Haka Mustyn ya so ya ce a zahirance sai dai ya tuna warning d'in abokinsa akan fad'ar hakan don haka ya guntse furucinsa had'e da sakin murmushi kad'an ya ce "Afuwa uwargida ya d'an shiga busy ne a office shi yasa ba ki gan shi ba." Nanna ta saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa kafin ta ce "Ko da na ji, ai shikkenan ku wuce mu je gida kuma tun d'azu fa nake kiran wayarsa ta k'i shiga."
Musty ya d'an saki murmushin sa kafin ya ce "aikin da yake yi ne mai mahimmancin gaske ne shi yasa ba ki gan shi ba." Ta d'an tab'e baki ta ce "Allah ya taimaka ka gaisa min da madam." Ya d'aga kai yana fisgar motar sa da sauri zuciyarsa fal da tunanin yarda za'a kark'e da wannan aure na abokinsa da kai tsaye zai iya kiransa auren Drama. Ya saki murmushi yana jijjiga kai tabbas Hammad akwai k'wallan shege. Ko da ya kira wayarsa still a kashe take.__________________
Sai magriba sannan ya fara shirin tafiya gida. Bayan wuni da yayi yana jigilar ta da jinyarta da gaske ya lura Hamda raki ne da ita na gasken gaske. Gaba d'aya ta bi ta narke masa. Yanzun ma tana zaune tana ganin yarda yake shiryawa ya d'au kayan da ya zo da su ya mayar jikinsa sannan ya zauna a gefenta yana mata kallon k'asan ido murmurshi fal fuskarsa. Gefen kumatun ta ya shafa kafin ya ce "Nuri ta zan tafi. Gobe ki shirya da wuri za muje shopping kin ga saura 4 days azimi. Duk dama ina tunanin kafin sallah zamu wuce gida don Gwaggo Asma ta matsa sai na koma." Shiru ta yi masa tana cono bakinta alamar zuciyar a kusa take. Ya matso da ita jikinsa sosai yana k'ok'arin lalubo k'wayar idanunta da ta runtse cikin muryar shagwab'a ta ce "Ni tsoro nake ji." Ya bud'e ido yana kallonta sosai cikin mamaki da ganin hawaye na malala a fuskarta. Ya sa hannu ya share mata hawayen saman fuskarta yana mamakin rigimarta "Yanzu me kike son ayi? su nan garin fa ba su da aljannu balle ki ce tsoro kike ji ba abinda zai sameki fa." Turo baki tayi kawai ta mik'e ta shige d'aki zuciyarta a tunzire gani take bai damu da ita ba, idan banda haka ta ya zai tsallake ya bar ta a condition d'in da take, don kawai ba ya son b'acin ran matarsa.
Ya dad'e rik'e da kansa kafin ya mik'e yabi bayanta waya a kunne yana neman layin Nanna. A karo na farko Hamda zata saka shi yiwa matarsa k'arya. Kafin ya shiga bedroom d'in Nanna ta d'au wayar ranta a b'ace ta ce "Yanzu Dear ina ka shige tun fitar safe?" Ya saki ajiyar numfashi kafin ya ce "Nanna am sorry aiyuka ne suka rincab'emin sai da asuba Zan dawo please take care ki rufe gidan." Kafin ta ce komai ya katse wayar ya kasheta gaba d'aya sannan ya shiga d'akin a zuciyarsa ya ce "Bari naje na ga Danger sam bai San yarinyar nan itama y'ar rigima bace sai yanzu.
A zaune a gefen gadon ya sameta fuskarta a had'e sosai da alama ma hawaye ta gama sharewa.
Yana murmushi ya k'arasa kusa da ita kafin ya zauna a gefenta yana zuba hannayensa cikin tattausan hannunta "Shikkenan hankalinki ya kwanta ba zan tafi ba sai da sassafe."
