Sosai hantar cikinsa ta kad'a da tambayar k'wakkwafin da ta jeho masa. A hankali ya yi k'ok'arin matsewa ta hanyar jan hancinta "Idonki bai lura bane, sau tari ina tafiya da kaya office na dawo da wasu musamman idan lokacin damuna irin wannan ya kama lokacin ruwan sama. Turare kuwa may be hancinki ne ya ji." Ta d'an saki ajiyar zuciya kad'an duk da ba wai ta amince da abinda ya ce bane zuciyarta tabbas tana wasiwasin lamarin. Cikin tsare gira sosai ta ce "idan ma wani abu ne a ranka ka tattara shi gefe ka ajiye don ba zan amince ka yi Aureba balle na yarda da kwamacalar had'a shimfid'a da
Wata mace." Ya bi idanunta da kallo ya tabbatar iya zallar gaskiyarta ta fad'a tabbas nan gaba kad'an ashe za a kwashi drama don ruwa da iska ba mai saka shi rabuwa da Hamda ko a da ma balle yanzu da ya kwankwad'i zallar madarar dad'i daga gareta.
Murmushi kawai ya sakar mata yana sauka daga gadon. Burinsa ya je yaga Hamda sai dai ya san bai isa ba a wannan lokacin don haka tilas ya hak'ura.Sai yamma bayan ya d'auko yara daga makaranta. Sannan ya sake shirinsa bayan ya yi wanka ya sameta a d'akinta. Zaune take a gaban mudubi tana sake tsantsarawa kanta kwalliya sam Nanna bata gajiya da kwalliya lamarin son kwalliya a jininta yake. Ya saki murmushi yana k'arasawa bakin mudubin. Ta jikin mudubin ta dinga masa kallon mamaki. Yana k'arasawa ya dafa kafad'unta yana kallon kansu ta jikin mudubin murya a raunane ya ce "Kin yi kyau sosai M. Khairi." Bakinta ta d'an turo kad'an kafin ta tab'e bakin ta ce "Sai ina kuma naga ka fece wanka?" Ya shafa gefen kumatunsa ya yi kalar tausayi "Am sorry dear, kin san abinka da d'an k'wadago yau ma kwanan office d'in Zan yi." Wani kallo ta jefe shi da shi na kada ka raina min hankali sannan ta d'auke kanta fuska a d'aure ta ce "Dear bana son fa rashin gaskiya, shekararka nawa a office d'in baka tab'a aikin kwana ba sai yanzu ka tsiro min da zancen aikin kwana." Wuyanta ya murza a hankali cikin kwantar da murya ya ce "To ya zan yi? May be nextweek ma za mu wuce Nigeria insha Allah, ina tunanin su Khairi ma a gidan Musty zan bar su."
