40

329 3 2
                                    

Babu alamar razana ko firgici a fuskarsa, ya sake dubanta ido cikin ido ya ce "Nanna kenan, ba na shakkar ki gayawa duniya ni na yi cikin Kamla na haifeta,
Kamar yarda ban ji kunya ba da aka danganta ni da Hamda, sai dai Zan sake tabbatar miki waccan maganar da na kafa miki sharad'i a kanta tana nan ban janyeba, don haka idan kin shirya karb'ar takardar sallama rubutawa ba zai zame min aiki ba." Daga haka ya saka kai ya fice ya bar Nanna da wani irin tsoro da tashin hankali, ita kanta ta San ba ta da muhimmanci a wajensa, idan ban da haka me yasa a koda yaushe ba ya jin shakkar furta mata zai iya rabuwa da ita. Ta saki murmushin takaicin yarda ya mayar da ita wawuya ya fice ya barta. A tunaninta zai ji tsoro idan ta yi masa barazana da fallasa waccan sirrin madadin haka sai ta hango dakiyarsa da juriya akan lamarin. Ta tabbata ko fad'an ta yi ba zai damu ba.
Ta zauna a gefen gadon d'akin Mahmahn tana cigaba da tattara kayanta gidansu take son zuwa taga Dida tunda ta zo ba su had'u ba.
Mahmah ce ta tura k'ofa ta shigo d'akin idanunta akan Nanna da ta lura da zallar tashin hankalin da ya mamaye fuskarta, ta d'auke kai ba tare da ta tambayeta ba, don itama hankalinmata ba a kwance yake ba. "Ina zaki? Na ga kina tattara kaya?" Murya na rawa tana ji tamkar ta rusa ihu ko ta huta da nauyin da k'irjinta ya yi, cikin rawar murya ta ce "Gida zani Mahmah." Tsawon lokaci ta d'auka tana nazarinta tabbas ta hango damuwa kwance a k'asan ranta kuma kamar tana k'okarin b'oye mata wani abin. Ta dafata "Nanna bana son ki saka damuwa a ranki, insha Allah auren Hamda da Hammad kamar na saka an warwareshi da son zuciyarsa ko babu, don nima ba zan so ki yi boranci a gidan aurenki ba, hakan ba zata faru ba insha Allah, kuma zuwa gida a wannan k'adamin ba kama ki ba, kin san dai kina zuwa Dida zata isheki da tabayoyi k'arshenta idan ta ji shirinmu ta ruguza mana tsari da wa'azinta da nasihar da ta saba, don haka ki bari mu aiwatar da komai kawai ta ji labari idan komai ya kankama." Nanna ta ja ajiyar zuciya tana jin kamar ta gayawa Mahmah waccan sirrin tana tsoron furucin Hammad a kanta, don haka ta ja baki ta tsuke tana jan ajiyar zuciya, shawarar Mahmah itace abar d'auka gwara ta kasa ta tsare har sai ta ga abinda ya turewa buzu nad'i. Zaman aure da Hammad yanzu ta fara, kuma ba zata amince ta yi boranci a gidansa ba. Don haka ta dire jakar had'e da mik'ewa ta ce "Bari inje can sashen namu tunda kin saka an gyara." "Yauwa maza je ki, kada ma ya samu damar da zai sake zuwa wajen waccan yarinyar, ki tabbata kin janye hankalinsa." Ta fice tana jin k'warin gwiwa a ranta.

*********
Hamda jiki ya yi sauki har likita ya bata sallama. A kuma rana d'aya aka sallemesu da Abbu bayan an d'ora shi akan magani an kuma zayyana wa iyalinsa dokokin da za su kiyaye masa. Ammi dai tuni ta janye jikinta daga asibitin ganin ba wanda yake marabtar ta har gwara ma Gadanga, amma idanun Didi ma tsoro suke bata, ranar k'arshe da ta zo ta tabbatar mata idan ta sake zuwa a take a wajen zata saka Gadanga ya saketa wannan ne dalilin da yasa su Najwa suka hanata komawa zuwa asibitin. Su dai suna zuwa kuma har Hamda sun je sun duba zuciyoyinsu cike da tausayin yarda ta zamo bare a cikinsu ga shi bata samu tausayin uwa ba. Munira ranar a wajenta ta wuni.

