31

312 4 0
                                    

"Me ka dawo yi Cikin zuri'ata bayan tuni na zareka daga cikinta.." Tuni kowa ya d'ago ana kallon Abbu fuskar kowa b'aro-b'aro da mamakin furucinsa musamman wad'anda ba su san zancenba don ba kowa bane ya sani a cikin family daga Abbun sai Ammi Didi da Mahmah. Sai kuma Asma'u Sadiya da Gadanga sai ahalin Hammad. In ban da su babu wanda ya San wannan badak'alar da take faruwa a dangin. "Ka fice min daga gida kafin na yi mai gaba d'aya na tsine maka." "Ta tabbata da a yi tsinanannu biyu a zuli'alku don kana tine mata ni ma don tine maka." Didi ta fad's fuskarta taf da jin haushin furucin Ummaru "Kai Umalu na lula baka tan zulu ba, to bali nima na fito maka a mutum kamar yalda kake so. Idan banda shashashanci an tab'a yanke shari'a ba a ji ta bakin mutum biyu duka ba. Wato ita ce mai gaskiya da ba zata fad'I k'alya ba." Ta nuna musu wajen zama. Hammad ya zauna ransa a had'e kowa ya zuba masa ido. Suma su Hamdan suka zauna Didi ta sa aka zuba musu abinci. Hamda kuwa ta samu abincin ta fara ci sosai don abincin ya yi Mata. Sinasir ne da miyar taushe da ta ji naman rago da kabewa.

Ammi kuwa gaba d'aya zufa ta ke duk da sanyin a'cn da yake kwarara a falon. Da gaske a tsorace take ga shi kanta ya k'ulle ta rasa ma tunanin da zata yi. Duk addu'ar da tazo bakinta take ja. Tabbas Hammad ya shammaceta a lokacin da ta manta da waccan matsalar sai ga shi ya dawo mata da ita bagatatan. Ta runtse ido ji take a lokacin notunan kanta suna shirin kuncewa saboda matsanancin tunani da ta zurfafa.

Kowa ya yi tsit baka jin k'arar komai sai ta cokula. Zuciyar Sadiya Asma'u da Lauratu yau fes ranar da suka dad'e suna jira yau gata tazo. Hammad abincinsa yake ci cike da nutsuwa duk da kallon banzan da Abbu yake zabga masa bai damu ba sai ma sakin murmushin k'asan kumatu yake yau zan shayar da Abbu ruwan mamaki shine abinda yake ayyanawa a ransa. Kuma dalilin murmurshin nasa kenan.

Sai da kowa ya yi nak, ga wanda suka ci abincin fa kenan sannan Didi ta juya ta kalli Hammad da yake fad'in Alhamdulillah bayan ya saki gyatsa ta ce "Hammad ya bayan saduwa? Ya kuma aka ji da wannan abu da ya falu?" Ya gyara zamansa a k'asan daddumar kafin ya ce "Bayan saduwa sai Hamdala abubuwan alheri da dama sun faru Hajiya Didi ciki kuwa har da aurena da Hamda."

D'aukacin mutanen da suke falon ba wanda gabansa bai fad'i ba da jin furucin Hammad da ya zo musu bagatatan. Harta Didi sai da ta runtse idonta ta bud'e sannan ta tabbatar abinda take ji ba mafarki ba ne. Shi da Hamda da suka san lamarin ne kawai babu alamar gigita a fuskarsu. Amma d'aukacin mutanen da suke falon idanunsa a waje yake alamar firgici da razani a tatttare da su. Tunaninsu d'aya ne tabbas Hammad ya samu tab'in kwanya idan banda haka ta yaya zai ce wai ya auri k'anwarsa da suke uba d'aya.

Nanna kuwa suman zaune ta yi tana jifan Hammad d'in da wani irin kallo. Ita dai gata nan a zaune ita ba sumammiya ba ita ba farkakkiya ba.

K'arar marin da Gadanga ya zube a k'uncin Hammad ne ya dawo da su suman wuncin gadin da suka yi. Idanunsu akan Hammad da ya rik'e kumatunsa yana jifan gadanga da wani irin kallo da murmushin takaici murya a shak'e ya ce "Me yasa zaka mareni?" Gadanga cikin zafin rai ya ce "Marinka na yi saboda ka dawo cikin nutsuwarka, ka yi mana filla-filla ka sanar damu abinda kake nufi da aurenku da Hamda, tunda ba a garin gab'a-gab'a muke ba. Kuma ko a kafirai ban yi zaton sun yarjewa kansu Auren y'an uwansu da su ke uba d'aya ba."

