A falon kowa ya hallara, ta samu zuciyarta da tsinkewa ta fad'i tunanin da tuni a cikin jama'ar nan zata zo ta zuba rashin mutunci. Didi ta zuba mata ido cikin takaici ta ce "Ba shakka Sadiya, wato nema ki ke duk wasu d'abiu na Sakina da ta zubar da su, ke ki tattara ki yayima ki zubawa kan ki, ana yabonki Sallah za ki kasa alwala, idan banda haka mutun nawa na aika kiranki ki ka yi burus da ni sai yanzu da d'anki ya je ya lallab'o ki sannan za ki zo ko?" Girgiza kai Ta yi kawai had'e da zama cike da kasala ta ce "Ki yi hak'uri Didi, ba k'in zuwa na yi ba bana jin dad'i ne." Didi ta girgiza kai "Ko da na ji, nan ina nan ina mamakin yarda ki ke nema ki canja daga ainahin sunanki na Halimatu wato mai hak'uri, ai duk wata Halima da hak'uri aka santa idan ba so ki ke ki zama masifatu ba, yo fisabilillahi waye bai san kalar hak'urin da kika yi a gidan nan ba, k'iri-k'iri Umaru ya dinga banbanta ki da abokiyar zamanki kai wallahi Umaru ina jiye maka tashi ranar alk'iyama da shanyayyen jiki Idan Sadiya bata yafe maka hak'kintaba kai da matarka." K'asa Abbu ya yi da kansa yana jin kunyar yaransa Su Hammad da suke zube a wajen, wani abu ne na tausayin Sadiya ya taso tun daga yatsansa ya lullib'e idanunsa, kunyarta yake ji sosai da ta yaranta, yau kam Didi ta b'aro masa aiki ta kuma ankarar da shi abinda ya dad'e yana son gyarawa son zuciya da sharrin shaid'an had'e da bin k'awace-k'awacen duniya ya hana shi ankarewa, sai yau da Didi ta taso da maganar takaicin kansa ya kamashi ya kasa had'a ido da kowa a d'akin musamman Sadiyar da ta sauke nata idanun a kansa tana son taga yarda zai yi, Ba shi da laifi a wani b'arin Sadiyar ce ta janyo koma mai ya faru, wata zuciyar kuma na k'addamar masa da laifinsa da hasko masa tarin kuskuren da ya tattafka a tsawon zamansu da Sadiyar, ya wajaba kam a gareshi ya nemi yafiyar ta kafin abinda Didin ta fad'a ya tabbata a kansa ya tashi da shanyayyen b'arin jikin, yana kallon idanun da Humaid ya zuba masa ya tabbata Ba tun yau yaron yake rik'e da shi a ransa ba, don duk ya fi su Hammad zafin zuciya. Ya gyara zamansa idanunsa cikin na Sadiyar yana sakar mata da murmushi zuciyarsa na hasko masa tarin kyawawan halayenta da nagartarta duk da ta b'angare d'aya take da cikas hakan ba zai zama hujja a gareshi da zai kasa yi mata adalci ba, d'auke kai ta yi tana fuskantar Didi da ta fara Rabon sufofinta, zuciyarta fes ta tabbata daga yanayin murmushin da ya sakar mata sak'on Didi ya isar masa burinta ya yi aiki da hakan su yi zamansu lafiya cikin aminci da k'aunar juna, abu d'aya ne Ba zata iya wannan kwamacalar soyayyar ta zamani, za dai ta k'okarta wanda ta ga zata iya, tausa, shafa masa mai amma banda duk wani kalar barikanci da Sakna take yi, wannan kam ta barwa yara ita da kanta ta yarda da maganar bahaushe da ya ce 'In An girma a san an girma'Jikar Nashe taku ce!
