23

437 6 0
                                    

Asma'u danne dariyarta ta yi, don ita kanta maganar Didin dariya take bata sai dai ta san da zarar ta yi dariyar yau ba ubanta Utmanu ba har kakanta sai ya sha zagi. Didi ta sake gyara zamanta ta ce "Ki je ki kilasu yau zaki ga futkar almura. Wannan karan Asma'u gagara k'unshe dariyar ta yi sai da ta yi saurin fita daga falon sannan ta saki murmushi.

B'angaren Mahmah ta fara shiga ta sameta zaune bisa sallaya da alama sallah ta idar ta zuba tagumi hannu bibbiyu. Lamarin gidan gaba d'aya ya fara fice mata a kai musamman matsalar mai gidan da bai d'auke ta a bakin komai ba. Ga matsalar Hammad da ya gagara fayyace mata gaskiyar lamari.

Sam bata san da shigowar Asma'un ba da take tsaye ta jera mata sallam ta fi biyar. Har sai da
Ta gaji cikin tausayawa ta k'arasa wajenta had'e da dafa bayanta sannan ta yi firfgitgit ta farko daga dogon tunanin da ta tafi idanunta ta d'ago tana sakin wata nauyayyiyar ajiyar zuciya bayan ta ga Asma'un durk'ushe a gabanta.

Asma'u ji ta yi kamar ta saka kuka ganin irin ramar da Sadiya ta yi a tsukun wannan lokacin "Tunanin me kike yi Sadiya?" Murmushin yak'i ta saki da son danne damuwarta ta girgiza kai "Bakomai" "A'a wallahi zance ne ma ki ce bakomai kin luluk'a can duniyar tunani sannan ki ce min bakomai." Ta fad'a tana jan hannunta cikin son kwantar mata da hankali ta ce "In dai matsalar nan ce ta Hammad ki kwantar da hankalinki ya tsumma a randa, zan iya yi miki rantsuwar da babu kaffara Hammad ba shi da alak'a da Hamda balle har a ce shi ya yi cikinta, haba Allah ba zai jarrabemu da wannan masifar ba, ita dai ta san yarda ta samo cikin d'iyarta." Sadiya ta girgiza kai had'e da share guntuwar k'wallar da ta zubo mata ta ce "Idan ke baki yarda shi ya yi cikin ba ai ragowar mutanen gidan sun yarda. Ji fa yarda ubansa mahaifi ya yi masa korar kare daga gidan nan ba tare da ya tsaya ya ji ta bakinsa ba. Shi kuma ya tsallake ya bar k'asar nan bai damu ya sanar da ni yarda abin yake ba." Asma'u ta girgiza kai ta ce "Duk wannan ya faru ne sakamakon d'aukewar maganar Didi amma yanzu ai komai zai daidaita tunda bakin Didin ya bud'e itace ma ta ce na tattaro mata kanku dukka." Da sauri ta kalleta kafin ta ce "Da gaske?" Tana murmushi ta ce "Ki je idonki ya gane miki." Suka mik'e gaba d'aya ranta fari k'al tana tunanin dukka matsala ta zo k'arshe da izinin Allah tunda bakin Didin ya bud'e.

Ita sashen Didin ta tafi da sauri. Ita kuma Asma'u ta nufi sashen Ammi Sakina. Ta dad'e tana knocking kafin Munira ta zo ta bud'e cikin fara'a da girmamawa ta shiga gaisheta Asma'u ta dafa kanta itama tana jin Munira a ranta kuma tana son ta musamman don yanayin halayenta da ya farrak'a da na y'an uwanta "Munira ya makaranta?" Munira tana murmushi tace "Hutu ake" Asma'u ta danna kai cikin falon tana fad'in "Suma sun so zuwa yanayin karatun na sune ya yi zafi na ce su bari sai an yi hutu." Tana nufin yaranta.

A hakimce ta tarar da Sakina da Kady a zaune a tsakiyar carpet d'in da yake falon. Sun baje tarkacen kayan ciye-ciye iri-iri da suka gama ci. Gefe d'aya kuma kayan kitchen ne na amare suke ta dubawa. Sallamarta ya sa suka yi saurin d'aga kai. Sakna ta yi kicin-kicin da fuska don haushin zuwan Asma'un take ji musamman da suka saka Didi a gaba da magungunan karya asiri. Ba ta damu da yanayin kallon banzan da take mata ba, ta samu kujera ta zauna fuskarta d'auke da murmushi na zallar mugunta ta ce "Barkanku da safiya matar Yaya, sak'o daga Didi tana son ganin kowa a fadarta har mai gidanki." Da sauri ta d'aga kai tana kallonta tana shirin rud'ewa ta ce "Didi kuma?" Asma'u ta d'aga kai cikin ginshira da k'asaita ta ce "Yes Didi dai ta mu ta gargajiya Allah ya bud'i bakinta yau." Daga haka ta mik'e "Mintuna ashirin ta bawa kowa ya hallara a gabanta." Wannan karan k'iris ya rage Ammi bata saki gudawa a wando ba. Gaba d'aya ta gama rud'ewa har bata san sanda Asma'u ta fice daga d'akin ba. Kady ta ja tsaki kafin ta ce "Tashin hankali matsala sabuwa! Amma in dai haka ne malamin nan ya yaudaremu da ya ce bakin almura ba zai tab'a bud'uwa ba." Sakina ta mik'e ranta a jagule ta ce "Ta ya bakinta ba zai bud'u ba alhalin shegiyar matar nan ta zo k'asar nan mijinta fa shehin malami ne."
Asma'u da take leb'e a bakin k'ofa ta yi saurin sakin murmushi sannan ta sake komawa falon idanunta cikin na Sakina da ta sake firgita da ganinta ta ce "Am sorry wayata na manta." Ta zura hannu ta d'au wayar da ta danna recording a kujera ta fice tana sakar musu murmushi zuciyarta fal farincikin samun nasarar nad'e maganganunsu ko wannan ya isheta kafa k'wakkwarar shaida.

Ya Abin Yake?Where stories live. Discover now