Ji tayi abinda ya tsaya mata a k'irji ya fad'a mata ta d'ago tana haske fuskarsa da murmushi ya lakace mata hanci had'e da jan hancin "Rigima idan ban da son kai haka kawai ki yiwa mata fashin mijinta, yanzu yau ya kike so ta yi bayan mun saba kwana gado d'aya." Wani kallo da ta watso masa ne ya saka shi sakin dariyar da bai shirya ba Ya dafe k'irjinta yana fad'in "Zuciyar ta kwanta kishi ko? Ashe ana so na?" Ta lumshe idanunta kawai tana ture hannayensa "Ana so ana kaiwa kasuwa ai tunda kika ce sai na kwana yau kuwa zaki fanshi Nanna duk wani abinda take min kema sai kin yi min shi. Wanka kafin na kwanta ta kuma shayar da ni tea da bakinta." Da sauri ta waro ido wata matsananciyar kunya na kamata ta ce "Ni fa ba don haka na ce ka kwana ba tsoro nake ji." Murmushi kawai ya saki yana janta tsaye tana tattale k'afa da kyar taje tafiya tsaf ya sunkuceta "Yarinya idan ma za ki mik'e ki mik'e yau mai till down ce." Ta runtse idonta jin lab'b'ansa a saman nata.______________________
Ammi hankali tashe take kallon malamin da suke zube a gabansa kafin ta ce "Malam ban gane ka yi iya yinka asiri ya k'i shiga jikinsa ba?" Fuskarsa a d'aure ya ce "Hakan da na gaya miki shine gaskiya kuma duk wanda ya ce zai sake miki asiri akan yaronnan ya ci shi k'arya yake yanzu jikinsa a tsare yake kuma kullum sai ya yi azkar bana haufi akan haka.don duk aljannin da na tura jikinsa a k'one yake dawo min." Sakina da Kady suka runtse idanunsu cikin tashin hankali suka mik'e. ko sallama ba su yi masa ba suka fice.
Ko a mota maganar da suka dinga yi kenan, Sakina ta ciji yatsa ta ce "Ga shi gari ba kusa ba balle mu k'addamar masa ina ga Didin kawai za mu aika da ita lahira don ni dai itace matsalata." Kady girgiza kai kawai ta tabbatar mata hakan shine maslaha. "Ki nemi guba mai k'arfi ko ta shak'awa ce a saka mata a turaren wuta ta shak'a ta margaya." Suka tuntsire da dariya had'e da tafawa don suna hango alamun nasara a tare da hakan. Kady ta saki dafa ta kafin ta ce "K'awata kafin hakan ya faru sai kin san yarda kika yi kika had'a gagarimin tashin hankali tsakanin Asma'u da Umar don na lura itace matsalarmu." Sakina ta girgiza kai tabbas ta yarda da Zancen k'awarta tabbas Asma'u ita ce matsalarta a wannan tafiyar. Ta shiga tunanin irin makircin da zata k'ulla mata. Murmushin mugunta ta saki tana dafa kafad'ar Kady "In dai wannan ce ki bar ni da ita a darennan Ba sai gobe ba zan yi maganinta. Ba dai yau girki na ba sai na zautashi na rikita masa kwanya na gigitasshi kafin na wuntsilo masa da maganar Shegiyar." Dariya sosai suka saka har suna sake tafawa Kady ta ce "K'awata ai na san ki ta wannan fannin ba sauk'i kina ragargazar y'an mazan. Na rasa wace irin baiwa Allah ya baki da har yau ba ki fara salamcewa ba." Sakina ta yi murmushi kawai kafin ta yi reverse da mota tana fad'in "Shima gogan kullum zancensa Kenan kullum kamar sabuwa nake dal a leda."