❤️❤️❤️❤️❤️🙏
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Zuciyarta fresh ta tashi tana jin ta wasai duk wani tarin shirgi na b'acin rai da aka dasawa zuciyarta tuni ya zagwanye. Wanka ta yi sosai ta hau gyara jikinta, yau kam da tunanin Hammad ta tashi ganin tun ranar bai sake neman keb'ewa da ita ba, bata sani ba ko fushi yake da ita ba, duk sai ta ji hankalinta ya tashi. Ta feshe jikinta da tsadadden turarenta duk da azimi ake amma sanin cewa ba inda zata yasa ta shiri na musamman. So take ta zagaya Sassan gidan ta gaishesu abinda ta dad'e ba ta yiba. Sosai ta yi kyau cikin sassauk'ar doguwar rigar da take jikinta ta yane kanta da mayafin rigar kafin ta goga lip stick.Dama tuni ta gyare b'angaren Didin tun suna barci da safe. A falo ta samesu suna kallon wa'azi a tashar Sunna t.v. Tsananin kyan da fatarta ta sake ne yasa Asma'u sauke magananta a kanta tana mamakin canjawar Hamdan cikin lokaci k'ank'ani, da alama gyaran da ta fara mata magungunan suna bin jikinta yarda ya kamata, tana tunanin anya kuwa Hammad zai iya jurewa ya hak'ura har lokacin da aka d'iba na bikin nan? Didi kuwa fad'i take "Tubarakallah Masha Allah, yanzu da kina da wannan kyan duk bai bayyana ba sai yanzu, gaskiya dai Sakina ta musgunawa rayuwarki duk ta bi ta sukurkuta ki ba a ganin komai a tare da ke sai tarin manyan idanuwa wannan kam kamar kya kwashe mutum da su." Hamda ta tsuke fuskarta tsam yanzu kam sam bata son a dinga zagar mata Amminta jinta take har k'okon ranta. Ta d'an gyara tsayuwarta kafin ta ce "Bari na shiga gida na gaishesu kafin time d'in d'ora abinci ya yi." Didi za tayi magana Asma'u ta yi saurin cewa "Maza ki je, hakan ya yi kyau sai kin dawo. Y'an uwanki ma yau suna hanya." Cikin farin ciki ta ware ido don ta san su wa UMMA Asman take nufi y'ay'anta da suke Dubai, kuma akwai sa'arta da suke mugun shiri a duk lokacin da suka Nigeria, zata iya cewa ma bata da aminiyar da ta wuce Sa'ada, da sauri ta ce "What time za su iso Umma?" Ta d'aga hannu tana nuna mata 4 da hannunta, Hamda ta yi saurin cewa bari na yi sauri na dawo na san mai zan dafa musu Sa'ada na san dambun shinkafa." Asma'u ta girgiza kai had'e da cewa "Tabbas, shine favorite d'inta, amma su su Babana ai ba sa sonsa." Ta d'an sosa kai tana son ta ce ina ruwanta amma kasancewar tunda can bata da wannan k'warin gwiwar yasa ta kasa furta abinda yake zuciyarta illa murmushi da sosa kai ta fice da sauri. Ta bar Didi tana zabgawa Asma'u harara kafin ta ja tsaki ta ce "Wallahi Asma'u idan kika ce haka zaki dinga min shishshigi akan yarinyar nan tsaf zan tattara komatsanki ki koma waccan shiyyar da ake sauke bak'i, saboda Allah ta ya zaki ce ta je ta gayar da mutanen gida? Ni fa bana son su shirya da uwarta balle ta samu fuskar da zata nuna min iko akan yarinyar da
Bata san yarda aka yi ta girma ba." Asma'u murmushi kawai ta saki tana jaddada rigima irin ta Didi ban da haka ta ya zata yi ta raba yarinya da uwarta ta ce da ita kawai zata yi shiri? Sai dai bata tankata ba ta ja baki ta yi shiru duk da tana jin Didin na sake mita tana bala'i kamar ta ci babu.
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.