_~ALƘALAMIN JIKAR NASHE
YA ABIN YAKE ?
LIttafin Nazeefah Nashe.
08033748387
Follow me on ArewaBooks
@nazeefah
https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽
ELEGANT ONLINE WRITERS
(Haɗin kai shine takenmu.)
Page 5
Ina macen datake fama da ciwon mara in mijin yana saduwa dake kirinka jin xafi to kixo kimallaki female careIna masu fama da basir constfree tea yana magnin basir yana gyara fata tayi kyau
Royal jelly ya gyara mace yafito mata da shafe dinta kama daga breast hips duwawo
Fat bunner yana rage kitse ina wanda kitse ya mata yawa a jiki kigarxayo kimallaki naki 09131164861
Gamai bukatan yin register xai iyayi yasaya afarashin company
Company ght zakiyi registered akan 4500 kikawo mutun biyu suyi siyaya company zatabaki 36000 inbaki shiryaba karkimin mgn ngd
****************************
_Mu d'in ba wasu masu wadata
bane sai dai muna cikin ni'imar ubangiji, don bamu rasa ci ba, bamu rasa sha ba, Kakanku a tsaye yake sosai akan iyalinsa ta yarda duk abinka baka isa ka hango gazawarsa ba, ya tsaya sosai musamman ga karatun iyayenku, burinsa a kullum bai wuce yaga sun samu nagartaccen ilimi ba, na boko da na muhammadiyya, Musamman Babanki Umar. Sanda ya gama secondary School Allah ya taimake shi har jami'a yaje can zaria inda yayi karatunsa a 'bangaren Zane-Zane kasancewarsa mai hazaƙa wata rana kawai yazo min da labari mai dad'i wai Gwamnati ta d'au nauyin karatunsu 'kasar waje can 'bangaren larabawa 'kasar Jordan zasu je su yi babban degree a can. Mun yi murna sosai sai dai Kakanku ya ce bai isa ba, ba zai tafi ba sai da aurensa, amma mahaifinku ya turje ya kuma kawo uzurin gwamnati tace ba zata d'au masu mata ba saboda ba zasu d'au nauyin mutum sannan su d'au nauyin iyalinsa ba, har da ce mana sunce sai dai ya hak'ura Haka dai dole muka k'yaleshi ya tafi ashe tafiyar zata zame mana jangwamgwam domin dai a can ya had'u da alak'ak'an uwarki ya aura.Tafiyarsa da wata uku yayi mana aike akan ya samu mata zai yi aure a can. Ai kuwa na rufe idona na ce bai isaba, hakan ya tashi hankalinsa sai gashi ya dawo k'asar ba shiri lokacin watansa shidda da tafiya. Da Allah da annabi da saka malamai suyi mana wa'azi muka amince da yayi auren amma da sharad'in ni da kakanku zamu je muga tushe da asalin yarinyar. Bai wani damu ba ya ce mana ya yarda. Nan muka fara cuku-cukun tafiya kakanku ya siyar da gonarsa d'aya muka tafi har da k'aninsa da suke ciki d'aya wanda kuke kira Baffa Mamman.
Mun samu tarba Ta mutunci daga iyayenta,babu aibu sam a tattare da su dattawa ne sosai, don shi kansa Umarun a gidansu yake zaune kuma yana d'an aiki a kamfanin mahaifinsu mutumin kirki shima daga Nigeria yaje karatu sai ya had'u da uwarta mutuniyar Jordan d'in ta nuna bu'katar aurensa shikkenan zamansa ya koma can don haka da yaga Umar bahaushe ne ya ja shi a jikinsa,
ya shiga farin ciki, ko da yarinyarsa ta nuna tana sonsa take ya amince ya bashi aurenta.Hankalina ya kwanta da naga ubanta bahaushe ne, kuma har kwatancen gidan su yayi mana a garin Niger (Minna) cikin unguwar limawa nan ce mahaifar Kakanku na wajen uwa, ta daina muku fankamar wai asalinta balarabiya ce, asalin uwarta dai.Kakanku ya ce zai bincika ya gani, ai Niger ba bak'on waje bane a wajensa.
Ba mu dawo ba sai da aka d'aura auren, amma jikina ya yi sanyi da na lura da uwar Sakina ce take kula da al'amuran gidan shi uban nasu ba shi da ta cewa sai abinda Ta d'aurashi a kai, kuma yarinyar da naji suna kira Sakna ni ce nan na mayar mata da sunanta Sakina har yanzu a garinsu Sakna ake kiranta, kaf halayen uwarta ne a tare da ita bata ganin mutane da gashi. Gaisuwa kanta sai taga dama take min gashi iyayen suna ji da ita tamkar masifa ko don itace babba.
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.