Baki sake take kallonsa ta ce "Nigeria kuma? For what reason duka-duka how many days rabonmu da k'asar ni sam wallahi ko sunanta bana son ji balle shiga cikinta nan kwana kusa." Ya girgiza kai cikin mamakin furucinta ya ce "Me yasa? Ke da k'asarki ta haihuwa?" Ta girgiza kai "Abinda ya faru ba k'aramin girgiza ni yayi ba shi yasa sam bana son sake ziyartar k'asar nan kwana kusa" yana jan jelar gashinta mai tsananin sulb'i da k'yalli ya ce "Ya zame miki dole ki je don kira ne daga Umma Asma'u na gaggawa akan wancan maganar da kike gudu, na fi son a yi komai a gabanki ki zama ready nan da 5 days." Daga haka ya saka kai ya fice yana fad'in take care. Idanu kawai ta bishi da shi zuciyarta cike da d'imuwa gani take kamar a tsukun lokacin a canja mata shi ganin yarda yake walwala da farin ciki tamkar sabon Ango da sauri gabanta ya buga da tsoro dafatan kada Allah ya k'addara mata ganin ranar da za'a yi mata kishiya. Ta girgiza kai tare da runtse ido ita kanta bata hasasho kalar haukan da zata yi ba.__________________
Cike da nishad'i da walwala ya kutsa kansa cikin falon. Bakinsa d'auke da wak'ok'in soyayya na larabci. A kwance ya ganta fuskarta a had'e duk da ta sha kwalliya cikin wasu matsatstsun English wears da suka bayyana tsantsar kyawun dirin jikinta. Amma sam fuskarta ba walwala idanunta kuwa sun nuna alamar ta sha kuka don sun d'an kumbura. A tunaninta tunda ta ji shiru ba zai dawo ba duk da dagewar da tayi ta tsantsara masa girki mai rai da motsi. Amma ta ji shi shiru tun safe daga cewa bari ya kai y'an makaranta ya dawo. Zama ya yi daf da ita sosai yana janta saman jikinsa "Me ya faru Nuri?" Ya rad'a mata a kunne "Ko missing d'ina kika yi?" Samun kanta ta yi da d'aga masa kai tana k'udundune kanta a jikinsa. Ya saki murmushi yana k'ok'arin d'aga fuskarta ta runtse ido kafin ta ce "Ni ka kyaleni bayan ba ka damu da ni ba ka yi tafiyarka ka bar ni." Murmushi ya ja yana kaiwa lab'b'anta sumbata tuni ya kashe bakin tsiwar ta yi muk'us kafin ya d'ago yana jifanta da murmushi "Tarbar da ya kamata ki yi min kenan, amma kin tsaya shagwab'a. Idan mace ta yi missing mijinta kyakykyawar runguma take kai masa ba k'ananan mita ba. Ni haka matata ta saba min." D'if ji da ganinta suka d'auke saboda tsananin kishi ta zare jikinta a hankali ta koma gefe idanunta na shirin zubar da ruwa. Yana murmushin ya sake damk'ota, tana tirjewa ya d'aga ta cak "Bari na je na baki hak'uri a d'aki mana. Kin ga idan na tada miki da mikin jikinki kya tuna ni mijinki ne ki dinga girmamani." Bakinta ta turo tana kicinyar k'wace jikinta ta sauka da kyar tana tirjewa da bubbuga k'afa "Haka kawai sai ka dinga min zancen matarka ka san yarda zuciyata take ji." Kallon mamaki yake binta da shi ya kuma tabbatar iya gaskiyar furucinta kenan. A yarda yake hangowa ma kamar Hamda ta fi Nanna kishi ashe akwai aiki ja a gabansa. Cikin tsokana ya ce "Tab, amma fa Nuri kin d'auko da zafi ki aure mata miji kuma ki dinga kishinta? Ita kuma ya kike so ta yi? Da kika kwace mata ni ya zama dole ki rage kishin nan don har yanzu Nanna bata san na aureki bane da kin gane kalar kishinki bakomai bane akan nata. Shekarar mu kusan nawa ko gado ba ma rabawa sai ta kama dole ko haihuwa ta yi bana yarda mu raba d'aki. Kullu yaumin manne take a jikina." Wannan karan Hamda ji ta yi kamar kanta yana son darewa biyu da sauri ta runtse idonta cikin b'acin rai ta ce "Ka san da haka wa ya ce ka aureni me yasa baka bari zunnuraini ya aureni ba? Ko kuma ka kyaleni na samo mijina ba mijin wata ba." Da sauri ya d'alle bakinta cikin jin zafin furucinta ya kuma manne ta da jikinsa yana ganin kamar wani zai kwace masa ita. Haushin lafazinta ne ya sa ya dinga datse leb'ensa ya kuma kakkafe ta da idanunsa "Kada ki sake min kwatankwacin wannan furucin. Shi kansa Zunnurainin ji na yi kamar na harbeshi san da na ganku kuna zance. A zuwansa na biyu kuwa da kaina na sameshi na ja kunnensa akan cewa an miki miji ya ja mutuncinsa. Ta yi lamo a jikinsa tana jin yarda yanayin bugawar zuciyarsa ya sauya ashe shima dai yana kishinta ba ita kad'ai take kishinsa ba. Shafa kanta ya yi ya jishi cunkus alamar yau bata taje ba.
