Cije leb'ena na yi kafin na ce "Zan jingine auren nasa, ta hanyar da shi ma ba zai tab'a zata ba." Daga nan na gaya mata shawarar da na yanke. Sakin murmurshi ta yi tana dunk'ule hannunta da d'aga min alamar jinjina ta ce "idan haka ne, tabbas sai na ce k'wak'walwarki ta fi tawa ja, kutmelesi ta yaya ki ka yi wannan tunanin? Kin ga shikkenan za ki haifi halastacciyya y'a inda ko nan gaba maganar ta tashi za ki sanar da jama'a da ubanta. Amma fa kin san dole a samo shaidu." Na jijjiga kai "Shaidu ba matsala ba ne, yanda nake tunanin zan saka Umar ya sake ni cikin sauk'i shine abin ji, amma zan shirya tafiya Jordan don na samo shawara mai b'ullewa." Ta d'aga kai "In dai shawara ki ke nema, ba sai kin je jordan ba, ki ba shi abin maye ya sha a lokacin sai ki tursasashi sai ya sake ki ki sa kuma ya rubuta a takarda, ta yarda duk bala'insa bai isa ya k'aryata ba, daga nan sai ki ce masa za ki yi zaman iddarki." Na d'aga mata kai kafin na ce "To ta yaya? Zan zauna a gidansa har sai na yi zaman idda na samu ciki na haife sannan zan koma wa aurensa." Ta yi jim kafin ta ce "Dole ki san yarda ki ka tsara ki ka sako Ummeey a maganar ita ce zata zame mana garkuwa ta hanyar ce masa za ki yi zaman y'ay'anki, amma fa ki tabbata saki uku ya yi miki, ki yi masa duk tijarar da zata saka dole sai bayan kin haihu kin d'aura aure da wani ko na awanni ne sannan ya sake ki shi kuma ya mayar da ke, duk da auren kisan wuta ba kyau amma a wannan gab'ar dole haka za'a yi, tunda kin san ke ba auren kisan wutan za kiyi ba, already da aurenku da buzu, idan ya rasa wanda zai zab'o sai ki ce ke kina da shi, sai mu gabatar da buzu mai gadi, daman mijinki ne kin ga bai zama auren kisan wuta ba." Na jinjina lamarin kafin na amince da hakan za'a yi. Yanzu buk'atar yanda za mu shawo kanta da Umar ya sake ni kawai.
Tun daga lokacin na d'aura d'amabar yi wa Umar rashin mutunci, ba lamarin da yake bak'anta masa kamar yarda na yi shakulatun b'angaro da shi a rayuwar auren mu, a kuma duk sanda aka yi magana na kan sanar da shi danginsa ba sa so na ni na gaji da shi ya sakeni kawai. Na sha fad'a masa magana musamman akan mahaifiyarsa, amma ko gezau sai dai ya dinga min hawaye yana cewa na taimakeshi ni ce rayuwarsa.