Hammad ya sake shafa k'uncinsa kafin ya girgiza kansa idanunsa cikin na Hamda da take jin marin da aka yi masa tamkar k'uncinta aka daka. Ya d'an sakar mata murmushi kafin ya ce "Gata nan ku tambayeta da aurena a kanta ko babu? Kuma ta tare a gidana ko a'a?" Da sauri Asma'u ta kama ta "Hamda gaya mana gaskiya shin abinda Hammad yake fad'a gaskiya ne?" Hamda ta yi k'asa da kanta tana d'aga kai alamar gaskiya ne. Jikin Gwaggo Asma'u na b'ari ta ce "Innalillahi wa inna ilaihirraji'una. Tabbas akwai lauje cikin nad'i idan banda haka ta yaya Hammad da iliminsa da komai zai je ya auri k'anwarsa sai kace wanda ya samu tab'in k'wak'walwa." "Tab'in k'wak'walwa na nawa? Ku yanzu ku ka San haka ni tuni dama na sani kuma na tabbatar a cikin rashin hankalin ya je ya haikewa matata ga shi nan yanzu yazo ya sake tafka haukan ta hanyar auren k'anwarsa jininsa ku fice min da shi daga gidannan kafin na yanke hukunci mai muni don wallahi Zan iya sawa a b'atar min da shi." Abbu ya fad'a cikin wata irin murya jikinsa na b'ari hannunsa na rawa yake nuna Gadanga "Fita min da shi Gadanga kafin na kashe shi ku zo kuna da na sani." Daga haka ya zauna idaunsa suna jirkicewa suna canja launi saboda zallar bak'in ciki.

A firgice su Asma'u suke da jin furucin Abbu, suma kenan balle Sadiya da ta ji kanta ya zama kamar dutse hak'oranta sun fara rawa suna kakkafewa tsoro take ji sosai kada zancen Abbu ya tabbata ace Da gaske Hammad ya samu tab'in k'wak'walwa. Idan ban da haka ta yaya zai aikata wannan kwamacalar? Zuciyarta ce kawai take bugu.

Ita kanta Hamda maganar Abbu ta jijjigata, Idan ya kasance hakan ta tabbata ya zata yi da cikin da yake mak'ale a jikinta? Wace amsa zata bawa duniya don gane da tarin tambayoyin da za'a dinga mata. Ta runtse ido ta bud'e tana fatan taji Hammad ya ce wani abu amma bai ce ba, sai murmushi kawai yake yana wa kowa kallon k'asan ido.

Zuciyar kowa dakan uku-uku take. A zafafe Didi da ta gaji da jiran cewar Hammad d'in ta ce "Kai don ubanka ka fito ka yi magana ka wanke kanka, ka bar mutane a cikin duhu ko so kake zuciyoyinmu su buga." Ya d'ago idanunsa cikin na Didi ya girgiza kai yana sakin murmushi kafin ya ce "Ai Abbu ya baku amsa tunda ya ce mahaukaci ne ni. Na yarda ni mahaukacin ne ayi min hukuncin da ya dace da ni musamman ga cikina na nan a jikin Hamda ku min afuwa.." A gigice Mahmah ta zuba masa marika har biyu a duk k'uncinsa. Ya rik'e k'uncin yana kallonta cike da tausayawa halinta da take ciki daga ganinta ka san zuciyarta bata aiki yarda ya kamata. Gani ya yi kawai ta zube a jikinsa tana fad'in "Ka fito ka fad'I gaskiya Hammad kada kasa zuciyata ta buga ka yiwa y'an uwanka asarata..." Muryarta na rawa cikin kuka da gigita take fad'a. Tausayin uwa ne ya ratsa shi ban da ita yau da ya k'yalesu su yi ta d'aukansa a mahaukacin. Ya kama tafukan hannunta ya sanya kansa a ciki kawai ya saki wani mahaukacin kuka da ya hargitsa duk zuk'atan mazauna wajen kada dai Hamda ta ji labari. Gaba d'aya ta yi firgai-firgai da ita.

Tsawon lokaci ya d'ago ya zube idanunsa cikin na Ammi. Wani irin kallo yake mata da yasa kowa ya mayar da hankalinsa kanta. Kallon nasa ne yasa jikinta ya dinga rawa alamun gaskiya ya bayyana b'aro-b'aro a fuskarta tun kafin ya yi magana idanunsa suka fara bata tsoro. Yana murmushi ya nuna ta da yatsa "Ki sanar da su gaskiyar yarda abin yake? Alk'awari na d'aukar miki ba zan gayawa kowa ba. Kuma na cika miki alk'awarinki don haka da bakinki ki sanar da su yarda ABIN YAKE?" Tun kafin ta fara magana wasu suka tabbatar da rashin gaskiyarya zuk'atansu suka fara saukuwa daga b'acin ran da suke ciki. Idanu suka zuba mata suna jiran cewarta. Ammi ta yi k'asa da idanunta tsoro ya cika ta fal, bata san yarda Umar Abbu zai fassara lamarin ba. Bata san kuma da me mutanen wajen za su kalleta ba idan ta gaya musu gaskiyar yarda abin yake. Ta share zufar da ta karyo mata kafin cikin rawar murya ta kalli Abbu ta fara magana....

Jikar Nashe taku ce ✍🏽✍🏽

❤️❤️❤️❤️❤️🙏

Ya Abin Yake?Where stories live. Discover now