8387
[1/12, 7:47 AM] Nazeefah Nashe: Tsayuwarsa a gabansu shi ya bawa cikinsu damar sakin wani irin rugugin sauti na razana da kid'ima. Daga yanayin kallon da yake musu tabbaci ne na cewa ya ji duk manak'isar da suke shirin k'ulla masa. Murmushi kawai yake saki mai nuna tsananin takaicin kasancewarsu zuri'ar mahaifinsa. Idan wani ne ya gaya masa hakan zata iya faruwa a rayuwa zai iya k'aryatawa sai ga shi zahirin lamarin kacokam ya faru a kansa, y'an uwansa da ya sani wanda suke uba d'aya su suke neman rayuwarsa bayan sun gama neman ta y'ay'an cikinsa duk akan wani banzan lamari wai dukiya da take k'arewa a duniya duk kud'in mutum bai isa ya tafi da shi lahira ba sai dai ya tafi da aikin ladan da ya yi ta sanadiyyar kud'in. Ya lumshe idonsa wasu hawayen bak'in ciki suka shiga zubo masa, bai san me yasa y'an uwansa suke k'insa har haka ba, duk da tarin kyautatwar da yake musu ba wanda ba ya cin moriyar arzikinsa mazansu da matansu, kai har ma da yaransu, akwai albashi da yake marasa k'arfin cikinsu duk wata ban da zakka da yake dunk'ulewa ya basu, hidimar biki shine kai komai ma shi d'in dai KK shine mai d'aukar kaso mafi tsoka a hidimar ahalin K. Mud'allab sai ga shi zuri'arsa ce ba sa so da shi kansa suke neman hanyar hallaka shi, anya kuwa ubangiji zai barsu da alahakin wannan bawa nasa, kaico wannan zamanin da son zuciya ya yi bake-bake a zuk'atan al'umma. Kukan ya ke sosai kukan da ya karya zuk'atan tsirari daga cikinsu suka riski zuk'atansu a cikin tarin da na sani, kunya matsananciya ta yi musu dabaibayi a zuciyoyinsu suka fara tunanin ta yarda zuciyarsa ta dinga ingiza su da bin son zuciyar wasu daga cikinsu.Lamarine mai girma a wajen KK don haka ya kasa furta musu komai illa jan sawayensa da ya yi ya fice daga bigiren da suke. Zuciya bata da k'ashi a yau duk hak'urinsa zuciyarsa ta karye ba ya jin har abada zai sake dubansu da idanun rahma, bai tsanesu ba amma ya zama dole ya nisanci mu'amala da su, duk kuwa da yake musu zahirinsa da bad'ininsa Allah ne shaida amma tunda su sun kasa fuskantar haka ya zama dole ya bi da su ta hanyar da karatun rayuwa zai fahintar da su, shima d'an zamani ne mai kuma madafan iko tunda yana da kud'i ya tabbata ko k'ara zai kaisu shine a sama, amma ba zai aikata haka ba, ko bakomai suna amsa sunan mahaifinsa ne K. Mud'allab albarkacin wannan sunan da yake rab'e da nasu ba su cancanci tozarci ba, sai dai zai bar su da halinsu ta hanyar yanke duk wata alak'a da su. Alhamdulillah tunda yanzu yana da zuri'a yana kuma da Ahalin Didi da ya mayar da su tamkar nasa ahalin madallah da ubangiji buwayi gagara misali. Da kansa ya fisgi motar da mugun speed ya bar harabar gidan, don dole escort na sa suka bi shi suma a guje, zuk'atansu cike da tunanin dalilin tashin hankalin da
Suka ga uban gidansu a ciki, fatansu dai ya zama komai lafiya.Bai tsaya ko ina ba, sai a gaban Didi. Cikin tashin hankali ya shiga falon Didin. Idanunsa sun kad'a sun yi jajir ya zube gwuwoyinsa a gaban Didin ya dafa cinyoyinta yana sakin wata irin ajiyar zuciya mai bayyana mad'aukakin tashin hankalin da yake ciki. Didi addu'a kawai take ja a zuciyarta don idanun KK kawai zaka kalla ka san zuciyarsa a turnik'e take da tashin hankali. Ta hau shafa kansa tana bubbuga bayansa had'e da jawo masa addu'oin samun sauk'in zuciya 'Allahumma la sahla illa ma ja'altuhu sahlan wa anta taj'alil hazna iza shi'ita sahlan.' A hankali ya dinga maimaita wa kafin ya saki wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ya lumshe idanunsa ya zame ya kwanta a k'asan carpet d'in Didin had'e da yin matashin kai da hannayensa. Nauyayyan barci ne mai k'arfin gaske ya d'aukeshi. Didi ta saki ajiyar zuciya had'e da zuba masa ido cike da tausayawa ta tabbatar duk abinda ya gigita shi mai girman gaske ne tausayinsa ya kamata, ganin duk tarin dukiyarsa shima akwai ta yarda Allah ya jarrabeshi don haka duk wanda ka ganshi kada ka yi addu'ar zama irinsa saboda baka san tarin matsalolinsa da suke bad'inance ba, kowa da inda yake da nak'asu a rayuwarsa. Didi ta saki ajiyar zuciya had'e da Kunna masa sautin Alkur'ani a gefen kunnensa sannan ta mik'e ta shige d'akinta, jin KK take kamar jininta a zuciyarta take jinsa kamar yarda take jin dukkan ahalinta.
____________________
Sai Azahar Umma Asma ta bar asibitin ita da Ammi da ta zo duba Hamdan bayan bayyanuwar ciwonta, suka bar Sa'ada da Munira a wajenta, sabida jikin nata da sauk'i su kuma akwai abubuwan da za su yi masu mahimmanci tunda bikin dai saura kwana uku kacal.
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.