*♡ YA ABIN YAKE? ♡*
Na
Nazeefah Sabo Nashe08033748387
Follow me on ArewaBooks
@nazeefah
https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e
E.O.W
_Yauma tafe nake da wani sabon rubutun wanda salonsa ya bambanta da waɗancan kamar yarda dai kuka sani. Fatana na nishaɗantar daku na kuma wasa muku ƙwaƙwalwa Sabon littafi kenan Mai Sabon Salo..._
_Daga jin sunansa kun san akwai rikita-rikita ku dai ku biyo.. ina masoya *ME ZAN YI DA ITA?.*_Page 1
Kamar yarda ta saba tashin y'arta ta kullum, yau ma ranta a b'ace take shurinta da k'afa tana dukanta wai duk so take ta tashi. Da kyar Hamda ta bud'e idonta ta zuba su akan mahaifiyarta. Zazzafan zazzab'ine a jikinta amma hakan bai sa ta d'aga mata k'afa ba.
Ta bud'e idonta da kyar da
duk sun canja launi na azabar da take ciki, ba yau bane mafari haka dama can Ammin take tashinta daga barcin a kowace asubar fari, tamkar ba mahaifiyar da ta tsuguna ta haifota duniya ba. Duk da a kullum tana tantamar kasancewarta tsatson Ammin,saboda tsana muraran da take nuna mata, wanda ko ƴar tsintuwa sai haka a yarda Ammin take ɗaukar lamarinta.Hawayen idonta ya zuba akan fuskarta, da gaske tana jin ƙunar lamarin sau tari Mahmah da ta ksance kishiyar uwarta tafi lura da lamarinta fiye da Ammin koda kuwa a ɓoye ne don idan ta fuskanci ka na tausaya mata ma tsanarka take sosai ta kuma ja maka kashedi game da shiga shirgin yarinyarta.
Da kyar ta miƙe zaune bayan ta dafa yaloluwar katifar ta irin ta ƴan boarding da take kwana akai ita ɗin ma tatace ta makaranta take kwana akai bayan gama karatunta. Hannayenta dafe da goshinta alamar kanta yana matuƙar sara mata ta ce "please Ammi wallahi yau da ciwon kai na tashi ba zan iya komai ba." haɗe rai tayi idanunta cikin nata tace "ƙwarai tunda yau kika saba aikin da ciwo a jikinki kin tashi ko sai mangareki?ai tunda kika sake kika zo duniya duk da ba ke naso haifa ba wallahi kin yi ta shan baƙar wahala kenan, ko kaɗan bana son na buɗe ido na ganki na tsaneki tsana mafi muni da ban taɓa yiwa wani ita ba, ki miƙe bakinki alaikum kije ki fara aikin da kika saba."
Da kyar ta miƙe zuciyarta na wani irin hanƙaron ɓacin rai ta zuba idonta akan gadon da yake bedroom ɗin yayyenta ne zube su uku suna shan barcinsu akan gadajen da suke zube reras a cikin faffaɗan bedroom ɗin.. kuma duk babu wanda bai bata shekaru ba a
Cikinsu babbar ta bata ak'alla shekara goma mabiyarta Ta bata shekara takwas yayinda wacce take bi ta bata shekaru shidda cif. Kuma duk ba suyi aureba. Yayarsu Najwa ce kawai mai aure a d'akin su.
Hawayenta Ya sake ninkuwa fiye da nada, ta rasa me tayiwa Ammi da tayi mata wannan muguwar tsanar ga yayyenta nan zube bata saka su aikin ba sai ita da take ƙaramarsu, madadin auta da aka sani da riritawa ita mahaifiyarta wulaƙantata take tana kuma nuna mata tsana muraran da gaske bata sonta. Ta faɗa a gaban idonta ta faɗa a bayan idonta. Hasashe kala-kala tayi tana son gano dalilin tsanar sai dai sam bata ci ribar gane gaskiya ba.Bata Sani ba Ko don kasancewarta baƙa saɓanin su da suka kasance farare tas dasu don kalar Ammin suka ɗauko gaba ɗaya kasancewarta balarabiyar jordan, Gashinta yalolo suka ɗauko saɓanin ita da ta zamo kalar mutanen Habasha, Gashinta kuwa.cunkus yake ga taurin tsiya don ko kitsashi ba a iya yi, sau tari haka take ƙudunduneshi ta cusashi a tsakiyar kai yayi mata kamar gammo. Ba ta yiyo kyan Ammi ba ko kaɗan bata sani ba ko wannan shine silar tsanar, duk da ta sha ji mutane da Dama suna faɗin tafi ƴan uwanta kyau don dai ita ƙananan kyau ne da ita ta kuma fi ƴan uwanta dirin jiki sosai da sosai. Bata san dalilin tsanar ba duk da tana kyautata zaton wannan ne dalilin saɓanin hasashenta taji kuma mutane da dama suna faɗin don taso ta haifi mace ne a haihuwarta kamar yarda kishiyarta tayi mata fintinƙau a haihuwar yara maza to rashin zuwanta a namiji tun bayan da aka yi mata scanning aka tabbatar mata namiji ne ta 'kwallafa rai Lamarin Allah kuma ranar haihuwar sai taga mace itama macen Gata kalar mutanen Habasha bata da Haske kamar larabawan da ta saba haifa ba.
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.