18

460 9 0
                                    

ALK'ALAMIN JIKAR NASHE

YA ABIN YAKE?

BONUS PAGE 18

08033748387

✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽

Yau Didi jikin sosai ta mik'e idanunta sosai akan y'ay'anta da suka baibayeta zagaye da ita a gadon asibitin.
Gwaggonsu Amina ce har a lokacin ba ta iso daga Dubai, don ta ce musu tana hanya a cikin satin mai zuwa.

Didi so take ta yi musu maganar Hammad amma ba baki, sai da dabara ta fad'o mata sannan ta duni gadanga ta yi masa alamar ya samo mata abin rubutu. Shi kad'ai take wa fara'a bayan shi ko kallon arziki ba ta yiwa Abbu da Lauratu.

Gadanga ya fita zuwa motarsa, ya samo mata littafi sabo da biro yana jin dad'in yau za su San abinda yake ranta. Sam ya mance da wannan hanyar ta rubutu.

Yana komawa d'akin ya manna mata biro da takardar. Ta amsa sannan ta fara rubutun duk da dai ta fi ganewa Ajami amma haka ta dagura Hausar. Ina Hammad da Hamda? Shine abinda ta rubuta ta mik'awa Gadanga, ya yi tsai da ransa saboda bai San abinda zai ce mata ba, shi kansa bai ji dad'in hukuncin da Yayan nasu ya zartar be. Sai da ta sake tab'o shi ta tsatstsareshi da ido sannan ya saki ajiyar zuciya a hankali ya ce "Yaya ya kore su." Didi ta mai da kallonta kan Abbu kafin ta mik'awa Gadanga hannu ya bata takardar da rubuta kalmomi guda uku ta mik'a masa "Ka yi gaggawar dawo da su, kafin na wa ran ya b'aci." Daga haka ta mik'awa Gadanga takardar ta mayar da kanta Ta kwanta zuciyarta ce ta ke suya Idan ta tuna da lamarin.

Abbu kam Shiru yayi fuskarsa a d'aure saboda umarnin Didin ya zo masa a bazata. Sam ba ya jin zai iya yafewa Hammad wannan gungumemen laifin, ita kuma yarinyar da zarar ya cigaba da ganinta tsanarta ce zata dinga hauhawa a zuciyarsa. Sai dai ya san sarai ba shi da ja akan umarnin Didi musamman da ya lura ko son had'a ido da shi bata yi.

Ammi kuwa dama ba zuwa take ba, sabida tasirin idanun Didin a kanta yarda take k'in kula ta da banzan kallon da take mata dalilin kenan da yasa ta bi shawarar Kady aka kai Didin wajen malami ya d'aure mata baki, la'akari da duban da take mata ta san zata iya tona mata asiri. Shi yasa a daren ranar ta nemi shawarar Kady ita kuma ta bata shawarar a mannewa Didin baki, ba sai tana magana ba balle ta k'aryata Ta. Shi yasa Ammin take shan shatafinta ko bakomai ta cusawa Sadiya bak'in ciki goma da ashirin, dama ta tsaya mata a rai bata son ganinta burinta bak'in cikin Abin nan ya kashe su ita da Didin idan yaso ta mallaki gida ba wanda zai saka mata ido.

Budirinta take sosai, musamman na shirye-shiryen auren y'ay'anta Najma da Nasma, ba ta damu sam da halin da ahalin d'an borno suke ciki ba, cafkar naira take a wajen angwayen son ranta irin surikan da take so kenan, y'ay'anta su samu mazaje na kece raini ba ta damu da wa za su aura ba? Menene halayyarsa? Burinta kawai su samu Hamshak'an masu kud'i wanda suka ci suka tada kai ba matasan masu kud'i ba, shi yasa ba ta kyashin fitar da ko nawa ne akan y'ay'anta don tabbas ta san kwalliya zata biya kud'in sabulu.

******

Tsawon mintuna Ashirin yana zaune cikin motar yana jiran Hakimar tasa Nanna kenan, bai d'auka har a lokacin fushin take da shi ba da bai wahalar da kansa ya zo ba, da sai ya turo mata text ya ce mata jibi za su tafi. Dama yazo ne su fahimci juna ita kuma ta zauna ta na b'ata masa lokaci. A d'abiarsa shi mutum ne da ba ya son rainin hankalin y'a mace sam ba ya jura. Wa la Allah ko don ya taso da taurin zuciya tunda abin ya faru ya dainewa mata uzuri a rayuwarsa. Gani yake duk halinsu d'aya, shi yasa ko da aka ba shi zab'in aure ya ce su zab'a masa ko ma wacece ba shi da lokacin soyayya da y'a mace, shi yasa Sam fushin Nanna ba ya tasiri Akan sa. Sau tari da kanta zata yi fushin da kanta kuma zata sharewa kanta hawaye ta sauko ta zo tana neman sulhu a wajensa. Duka mata kud'in goro yake musu bai tab'a kallon mace ya ji yana sonta ko ya furta mata ba. duk da karakaina da matan suke a kansa da nuna masa soyayya baya jin komai a ransa game da su, shi yasa a yanzun yake mamakin kansa da har ya shiga hurumin Hamda yake tausaya mata, bai San dalili ba, ko don kasancewarta.... tsam ya yi da ransa yana cije leb'e kafin ya sauke ganinsa akan Nanna da take taku tamkar wahainiya duk don ta ja ra'ayinsa, Sai dai ta makaro don sau tari ko a b'angaren mu'amalar aure Nannan ce dai take kawo kanta gareshi ba dai shi ya nemeta ba. Ya lumshe ido bayan ya ja hucin ajiyar zuciya sannan ya danna button motar ta yi unlocking kanta, hakan ya Bawa Nanna damar shiga gaban motar, bayan ta sake d'aure fuskarta tamau,
Duk da gargad'in da Dida ta yi mata bata ji ba, burinta ta samu ta lallashe shi ya janye tafiyar da waccan bak'ar yarinyar da haka kawai ta ji ta tsaneta.

Ya Abin Yake?Where stories live. Discover now