Fuskarsa a d'aure ya cigaba da jifan Nanna da kallo, ya tabbata ita take sake saka Mahmah a wannan hanayar da ya tabbatar ba ta d'abi'antu da ita ba. Takaici ya sake kumeshi ganin yarda Mahmahn ta kafe Hamda da kallo. Ya k'arasa gefen gadon idanunsa na kan Mahmahn da buk'atar ta tausayawa Hamdan. Bata kalleshi ba, balle ya saka ran zata amshi buk'atarsa. "Ki tabbata da zarar an sallameki, kin dangana da d'akin uwarki, shine kawai kwanciyar hankalinki, Bana buk'atar sake ganinki da shi. Ki na jina?" Mahmah ta fad'a cikin kausasawa muryarta da gask is babu wannan tausayin da jin k'ai da take wa Hamda a lokutan baya.
Hawaye ne kawai ya shiga zubo mata, hankakinta a tashe ji take kamar ta zunduma ihu, zata iya jure komai amma banda rabuwarta da Hammad. Me yasa a koda yaushe take gamuwa da tarin matsaloline daga wannan sai wannan? A zuciyarta ta shiga Kiran sunayen Allah dafatan ya kawo mata d'auki a dukkan lamarinta.
Hammad shima ji ya yi, kamar ya saka kukan, ya dinga jin zuciyarsa na buga wani sauti da ya tabbatar na zallar tashin hankali ne, tabbas uwa uwace, da wani ne ya yi masa wannan abin da ya ji amsa daidai da abinda ya aikata. Jikinsa a sanyaye ya kama hannun mahaifiyarsa, murya a tausashae yake son lallai sai ya fahimtar da ita. "Please Mahmah, ki yi hak'uri ki bari ta samu lafiya, me yasa ki ke k'in Hamda alhali da ubanta ba shegiya ba ce." "Kai ka san ubanta, ni ban san shi ba bata da banbanci da shegiya a wajena. Cutar da uwarta tayi min a rayuwa shi yasa ba zan amince na gwamutsa zuri'ata da tata ba, ina tabbatar maka zaman aure da kai da Hamda ka k'addara ya haramta a tsakaninku. K'in bin umarni na kuwa yana nufin zartar da duk hukuncin da naga dama." Daga haka ta fice da sauri kamar ta tashi sama. Ta nufi d'akin da Abbu yake. Asma'u ce dama ta kirata tana mata fad'an bata kyauta ba, da bata zo ta duba Abbun ba, kuma Didi tana ta fad'a. Hakan yasa ta taho ba shiri duk da dare ya tsala, kuma ita ta tambayi Hameed yarda Hammad yake ya nuna mata d'akin shine suka taho da Nanna.
Tana ganin sun fita ta rik'e kanta da take jin jiri kawai ta saka kuka, wannan karan Hammad kasa lallashinta ya yi don ya tabbatar kukan shine abinda zata yi ta ji sanyi, kuma ko bakomai lamarin ya kai a zubar masa da hawaye. Ya zauna a gefen gadon kawai tare da mannata da jikinsa, duk da k'ok'arin k'wacewa da ta yi ya kasa bata damar hakan, shi kansa a lokacin dauriya kawai yake amma yana jin kamar ya tayata zubar da hawaye, dole ne ma ya yi maganin Nanna ta hanyar da bata zata ba don ya tabbata ita take sake ingiza masa uwa.
Abbu da kyar ya bud'e idanunsa da ya ji sun masa nauyi, fatansa da burinsa duka lamarin ya zama mafarki. Amma ganinsu kewaye da shi ya tabbatar masa ba mafarki bane zahiri ne duk abinda yake faruwar. Kewaye mutanen d'akin ya yi da idanunsa yana amsa musu sannun da suke masa. Idanunsa ya sauka cikin na Sakna da duk take a firgice. A karo na farko a rayuwa ya ji tsanarta da tarin haushinta ya saukar masa a zuciya, duk da shima da laifinsa me yasa bai fito ya sanar da duniya sun rabu ba, ya biye tata suka aikata son zuciya. Runtse idanunsa ya sake yi ba tare da ya sake mata kallo na biyu ba, yana son Sakna sosai kuma har a lokacin bai Ji son nata ya ragu a zuciyarsa ba sai da ya had'u ya cakud'e da k'iyayyarta da kuma jin haushinta duk lokaci guda.
Hamdala duk d'akin aka shiga yi, tare dafatan k'arin lafiya a gareshi. Dama tun safe suka sake dawowa duba shi, ganin har lokacin bai farka ba hankalinsu yake a tashe.
Da d'aid'aya suka dinga ficewa jin Gadanga ya ce "Yakamata mu bawa matansa waje su gyara shi, tunda hannayensa sun d'an yi nauyi kuma ina da tabbacin zai buk'aci shiga toilet." Didi ta ja tsaki kafin ta ce "Kai dai Gadanga da tsiya ka ke wallahi, matansa su gyara shi ko matarsa? Ai Yanzu ba shi da wata mata da ta ta wuce Tadiya." Tsit Abbu ya yi akan gadon yana sauraran furucin Didi. Shi akan kansa yana buk'atar sakin Sakna amma bakinsa ya yi nauyi wajen furta furucin. Yana jiyo shashshek'ar kukan Saknan hankalinta tashe, Didi tana iza k'eyarta zuwa waje "Wallahi sai kin fita, haba a yi mace mayya tun dare bake korarki kin k'i tafiya ko y'arki ba ki je kin gani ba, to ko tale aka halicceku da Umalu sai na rabaku wallahi." Tana turata k'ofar ta ja da k'arfi ta datseta.