Haka dai suka yi ta hirarsu da makircinsu kafin su isa gida.Asma'u ta samu Sadiya a d'akinta. Ta mik'a mata wayar hannunta bayan ta danna recording d'in da ta d'auki su Sakina kaf hirarsu ta d'azu ta fito a cikin wayar. Tsananin mamaki da frigici ya kama Mahmah ta kalli Asma'u kafin ta ce "Yanzu Umman yara shaid'anancin Sakina har ya kai haka? Ita ta rufewa Didi baki fa na ji tace." Asma'u ta girgiza kai "Sharrin Sakina ya zarce hakan, kada ki gayawa kowa lokaci kawai nake jira da zan bayyanawa duniya wacece Sakina? Ki kuma tursasa Hammad ya dawo a yi mai gaba d'aya. Yanzu dai kin tabbatar da cewa k'arya take Hamda ba jinin Hammad bace?" Sadiya ta girgiza kai cikin jinjina girman lamarin ta ce "Tabbas! Idan kuwa haka ne ya zama dole d'anki ya dawo nan kwana kusa ya dawo mata da shegiyar y'arta da ta nanik'a masa ta je can ta nemi Ubanta. Ranar zan ga Abbu da wani ido zai kalleni bayan ya gama tozarta ni a idon matar nan duk abinda na yi ban iya ba Sakina ce ta iya. Sau tari ya sha kira na da Sakina madadin Sadiya. Shimfid'ar aure kuwa tuni na sallama mata don ko na kai kaina raina ne yake b'aci. Abincina sai ya ga dama yake ci. Akwai ranar da fa cikin dare ya buk'aci na siyar masa da kwana na ya je ya tara da Sakina wallahi Asma'u ranar kukan jini ne kawai ban yi ba sabida bak'in ciki. Shekara da shekaru fa bak'in ciki da nake fuskanta kenan." Hawaye ne kawai yake malala a idanunta alamar abin yana mata ciwo sosai. Asma'u jikinta ya yi sanyi da jin wannan babbar lamarin tabbas sun san d'an Uwansu baya adalci a tsakanin matansa amma sam bata san lamarin ya ta'azzara har haka ba. Ta jinjinawa hak'uri irin na Sadiya da tarin kawaicinta tsawon shekaru tana k'unshe da wannan bak'in cikin tana danneshi a ranta. Tabbas ta cancanci lambar yabo. Kasa ce mata komai ta yi illa kama hannunta da ta yi ta manna mata wayar da Kiran Hammad ya shigo alamar ya ji Kiran da suka yi masa bai d'aga ba ya biyota. Muryar Sadiyar a dashe ta ce "Hello Hammad kana ji na?" Da sauri Hammad ya amsa da "Eh Mahmah ina jin ki, ya na ji kamar kuka ki ke lafiya dai ko?" Ta ja ajiyar zuciya kafin ta ce "Ya Zama dole gareka ka bi umarnina in dai ni na durk'usa na haifeka ka tattaro ka taho Nigeria a satin nan. Kuma taho musu da shegiyar y'ar su idan kuma ka k'i ina tabbatar maka ba ni ba kai." Ta kashe wayar bayan ta kalli Asma'u Tana murmushi ta ce "Ummansu idan ba haka na yi masa ba ba zai zo ba, yanzu kuwa na tabbata hakan da na yi masa zai saka shi ba shiri ya taho." Asma'u ta girgiza kai ta ce hakan ya yi.
Shi kuwa Hammad kasak'e ya yi da wayar a hannunsa yana shafa kan Hamda da ta dage sai ya sata ta yi barci kafin ya fice bayan sun yi sallahr asuba. Tana jinsa tayi lamo a jikinsa sam rabuwa ce bata son yi da shi. Tana son jinta a jikinsa manne da juna musamman Idan yana shafata sai ta ji ta a wata duniyar da bata fatan abinda zai raba su. Ta sake juyi a jikinsa ta na d'an bud'e idonta a kansa ya sakar mata murmushi "Bari muje na yi mana booking flight zuwa nan da nextweek za mu tafi Nigeria Mahmah ta matsa." Sosai ta ware idonta a kansa har hakan ya saka shi kaiwa idon sumbata murya a sark'afe ya ce "Ki daina min wannan kallon Idan Ba so ki ke ta karb'i hak'kina ba ga tsoro ga neman magana." Ta turo bakinta tana juya masa baya. Murmushi ya sakar mata a wuya yana mik'ewa da sauri ya fice daga d'akin don idan ya biye ta tata sai yara su yi late a school.
Ita kuwa Hamda gabanta ne yake fad'uwa tsoronta d'aya kada suje Nigeria a raba su. Don tana jin sanda Mahmah ta kirata da shegiya! Shi yasa k'irjinta ya yi nauyi ta fara jin tsoro a ranta. Sam bata tunanin zata iya sake rayuwa a duniya ba tare da Hammad mahad'in zuciya da gangar jikinta ba. Musamman a yanzu da suka zauna na kwana biyun ta tabbatar da shi a matsayin lafiyayyen namiji abin alfaharin kowacce mace. Dama can a mafarki shine burinta balle yanzu da ya shayar da ita zumar k'auna ya lula da ita duniyar dad'i a zahirance. Ba ta jin akwai mahaluk'in da zai raba su.
To fa! Idan Mahmah ta zafafa fa? Ya za ki yi Hamda?
VOUS LISEZ
Ya Abin Yake?
Fiction généraleUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.