40

125 0 0
                                    

Kafin ya gama gaya min, tuni duk wasu k'ofofin numfashina sun d'auke, na dinga kallonsa wani iri, ina jin yarda gumi ke tsiyaya a jikina, fatana a lokacin a ce mafarki nake ba ido bud'eba, wani irin abu nake ji, da gaske zahiri za'a samu kwatankwacin wannan abin da ya fad'a min a rayuwa, zuciyata ta tsananta bugu ina jifansa da wani irin kallo, da na san hakan zan ji daga gareshi da ban
Amince masa na saurari abinda ya fad'a min ba, yanzu ya sake d'ora min wani irin nauyi da ba mamaki ya saka zuciyata ta buga..."

Hammad ya saki ajiyar zuciya yana jifansu da kallo, yanayin da suke ciki ya tabbatar masa k'iris ta su zuciyar take jira ta buga. Sai ya gyara zama yana d'ora wa daga inda ya tsaya.

Tunda na tafi k'asar waje na mayar da hankalina kan business d'in da nake, burina na manta da waccan badak'alar rayuwar da maganar da ta bi ta dabaibaye min zuciya.
Na samu nutsuwar zuciya sosai a lokacin, bana tare da tension ko kad'an, sai wani lokaci ina office a zaune na samu kiran gaggawa daga wani asibi ana nemana.

Ina zuwa asibitin na ganshi cikin tashin hankali ya kasa zaune ya kasa tsaye. Ya cafki hannuna yana duba na da idanunsa da suke min kwarjini "Haihuwa zata yi Hammad!" Gaba na na ji ya buga, a hankali muryata a dashe nace masa "An kuma?" Ya jijjiga min kai don son tabbatar min da hasashensa An kuma Hammad, amma wannan karan ma ya zama Sirri tsakanina da kai kuma ka yi min alk'awarin rik'e y'ar ba tare da sanar da kowa ba kai ka haifeta ba, har zuwa lokacin da Sirrin zai bayyana a idon duniya..." cikin takaicin lamarin na cije leb'ena Ina dartse shi da k'arfi har wani gishiri na ji a bakina alamar na fasa shi jini ya fito, na dafe goshina kawai sai na samu kaina da jijjiga masa kai, alamar na karb'i alk'awarinsa koma mai zai faru ya faru.

A cikin daren ya min waya ta sauka, a cikin daren kuma na d'auko y'ar na dank'awa Nanna tare da yi mata kyakykyawan kashedi. Mun kai ruwa rana kafin ta amince da buk'atata bisa tursasawar zuciyarta ta cigaba da kula da KAMLA. Wannan shine abinda ya faru.

Takaicine yasa Abbu mik'ewa ya kai masa mari, "Me kake so ka fad'a mana, wani sirri ne da ba zaka fito ka fad'e shi ba kake kewaye-kewaye, don ubanka waye mutumin da kake zancensa tunda duk a cukurkud'e ka yi maganar BUZU ko GADANGA?" Idanunsa ya jefa cikin na GADANGA kafin ya runtse idanunsa ya bud'e ya d'aga hannunsa ya nuna shi. A bakinsa zaku ji komai, don alk'awari na d'aukar masa ba zan fad'a ba kuma na cika masa... mutanen wajen suka bi inda yake nunawa da kallo kafin cikin matuk'ar mamaki kowa ya ce "GADANGA!"

Ina yin ku mutanena.

Jikar Nashe taku ce, iya wuya ana tare one love kawai.
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Shi kansa Gadangan a razane yake kallon jama'ar da suka zuba masa ido, da gaske furucin Hammad d'in yazo masa a bazata jin kuma sun ambaci sunansa yasa gabansa fad'uwa, idanunsa cikin na Hammad yake masa kallon tuhuma.

Wani irin had'adden k'amshi ne ya ziyarci k'ofofin hancinsu k'amshin da kai tsaya za'a iya kiransa na tsadadden turaren da ya lashe mak'udan kud'i wajen siyansa. Gaba d'aya ya maye duk wani k'amshi da yake falon, kafin k'ofar falon ta bud'u. Kammalallen mutumin mai fuskar dattawan k'warai ta bayyana. Fuskarsa ba b'oyayyiya bace a kaf fad'in Nigeria an sanshi kasancewarsa na gaba-gaba a sahun masu arziki da suke k'asar. Ko yaro k'arami ka haskawa hotonsa direct zai fad'a maka sunansa kai tsaye K.K MUD'ALLABI, Dogo ne sosai mai cikar zati da Haiba gami da kamala. Excort d'insa ne a bayansa suke biye da shi suna sanye da bak'aken kaya wuluk kafin ya murza yatsun hannayensa alamar da take nuna musu baya buk'atarsu a wajen su fita. Suka sara masa had'e da juyawa da sassarfa. Hammad da sauri yazo ya tareshi cikin matuk'ar girmamawa shi kuma ya ja Hammad d'in jikinsa ya bashi kyakykyawar runguma, jin Hammad d'in yake kamar jininsa kamar shi ya tsuguna ya haifeshi.

Idanun d'aukacin mutanen da ke falon zube suke a kansa suna mamakin mai ya kawo KK Mud'allab gidansu. Mutumin da yake wahalar gani a K'asar sai kana da babban matsayi sannan kake ganinshi, shima d'in on appointment, ba su gama wancan mamakin ba wani ya kashesu, ta yarda ya rungume Hammad tsaf a jikinsa tamkar zai mayar da shi cikinsa. Hammad ya ja hannunsa ya isar da shi har tsakiyar falon aka sama masa waje ya zauna, fuskarsa d'auke da matsanancin murmushi mai bayyana tsananin farincikinsa. Zai iya cewa bai tab'a riskar kansa a farinciki kamar na ranar ba. Nan aka shiga gaisheshi idanunsa yake zagaye falon da su kafin ya sauke idanunsa kan Hamda, ko ba'a fad'a masa ba ya san ita ce, ya san Hamda ce ba ya neman k'arin bayani, ji yake tamkar ya jata jikinsa ya sanyata a k'irjinsa ya rungumeta. Shiru suka yi, d'aukacin mutane falon suna jiran k'arin bayani daga bakin Hammad, da shima tasa fuskar ta kasa b'oye murna da farin cikin da yake yi, ko bakomai yau zai huta da ajiyar wannan gundumemen sirrin da yake, da kullum tunaninsa ranar da zai fallasu, ya dad'e yana jigatar da shi duk dare da abin yake kwana yake ta shi.

Ya Abin Yake?Where stories live. Discover now