Ranar muna zaune da daddare na fece wanka sai zabga k'amshi nake, chewingum ne a bakina ina masa taunar rashin arziki. Kawai Umar ya shigo wata ajiyar zuciya ya saki zatonsa daidaitawa nake son mu yi, ni kuwa a zuciyata na yi alk'awarin dole ne ma Umar yau ya sakeni kuma a cikin hankalinsa ba ba wai a maye kamar yarda da muka shirya ba. Ya zauna gefen hannun kujerar da nake yana jifana da murmushi, abin ya tab'a zuciyata amma na share na tsuke fuskata ina cigaba da taunar chewingum d'in da nake. Ya shiga nuna min yarda ya yi kewata amma idona cikin nasa na dinga zabga masa rashin mutunci, ga shi a yanayin da muke dole ya shiga damuwa saboda ya yi nisa ba ya jin kira. A tsawa ce na janye jikina na ce "Umar ban san kai tantirin mara zuciya bane sai yanzu, Haba mutum sai ka ce bunsuru na ce bana sonka bana sonka ka k'i yarda, to yau zan sake jaddada maka idan ka cika d'an halak cikin uwarka da ubanka ka sakeni kuma saki uku ba d'aya ba." Tunda nake ban tab'a ganin zallar b'acin ransa kamar na wannan ranar ba, fuskarsa ta had'e sosai sai hucin bak'in ciki yake murya a shak'e ya ce "Ko kece Hurul aini na sake ki saki uku.." Ya yi furucin wasu hawaye na zubar masa a k'unci, ya mik'e ya zira rigarsa. Sai na ga kawai ya durk'ushe ya kife kansa a kujera ya saki wani irin rikirkitaccen kuka. Buga kansa yake yana fad'in "Why? Why? Sakna?" Ni kaina a yadarance na saki kukan ina rungumeshi Umar ka sakeni? Saki fa Umar?" Tsam ya rik'e ni a jikinsa sai saukar da numfashi yake yana "Na shiga uku Sakna, ban san me ya shiga kaina na aikata ba, ke kika jawo Sakna." Ji na yi numfashinsa ya yi d'if alamar ya d'auke. Da sauri na mik'e ina jijjiga shi "please Umar kada mu yi haka da kai don Allah ka tashi." A diririce cike da firgicin lamarin na shige toilet d'in d'akin na d'ebo ruwa na watsa masa. Sai ga shi ya kawo numfashi mai nauyi, idanunsa cikin nawa ya mik'o min hannu, muryarsa can k'asa ya ce "Allah yasa mummmunan mafarki nake, ba a zahiri abubuwan da na gani Suka faru ba." Cikin yaudararrun hawaye na shiga gyad'a masa kai kafin na ce "Mai afkuwa ta afku Umar ka sake ni har saki uku? Yanzu mai Zan ce da dangina? Musamman wad'anda dama suka tabbatar min nan gaba sai ka cutar da ni, mahaifiyata dama a kullum burinta kenan ka sakeni, ga shi yanzu ka aiwatar da hakan, duk abinda ka ji na gaya maka ko nake maka, wallahi ba har cikin zuciyata bane, duk na yi ne don in tabbatar da son da kake min. Sai ga shi ka yi abinda muka haramta da juna har abada ko na ce sai na yi wani auren mijin ya sake ni sannan ka ke da damar mayar dani." Wani irin hawaye Umar ya saki, yana sake ja na jikinsa. Ni kuwa don in sake tunzira shi na ce "Wallahi ka ban mamaki, daga gwaji ta yaya kake zaton ni zan k'i ka? Alhali saboda kai na rabu da dangina da k'asata na zo nan inda ban san kowa ba. Na tabbata yanzu Ummeey ta ji labari ba zata bari mu komawa auren mu ba, cewa zata yi na tattaro na taho. Haka kaima idan Didi ta ji labarin shikkenan ta samu abinda take so." A gigice Umar ya rungumeni k'am a kunne ya dinga rad'a min "Me yasa kika min irin wannan wasan Sakna? A lokacin da kika san ba zan iya controlling kaina ba, kin san rashin kusantarki babbar masifa ce a wajena, please ba wanda za mu gayawa ya zama sirri a tsakaninmu, idan kin gama idda a sirrance zan d'aura miki aure da mutumin da na tabbata a ranar ma zai iya sakin ki na mayar da aurenmu ba tare da kowa ya sani ba." Na yi d'an jim har farincikin da yake cikin zuciyata ya bayyana b'aro-b'aro akan fuskata na k'ank'ameshi sosai a kunne na dinga rad'a masa na amince ya zama sirri a tsakaninmu amma ranar girkina ya zaka yi?" Ya runtse idanunsa yana dafe k'irjinsa kafin ya ce "Dole zan nisanci garin nan har ki ka gama idda, ina dawowa a d'aura mana aure, don ba zan iya controlling kaina idan ina ganinki ba Allah ya sani. Auren kisan wuta ba bu kyau amma da mu aikata Zina gwara mu aikata waccan b'arnar. Allah ka yafe mana don girman zatinka." Ya fad'a yana saka kansa a cikin tafukan hannayena sai ga shi na ji yana wani irin gigitaccen kuka, mai tada hankali. Kafin ya mik'e cikin kasala da mutuwar jiki ya fice daga d'akin yana waiwayena. Nima hawayen ne suka zubo min masu zafin gaske sai na ji kamar ban kyauta ba dama ban aikata son zuciyata ba, amma buk'ata ta da haihuwar d'a namiji shine ya janyo komai. In dai Zan samu cikar muradina to komai na yi gani nake dai-dai ne a lokacin.
