LET'S FEED THE NEEDY with chef keeno's corner (RAMADAN 2023)
Prophet Muhammad (S.A.W)Also said, O people!one who gives IFTAAR to a fasting person during this month (Ramadan) will be like one who has freed someone and his past sins will be forgiven.
Me kuke jira Yan ,uwa ? Munaji muna gani wannan dama bazata wucemu ba, Ina masu neman ladan da bashi da iyaka ku tawo mu hada karfi da karfe mu samu wannan gwaggwaban ladan baki daya.
Ina wadda keson yin sadakar abunci Amma Bata da halinyi ita kadai, matso kusa Yar uwa mu hada hannu muyi mu samu ladan duka.
Shin nawa muke kashewa a siyan Data a wayoyinmu duk wata? Kuzo mu hada Kai mu Yi abun da zai fishshemu ranar gobe kiyama Yan uwa.
Insha Allah zamu fara Tara kudi kamar yadda muka Saba duk shekara, farawa daga karshen November nan zuwa lokacin azumi .
Kamar yadda kuka sani muna saka 500 duk karshen wata zuwa abun da mutum yaga zai iya sawa ,Amma duba da yanayin da muke ciki na tsadar abubuwan rayuwa mun Mai dashi duk karshen wata 1k zuwa abunda mutum yai niya in kana da karfin saka dubu Dari ma munaso , Allah ya bamu iko
Insha Allah Kuma za,a ringa dafa wannan abun sadaka a karkashin kitchen Dina na keeno's corner catering services kamar yadda aka Saba, ba Kuma ko kwandala za,a biyani na dafawa ba kawai burina mu Hadu mu samu ladan duka.
Allah ya horewa kowa ya hadamu a ladan baki daya sadaka sai an daure anyi yaki da shaidan Yan uwana.👏🏻
🌙 account no da za,a ringa saka sadakar : 0002078540
Account name: sakina Dandawaki Aminu jaiz bank👉🏻Akwai group inda Mai bukatar shiga , yadda kowa zaiga irin abun da mukeyi ,Kuma da lokaci yayi za,a ringa tunasarwa , inda Mai bukatar shiga sai a tuntubemu ta wannan wayar : 08066154995
Or 08033748387
08062727464JAZAKUMULLAHU BIL JANNAH👏🏻
****************************
Zufa ce gaba d'aya ta jik'eta, tun kafin ta ji ainahin zancen, duk da in dai kunnuwanta sun ji daidai bata buk'atar k'arin bayani ko kad'an. A razane bata San sanda ita kanta ta murd'a mabud'in d'akin ba ta bur ma kanta ciki ba tare da neman izini ba.
Yanayin kallon da take jifansu da shi ya tabbatar musu ta ji abinda suka ce, tashin hankali ya bayyana b'aro-b'aro akan fuskokinsa, shi tunanin da yake daban itama Nanna nata tunanin daban, duk da ko ji Mahmahn ta yi ba zai zama laifinta ba tunda ba kai tsaya ta je ta sameta da maganar ba, balle alk'awarinsa na sakinta da zarar wani ya ji zancen ya tabbata.
Yarda suke kallonta a tsorace haka itama take kallonsu, kafin cikin dakiyar murya ta ce "Wace magana na ji kuna yi? Ina son jin gaskiyar zance don samun akasin hakan daga bakunan ku yana nufin bayyana muku asalin wacece ni, don tsaf Zan cire duk wani abu a raina na ci mutuncinku, Kamla y'ar waye? Da ta zama ba y'arku ba?" Bugun da zuciyarsa yake yi ya k'ara tsananta, don bai so lamarin ya zo masa a gicciye haka, ya yi alk'awarin b'oye Sirrin har lokacin da gaskiya zata yi halinta. K'asa ya yi da kansa yana cigaba da sauraran bugun da k'irjinsa yake yi, idanun Mahmah a yau sun masa kwarjinin da ya kasa kallonta kai tsaye ya furta mata abinda yake zuciyarsa wa zai ce mata itace Uwar Kamla idan shi ya zama ubanta?
Kasa furta ko kalmar 'A' ya yi ga tarin mamakinsa yau duk tsaurin idanunsa ya kasa fitar da maganar da ta zamo sirri mai girma a gareshi.
Har a lokacin idanun Mahmahn yawo suke yi a jikinsa cike da mamakin yarda ya k'i ya kalli ko inda take, balle ya kalli cikin k'wayar idanunta wanda idanun takewa duk y'ay'anta tarko idan ta na son jin gaskiyarsu, ta tabbatar shi yasa kai tsaye ya k'i kallonta. Kai tsaye ta mayar da kallonta kan Nanna da ta takure guri guda, duk da ita kanta tana masa barazanar tonuwar sirrin amma iya kan fatar bakinta kawai yake ba wai har zuciyarta ba, ba burinta fallasuwar sirrin ba don tana son Kamla tana kuma jin ta kamar su Khairi da ta tsuguna ta haifa bata sani ba ko don kasancewar Kamlan ta sha nononta ne, shi yasa take mata wata iriyar zazzafar k'auna. Ta sake k'asa da kanta tana nadamar tashin tashinar maganar da ta yi har tasa Mahmah ta jiyo zancen a ranta ta furta 'Tsautsayi' da kuma ba mamakin Allah ne ya so bayyana sirrin da suke b'oyewa da ko su Khairi ba su sani ba. Jin maganar Mahmah ta yi kamar dirar aradu "Tunda shi ya k'i gaya min, ke idan ba ki raina ni ba, gaya min wacece Kamla?" Karan farko da Nanna taji matsanancin tsoron Mahmahn ya dirar mata, sam bata san hakan Mahmahn take da kwarjini ba sai yau da ta tsatstsareta da idanunta fuskarta a had'e babu alamar wasa a lamarin Mahmahn. Tsawar da Mahmahn ta daka mata ya sata firgita, jikinta na rawa ta dinga kallon Mahmahn "Zaki fad'a ko ba zaki fad'a ba sai na tara muku jama'a?" Hannunta ta dinga yamutsawa cikin d'aya hannun, zufa na kwarara mata daga jiki, murya na rawa cikin wata irin Ininar da bata san da ta fara ta ba ta ce "Zan fad'a Mahmah." Mahmah ta gyara tsayuwa kafin tace "Ina jinki." Kujere Nanna ta ja mata ta nuna mata da son ta zauna, duk da ba ta jin tana son zaman ba hakan ta zauna still idanunta cikin na Nannan. "Mahmah zan fad'i iya abinda na sani, wallahi gaskiyata zan fad'a miki. Bana manta wata ranar alhamis da daddare har mun kwanta na ji wayar Abban Khairi tana kira, na d'aga ina mik'a masa ganin numberr garin da muke ce wato Birmingham da barci a idanunsa kawai na ji yana cewa "Alhamdulillah, masha Allah ta haihu? Shikkenan gani nan." Da sauri ya mik'e ni kuwa tsammani na d'aya daga cikin matan abokansa ce ta haihu yasa na ce masa wacece ta haihu? Girgiza min kai ya yi kafin yace "Ina zuwa, idan na dawo zaki ga ko wacece duk da baki santa ba." Daga haka ya yi saurin ficewa a gaggauce kamar ya fad'i. Mamaki ya kamani da tunanin wacece a garin wacce ba santa ba, sai kuma na tab'e baki na mayar da kaina barci ya sake kwasheni.
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.