayyanawa mutane gaskiyar lamari."

Kady tsaki ta ja, kafin ta ce "Ni ban ga dalilinki na rashin son kashe shi ba, mutumin da rayuwarsa kamar wata bala'i ce ga taki rayuwar, ke da kanki kince baya miki kallon mutunci balle ya girmamaki, kina tunanin idan ya cigaba da yi miki haka uwarsa ba zata so sanin dalili ba? Kina tunanin idan ya b'oyewa kowa zai iya b'oyewa mahaifiyarsa?"

Sakina ta share zufar da ta game goshinta. Hankalinta a tashe ta ce "Tabbas zancenki na kan hanya, saboda yarinyarsa Kamla yarda kika san kaki yarinyar nan Hamda tayi saboda tsananin kamarsu, ni kaina har mamakin bayyanuwar kamar nayi, wallahi abin ya bani tsoro kamar dai wata ishara ce Allah yake so ya nuna...."

"Shi nake so ki gane, ki cire duk wani shakku a kawar dashi daga doron k'asa, ina dalili? Tun ranar da abin ya afku na sanar da ke a kawar da shi kika wani ce a gargad'eshi, alhali kwalliya bata biya kud'in sabulu ba namijin dai da kike so baki haifeshi ba, kika tsaya cewa wai yaro ne zai ji tsoron tona hakan ga kowa, to ga dai yaro nan  ya girma kuma yana shirin bankad'a duk wani sirri idan ba kiyi wasa ba, haba idan da nice ai da tuni an wuce wajen."

Sakina ta ja ajiyar zuciya "Shikkenan, ki bari zan shigo yanke shawara  anjima insha Allah." Daga haka suka yi sallama, Sakina kam ta samu salama a zuciyarta ta kuma amince da shawarar Kady tana ganin hakan kawai shine mafita a gareta, da ahalin D'an Borno family gaba d'aya.

_____________________________

Tun asuba da ta farka bata koma ba gyara sashen Didi tayi kafin ta tafi sashen Amminta nan ma ta gyara. Wanka kawai tayi ta dawo parlourn Didin ta zauna had'e da d'aukar Alk'ur'ani tana karatu, Didi kuwa lazimi take, da radio a gefenta tana saurarar labaran BBC Hausa.
Sai da Takwas ta cika sannan ta shiga kitchen don d'ora abin karyawa kasancewar juma'a ce Didin bata azimin tsofaffi don idan watan azimin tsoffin ya shiga sau hud'u take yinsa duk sati litinin,talata,laraba da Alhamis.

Kunun tsamiya da ta saka wadataccen lemon tsami tayi musu, sannan ta soya musu k'osai da dankali da k'wai.

Kafin kace me? Har ta gama, ta kawo Daddumar Didin ta jeresu. Didin shi mata albarka kawai take tana fad'in Uwarki tayi farar haihuwa sai dai ita bata san haka ba shashasha, a zamanin nan samun yarinya mai hali irin naki ai sai an tona." Murmushi kawai Hamda tayi. Dai-dai lokacin da aka yi knocking k'ofar sashen Didin.

Ya Abin Yake?Where stories live. Discover now