Suna komawa gida Najwa da ta zo daga Abuja ta saka Ammin a gaba da nasiha akan lamarin Hamdan, "Don Allah Ammi ki tausaya mata, ki daina nuna mata k'iyayyar da kike mata, zafin zai mata yawa ki tuna fa ba laifinta bane Ammi, duk ke kika jawo mata wannan matsalar sannan kuma ki kasa janta a jiki ki nuna mata kulawa." Ammi ta d'auke hawayen idanunta, a karo na farko ta kalli idanunwan babbar y'arta ta saki ajiyar zuciya ta ce "Ni kaina Najwa a yanzu ina takaicin yarda na bazangatar da lamarin Hamda na yi kuma d na sani matuk'a da gaske, amma zallar kunyar Hamda ce ta sa na kasa kusantar ta a yanzu. Kunyarta na ke ji Najwa ban san ya zan mata bayani ta fuskanceni ba, na dad'e ina cutar da ita, cutar da ko d'an rik'o ba zaka yiwa ita ba, tunda nake Hamda bata tab'a jin d'umin jikina ba, ban tab'a mata wanka da kaina ba, balle tsarkin fitsari ko kashi, zan iya k'irga sau nawa na bata mama na ta sha, ban tab'a kallonta na mata magana mai sanyi ba, kullum sai hantara da cin mutunci, da musgunawa, idan bata da lafiya ban san ya take ta warke ba tunda bana kaita asibiti, duk da haka a kullum cikin kyautata min take ko bata da lafiya bata fasa yi min aiki, ni da kaina na san ban kyauta ba Najwa ta ya zan gyara tsakani na da ita?" Kuka ne sosai ya kece mata, Najwa kanta kukan take irin wannan ranar ta dinga gujewa Ammi tun a lokutan baya da take gallazawa Hamdan ga shi ta zo a cikinsu ba wanda Ammin ta bari ya kyautawa Hamdan don a lokacin ma ta sha fad'a musu bata k'i Hamdan ta rasa ranta ba sanadiyyar bak'anta mata da ke. Kuka sosai su ka yi kafin Najwan ta share hawayenta ta dafa Ammin kafin ta ce "Ki nuna mata soyayya, ki jata a jiki ki bata kulawa ta yarda za ki goge wancan bak'in fetin da kika sakawa zuciyarta duk da goguwar tasa zai zama aiki ne ja." Ammi ta share hawayen, numfashinta da kyar yake fita saboda yarda take kukan sosai abubuwa goma da ashirin sun cakud'e mata, ga rashin ragayyar da ta hango a idanun Abbun ga fargabar sakin da Didi ta ce sai an mata, idan da abinda ta fiso a rayuwarta to rayuwar aure da Abbu ne, jikinta a sanyaye ta mik'e tana jan istigfari a zuciyarta.

**********

Didi na kishingid'e a falonta ita da Lauratu tana matsa mata k'afafunta. Umma Asma da Hamda suka yi sallama cikin falon, a firgice Didi ta mik'e tana kallon Umma Asma da Hamdan fuskarta a had'e ta ce "Asma'u lafiya ko?" Murmushi ta yi jikinta a sanyaye ta shige gaba had'e da cewa Hamda "Shigo mana, Ki ka ja kika tsaya, ko nan d'in bak'onki ne?" Da kyar ta ja k'afafunta ta isa gefen kujerar da Didin take ta d'an rank'wafa da niyyar gaisheta.
Didi ta watsa mata wani kallo ciki-ciki ta amsa gaisuwar ta ta had'e da cewa "Maza ki wuce wajen uwalki, Ai yanzu ba ki da mahalli anan, to fisabilillahi fa, me ye had'i na da ke? Da d'in ma da ki ka ga na jaki a jiki na zata jinin Umalu ce, amma yanzu tunda na gane ba bu abinda ya had'aki da Umalu ma balle kuma ni, son ki a likkafa ki ja sillan k'afafunki ki yi wajen uwalki kafin shi Umalun ya San yalda zai yi da ita, tunda ina nan na zuba ido tai Takina ta bal gidan nan wallahi." Jikin Hamda a sanyaye ta mik'e da niyyar barin wajen, Umma Asma ta saka baki ta kira sunanta "Hamda, maza wuce cikin d'akinki." Ganin babu Wasa a fuskar Asmaun Yasa Hamda ta shige ainahin d'akinta na b'angaren Didin. Didi ta saki baki tana kallon d'iyar tata cike da mamaki ta ce "Ba Shakka, Shin Asma'u yaushe kika maye gulbin uwata ba ni da labali? To wallahi ki je ki fice kin da waccan k'anwal shegiyal kafin na had'aku na ci muku mutunci, zancen banza zancen wofi me ya had'ani da ita?" Asma'u fuska a d'aure ta ce "Abinda ya had'aku shine Auren Hammad da ta yi, don haka tilas ba ta da Inda ya fi nan, don Allah Didi ki tausayawa yarinyar nan ki rik'eta, ni fa na san Didin mu mai hak'uri ce, yara nawa kika rik'e a gwarzoma balle wannan da dama ta taso a wajenki kin san dai ballagazar uwarta ba rik'eta za ta yi ba, ga Sadiya da shashanci ta ce Hammad sai ya saketa to ina ki ke so ta je? Ki tuna fa d'a na kowa ne, kuma hakan da za ki yi sai ya zama silar shigarki aljanna." Didi ta saki ranta musamman ganin yarda Asma'u ta ke sake kambama lamarin tausayi da jin k'anta sai ga shi tana sakin murmushi ta ce "Allah na tuba dama ni me ta yi min? Da Allah ya rufa mana asili ma uwal ta hanyal halal ta samal da ita, zan lik'eta amma ki tabbata kin ja kunnen d'an ki wallahi ba shi ba hanyal nan d'akin kada in ga k'afafunsa dama anan, lokaci na ne nima yanzu wallahi sai na mulza kambuna, ai ni ya yi min daidai da ya rama min abinda ubansa ya yi min ya je ya yi aule ba tale da Sanin kowa ba, ki gaya masa ba shi ba sashen nan te ya take neman aule daga falko idan na ga dama na ta Tadiya dole ta amince ya d'au matalsa idan na ga ba a kyautata min kuma wallahi na bawa wani aulenta."

Jikar Nashe ce✍🏽✍🏽📄

❤️❤️❤️❤️❤️🙏

Afuwa insha Allah yanzu yara sun samu hutu daga gobe za ku dinga ganin dogon posting nagode.

Ya Abin Yake?Where stories live. Discover now