Daga ranar muka shiga wata irin rayuwa ni da Umar, ya zama ba shi da walwala ko kad'an. Sannan ya shiga neman visa ba ji ba gani. Idan ba ku manta ba shine lokacin da ya tafi Dubai ya yi zaman sa a can sai dai ya aiko da kaya a siyar masa idan an had'a kud'in a aika masa. Tsawon watansa hud'u a can.
Ni kuma a lokacin ni da Kady muka shiga farautar mai gadi duk da jira nake na gama idda sannan na bayyana masa k'udirina. Amma fa ina yawan yi masa d'inki sannan na dinga sanar da shi bana son k'azanta. Don haka ya rage k'azantar.
Daren da na gama idda, a daren na kira shi na bijiro masa da buk'ata daga ni sai Kady a zaune a falon har rufe k'ofa muka yi." Tsawon lokaci ya d'auka shiru kafin ya d'ago ya yi min kallon cikin ido. Kady ta kafeshi da ido cikin tsare gira ta ce Saduwa d'aya za kuyi ka zabga mata saki uku bayan mun tabbatar da cikinka a jiKinta." Na gyara zama kafin nima na d'ora da cewa " Tun bayan da ka sanar min, yawaitar maza a zuri'arku, na tabbata Allah ne ya kawo min kai don na samu namijin da nake so, amma fa ta hanyar aure ba hanyar zina ba." Kady ta sake tsareshi da ido kafin ta ce "A gobe muke so komai ya wakana saboda nan da sati biyu Alhajin zai dawo, ban dama an rufe dubai d'in da tuni a yau zai dawo a mayar musu da aurensu. Abinda muke so kafin ya dawo ya zama da tayin cikin namiji a mahaifarta, inda da zarar ya bijiro mata da maganar auren kisan wuta zata sanar da shi ai da cikinsa a jikinta, ka ga ba aure kenan har sai bayan ta haife. Amma fa duniya zata d'auka yes cikinsa ne. Tunda ba kowa ya san da sakin ba, kai ma kuma ya zama sirri a wajenka, don bayyanar sirrin kamar fansar da ranka ne, kuma tunda muka gaya maka sirrin mu ya zama dole ka yi mana abinda muke so. Sannan albishir d'in da zan maka bayan kwasar ganimar jikin tsaleleliyar mace akwai kyautar miliyan biyu cus da zamu maka ka tattara ka koma garinku." Ya share zufar goshinsa kafin ya d'an saki murmushi ya tabbatar mana da ya amince. A daren ranar Kady da ni da wasu maza a wani k'auyen k'aramar hukumar k'araye aka d'aura mana aure. Sai da muka amshi sunayen shaidun saboda ko nan gaba magana za ta tashi sannan muka taho.
Na biya da shi yarda zai dinga zuwa gyaran kai da hak'oransa. Kady sai tsiya take min.
Bayan kwana biyu Buzu ya dawo tas da shi. A kuma lokacin ne aka yi wata mutuwa a Gwarzo duk gidan suka tattara suka tafi. Na had'a musu har yara na suka tafi da su.
Wannan damar na samu na kira buzu mai gadi na muka keb'ance a d'akina. Bayan na saka shi ya datse gate d'in gidan. Sai dai a rashin sani da tsautsayi sai ga Hammad ya dawo ranar kamar an turo shi sabida ba ya dawowa daga kasuwa da rana. Shi kuma ya riskemu a d'akin wanda ban san dalilin da ya kai shi d'akina a ranar ba. Sai ganinsa kawai muka yi, a lokacin ya turo k'ofar d'akin. Cikin gigitaccen yanayi ya saki ihu, ihun da yaja hankalinmu muka mik'e a firgice ina jan bargo. Buzu yana neman hanyar guduwa....Jikar Nashe taku ce
❤️❤️❤️❤️❤️🙏
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.