13

582 17 1
                                    

Alk'alamin Jikar Nashe

YA ABIN YAKE?

https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e

Follow me on ArewaBooks

@nazeefah

On Wattpad @Nazeefah381

13

✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽

Kamar an farkar da Abbu cikin daren, akan idonsa Samudawan suka shiga sashen Hammad d'in bayan sun sumar da masu gadi har biyu da suke bakin gate d'in.

Hankalinsa a tashe ya kira y'an sanda kafin cikin sand'a ya nufi part d'in su Hammad d'in yana bin bango, akan kuma kunnensa suka yi wannan furucin, da yayi barazanar hargitsa kayan cikinsa. Addu'a ya shiga yi akan Allah ya kawo police d'in da wuri.

Cikin hukuncin Ubangiji duk da dukan da suka yiwa Hammad d'in bai yarda ya sha k'wayar da suke tura masa a baki yana furzarwa ba.

Ance Sarkin yawa yafi sarkin k'arfi, don haka kafin kace me tuni sun wahalar da shi, duk da ya kafe akan k'in shan maganin.

A lokacin ne kuma y'an sandan suka bayyana cike da k'warin gwiwa suka danna kai sashen bisa jagorancin Abbu.

K'ok'arin gudun da suke ne yasa police d'in danna musu harbi a k'afafunsu, sun yi nasarar kama mutum biyu, yayinda uku suka tsere.

Ba wani b'ata lokaci suka gark'ame su da ankwa, a kuma lokacin ne mutanen gidan k'arar harbin bindiga ya farkar da su, Dama Didi da Hamda ba barci suke ba, a razane suka fito duka d'aukacin jama'ar gidan suka nufi inda suke jiyo harbin.

Cikin tashin hankali Didi take kiran sunan Hammad "Ubangiji Allah kasa ba su kashe min jika na ba"
Ta fad'a idanunta akan Hammad d'in da yake kwance magashiyyan Abbu yana k'ok'arin d'aukansa don su kaishi asibiti amma ya kasa, ga shi gidan ba maza duk suna gidajensu shi kuma Hamood yana makaranta.

Mahmah kuwa kuka kawai take ta kasa katab'us, sai Ammi ce cike da kissa ta kama k'afafun Hammad d'in suka kinkimeshi da Abbu don zuwa asibiti, hankalinta a tashe don bata san mai zai je ya dawo ba idan Hammad d'in ya farfad'o, ba mamaki a take a wajen ya tona mata asiri, da ta sani bata bi gurguwar shawarar kady ba gashi ta kaita ta baro. Dole ta nemi mafita a gaggauce kuwa kafin wankin hula ya kaita dare.

Bugun da suka yi masa a baya da gefen muk'amik'insa shine yake masa ciwo sosai sai kuma dukan da suka yi masa a kai da yayi sanadiyyar sumansa. Haka likitan yayi musu bayani kafin suyi masa allurai aka kuma jona masa drip barci mai nauyi ya d'aukeshi.

Dole Abbu da Didi ne suka kwana a asibitin don Sadiya bata zo ba bata son surutun Didi, shi yasa tayi zamanta a gida, Ammi ta so zama amma Didi ta ce a sabida me? Don kalan dangi, to ki fita idona wannan ba huruminki bane me kika had'a dashi? Banda auren ubansa da kika yi, maza-maza ki tattara komatsanki kiyi can wajen samudawan y'an matanki da
Kika ajiye kina adon d'aki da su."

Ranta a tunzire ta tafi, dama taso zama ne ko ta samu mafita, wannan karan yarda take jin zuciyarta da tsoron tonuwar sirrinta, tana tunanin da kanta ma zata iya kawar da Hammad idan ta samu faraga sai gashi tsohuwa Didi tayi mata kanda garki, ta hanata sakat don haka jikinta a salub'e ta tafi, had'e da aniyar sake wani shirin ko da na zuba masa guba a abinci ne, sai dai tana tsoron a kamata, don haka zuciyarta ta amince da shawara d'aya da zata zartar da ita da zarar ya warke ya koma gida.

____________________________________

Da sassafe Hamda ta gama duk wasu aiyakunta, har peppe soup da sinasir tayiwa su Didi da zummar idan tayiwa yaran wanka su tafi gaba d'aya su duba Babansu.

Ya Abin Yake?Where stories live. Discover now