Gadanga ransa a b'ace yake kallon Didi kafin ya ce "Amma fa hakan bai dace ba Didi, tunda dai shi Yayan ba ki ji ya ce miki ya saketa ba, yanzu wa kike so ya raka shi toilet ya gyara jikinsa?" "Tadiya ce zata lakashi ai Umalun ba lasa k'afa ya yi ba, ka ga Gadanga ka fita idona na lufe." Gadanga ya rik'e kansa idanunsa cikin na Yayansa da ya hango yarda zuciyarsa take bugu da sauri da sauri. Da kansa ya taimakawa Sadiya suka saka shi a toilet sannan ya fice ya bar Sadiyan, tana tsaye ta b'ata rai ta kuma kasa yiwa Abbun komai sai kallon jin haushi take wurga masa. Abbun ya d'ago muryarsa a k'asa sosai ya ce "Idan ba zaki iya ba, Ai gwara ki kirawo wanda zai yi, kin barni sanyi yana dukana." Sai sannan ta lura da rawar sanyin da yake. Hakan yasa ta d'au towel d'in ta fara shirin tsaftace masa jiki ba nuna tausayawa bakomai balle kwantar masa da hankali, wanda a condition d'in da yake bai kamata ace ta nuna masa b'acin ran ba, ta yarda Sakna ta yi mata fintink'au kenan.**********
Idanunsa a lumshe hannayensa zube bisa k'uncinsa ya yi nisa cikin tunanin da yake, yayinda Hamda take barcinta peacefully bayan ya taimaka mata ta yi wanka. Da gaske lamarin Mahmah yana tab'a zuciyarsa ya rasa ta yarda zai b'ullowa lamarin.
Turo k'ofar da Umma Asma ta yi, shi ya farkar da shi daga zuzzurfan tunanin da ya tafi. Sai dai tana ganinsa ta san tunani yake. Da murmushi a fuskarta ta ce "Sannu Hammad, mun bar ka da jinya,
Sai yanzu hankulanmu suka kwanta Yaya ya farka da lafiyarsa sai dai hannunsa da k'irjinsa da suka yi masa nauyi." Hammad ya ja ajiyar zuciya yana gyara zamansa, cike da k'warin gwiwa da jarumtar da ya arowa kansa ya gaisheta. Ta yi tsam da ranta tana sake karantar yanayinsa kafin ta ce "Me ya faru ne? Na ganka a wannan yanayin?" Nutsuwa ya yi sosai kafin ya sanar da ita abinda Mahmah ta ce, kafin ya gama tuni duk wani annurin fuskarta ya b'ace b'at, mamakin sauyin Sadiyar take yi, matar da aka santa da kyawawan halaye ta yaya lokaci guda ta rikid'e ta koma haka? Ta ja ajiyar numfashi kafin ta dafa shi "Ka kwantar da hankalinka Hammad, babu abinda zai faru insha Allah, amma a yanzu dai Kada a tursasa mata ta zo tana maka furuci mara kyau, ka bar Hamdan a wajen Didi kafin komai ya lafa, don na san uwarta ba zata rik'e ta ba, tunda har yanzu ma bata zo dubata ba, ka barta a wajen Didi na san ta yarda Zan b'ullowa Didin insha Allah ba za'a samu matsala ba." Ya amince da shawararta ba don zuciyarsa ta so ba, sai don sanin cewa a yanzu hakan shine mafita a gareshi da Hamdan ma gaba d'aya, takaicinsa d'aya yarda Zai yi kewar Hamdan kafin komai ya lafa. Daga haka ya mik'e ya je duba Abbu ya bar Umma Asma tare da Hamdan da take sauraransu kamar mai barci Sai dai tun shigowar Umman ta su ta farka daga barcin kuma komai suka fad'a a cikin kunnenta. Ina ma Allah Zai bayyana mata ubanta da duk talaucinsa ta bi shi garinsu ta huta da yarda ake ta walagigi da rayuwarta.____________
Cikin masifa da gadara ta zube idanunta cikin nata, ranta a matuk'ar b'ace take sake jifansa da duk kalaman da suka zo saman harshenta. Da gaske haushinsa take ji sosai tun bayan da ya bayyana Hamda a matsayin matarsa. Kasancewarta mai Tsananin kishi ya sa take sake bayyana haukanta tuburan, yana zaune yana kallonta cike da takaicin rashin mutuncin da take zuba masa "Wallahi dole ka saketa, idan kuma ka k'i sai na bayyanawa duniya Kamla ba y'ata bace a can waje ka je ka yi cikinta ka kawo min ita a ranar da aka haifeta tare da kafa min sharad'in da ka San dole ba Zan k'etare shi ba, ka ce lallai sai na rik'eta na kuma sanar da duniya ni na haifeta idan ba haka ba a bakacin aure na, don haka a yau nake son sanar da ni wacece Kamla?" Idanunsa a firgice ya d'ago yana watsa mata wani banzan kallo...
Jikar Nashe ce.✍🏽✍🏽📄
❤️❤️❤️❤️❤️🙏
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.