Ya ja gashin sosai kafin ya ce "Dole gobe da kaina na kai ki saloon a gyara gashin nan ya yi tauri da yawa ba irin na Nanna bane mai taushin gaske." Da sauri ya rik'e bakinsa dariya na shirin kama shi ganin yarda ta yi da fuska ya ja karan hancinta "Seriously gashin Nanna ya fi na ki kyau ko don ita tana gyarawa ne. Ke ma ki dage da gyara don ina son inji gashin mace yana sulb'i. Bata san sanda ta kai wa hannunsa cizo ba cikin takaicin maganganunsa sannan ta fad'a jikinsa tana shirin saka kuka ya yi mata abinda tilas ya sata had'iye guntun hawayen shagwab'arta.______________
Haka dai suka dinga zuba soyayyarsu har ana i gobe azimi don haka da daddare ya zaunar da ita kusa da shi murya k'asa-k'asa ya ce "Please mu yi magana ta fahimta, gobe azimi gaskiya ba zan iya jurar ganinki da rana na kyaleki ba. Ba tare da na ji wani feeling a raina ba. Ina gudun karyewar azimina don haka zan dinga zuwa bayan magriba na tafi da asussuba na sanar da Nanna aiki na ya koma na dare so ba ni da fargaba ta wannan fannin." Runtse idanunta ta yi tana jin kunyar kalamansa don duk da a lokacin ta d'an fara sakewa da shi. "Nan da 3 days za mu tafi Nigeria insha Allah, dad'in da na ji ma ba ku fara lectures ba har ma je mu dawo ma da izinin Allah." Ta d'an d'aga kai tana jin yarda k'irjinta yake bugu a duk sa'ilin da aka ambaci Nigeria.
Haka dai suka dinga morewa amarcinsu kafin ranar tafiyarsu ta zo. Da kansa ya kai su Khairi gidan Abba Musty kuma sam ba su damu ba murna ma suke don da sa'anninsu a gidan kuma school d'in su d'aya. Ga Abba Musty da son yara.
A daren ranar a gidan Nanna ya kwana. Don haka Hamda kwan ta yi tana sallah da addu'ar kada Allah ya kawo abinda zai rabata da Hammad. Ubangiji yasa zamansu ya d'ore har aljanna. Tuni ta shirya akwatinta tsaf.
Da safe kuwa da kyar ta mik'e don tafiyar rana za suyi. Wanka ta yi sosai ta sanya wata doguwar riga mai masifar kyau light purple ta yane kanta da mayafin rigar. Kyau kam ta zuba shi a ranar da duk wanda ya kalleta na tabbata sai ya sake jiyowa ya kalleta.
Tun a mota Nanna da taga yayi parking a k'ofar gidan ta kalleshi "Me za muyi anan ko mota zaka ajiye? Wai gidan ma waye tukunna?" Fuskarsa a d'aure ya ce "Wace tambaya kike so na amsa miki? Ko gidan ma waye ai yanzu zaki gani."
Ya fad'a yana ficewa daga motar. Wannan karan madadin ya bud'e da key kamar yarda ya saba sai ya danna door bellHamda da take zaune mamakin waye ya kamata ta mik'e a hankali ta bud'e k'ofar. Kallo d'aya ya yi mata ya d'auke kai "Oya ki yi sauri ki fito muna mota." Daga haka ya juya. Hamda da take tsaye turus ta yi tana kallonsa tana mamakin dalilin canjin fuskarsa ko don ya d'auko Hakimar tasa ne?
Jikar Nashe ce...
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.