21

453 4 0
                                    

Hannunta ne sosai ya fara rawa tana k'ok'arin matsawa daga daf da juna da suka yi. Tunani take anya Yaya Hammad bai samu matsalar k'wak'walwa ba ya za'a yi yace shi ya aureta shikkenan daga matsayin wa ya koma Uba, daga uba kuma ya koma miji lamarin kamar almara. Har a lokacin idanuns cikin nata suke ya gagara sauke su, damar da ya dad'e yana jira kenan. Tana k'ok'arin zamewa ya sake janyota jikinsa "Kada ki hanani kusantar jikin da yake halaliyata da gaske ni ne mijinki ki nutsu sosai zan gaya miki abinda kika dad'e kina son ji. Ba ni da alak'a ta jini ko d'aya da ke." Ya kama hannunta ya zaunar da ita a gefen gado still hannayensu cikin na juna yana murzarsu a hankali ganin a rud'e take ya sa a hankali Cikin wata irin murya ya fara magana a kunnenta tamkar ba ya son wani ya ji "Da hankalina Hamda, da gaske nake miki ba ni da alak'a ta jini da ni da ke. Duk da labarin ba mai dad'in ji bane zan sake tabbatar miki ke y'ar halak ce kuma y'ar sunna da mahaifiyarki ta bi son zuciyarta domin samar da ke. Na San za ki fara tunanin wace irin magana ce wannan ana aure akan aure ne? Ba ni da wannan amsar Hamda amma da kunne na ji sanda ake jaddada ke y'ar halak ce y'ar sunna." Zuwa yanzu rikitar da take cikin kwanyar Hamda ta bi gaban a misalta da gaske ta shiga cikin rud'u don haka kallon Hammad take kawai zuciyarta na d'agawa da sauri da sauri har hakan yana bayyana ta saman rigarta. Jin ta take tamkar a wata duniya ta mafarki da take fatan ta farka nan kusa a kuma sanar da ita mafarkin da ta saba ne mafarkin aurenta da Hammad. Ta yi mafarkin nan ya fi a k'irga a rayuwarta tun bayan dawowarsu da suka had'u take mafarkin sa a matsayin mijinta mai nuna mata zallar soyayya da gaske Didi take a duk San da ta rungume pillow a cikin barci to ba kowa take rungumewa ba sai Hammad har
Hakan ya rinjayi zuciyarta a zahirance idan har za ta ga Hammad to za ta ganta rungume a faffad'an k'irjinsa ya nuna mata zallar soyayya. Ta fi alak'anta hakan da shaid'anu ko aljannu da suke suffanta mata Hammad d'in a matsayin mijin da ya dace da ita da zarar hakan ya faru ista'aza take yi a ranta ta kuma runtse idanunta tana jin bugun zuciyatta.

Sai ga shi yau a zahirance ba bad'inance ba ita ce daf da Hammad yana nuna mata kwatankwacin waccan soyayyar ta bad'ini.

Bai bar murza hannun nata ba, ji yake hakan da yake yana samar masa wata irin nutsuwa da shiga wata duniya da bai tab'a katarin kasancewa a cikinsa ba, ko don bai tab'a had'uwa da macen da yake wa kwatankwacin so irin na Hamda ba. Tun bayan zuwansa Nigeria da ya kyallara idanunsa a kanta ya ji matsananciyar k'aunarta ta kama shi irin k'aunar da take huda k'ashi da b'argo fatansa kawai a kullum hanyar da zai bi ya mallaketa ya ji tattausan hannunta a cikin na sa hannayen ya ji wannan tattausa lab'b'anta masu tudu kad'an a cikin bakinsa ya ji shi yana murza dukka sassan jikin ta da ya tabbatar da cikar halittun ta ko ta ina, cikin tafukan hannayensa. Ya kwana da sanin cewa idan har ya ce zai aureta akwai rigima kwatancciya da zata b'ullo shi yasa ya dinga k'ok'arin danne duk wata zilamarsa. Sai yau da ta zama halaliyarsa mallakinsa ta amsa sunanta na Hamda Matar Hammad. Ya lumshe wasu hawayen farin ciki suna ziraro masa bai tab'a sanin ashe haka masoya suke ji ba sai yau da ya mallaki Hamda ashe tilas masoya su rud'e a lokacin da suka rasa abinda suke so. Yana son Hamda son nan da ake cewa So da zai iya aikata komai a kansa ciki kuwa har da sadaukar da rayuwarsa kacokam a kan ta.

Zame hannunta ta shiga yi saboda wani irin yanayi da Ta shiga. Da sauri ya sake damk'e hannun ya jingina kansa a saman kafad'arta bakinsa a cikin kunnensa ya ce "Please kyaleni Hamda kin san tsawon lokacin da na dad'e ina jiran wannan ranar." Ta lumshe idanunta tana amsar sak'onnin da yake isar mata wata irin kunya ta kamata saboda yarda ya rikid'e mata sam ba kunya a lamarin sa yau ya ajiye Yaya Hammad d'in ya ajiye Daddyn da ta ce ta dinga ce masa ya koma mata Hammad d'inta na mafarki.

Murya a dashe, muryarta da yake so sosai a dashe take kad'an ta ce "Please Yaya Hammad!" Da kyar ya bud'e idanunsa da suka canja kala a kanta kawai sai ji ta yi ya rungumeta tsam a jikinsa yana k'ok'arin zame mayafin da ta k'udundune kan ta da shi. "Ni fa ka kyaleni ba zan amince da kai ba har sai ka tabbatar min da gaske ba ni da alak'a ta jini da kai kada naje ko irin abinda ka yiwa Ammi zaka yi min..." Cikin wani irin sauri ya sake ta yana bin ta da wani kallo sai dai madadin ta ga alamun b'acin ran sa still soyayyarsa ta gani kwance a idanun. Ya ja ajiyar zuciya kafin ya mik'e ya bar d'akin gaba d'aya sai kuma jikinta ya yi sanyi ta ji sam bata kyauta abinda ta yi masa ba. Ta lumshe idanunta farin cikin cikar burinta ya gama naso a zuciyarta da gaske Hammad shine mijin ta dad'e tana nema. Bata san sanda ta kai goshinta ta yi sujudar godiya ga Allah ba. Amma kafin ta amince masa ya zama dole ya gabatar mata da shaidu da kuma tabbatar mata ba su da alak'ar jini da shi. Ya kuma sanar da ita ta hanyar da aka sameta tunda ya ce y'ar sunna ce ita? Abin tambaya dama ana aure akan aure ne?

Mik'ewa ta yi tana sake nazarin d'akin, yana d'auke da babban gado family side ruwan k'asa mai adon silver. Kasancewar d'akin da girmansa daga gefe can dresser ne mai d'auke da cahinet ta zuba kaya sai wajen saka takalma da jakunkuna.
Kuma ko ina ta bud'e cike yake da kaya alamar da gaske Hammad ya shiryawa auren nan. Ta tsaya jikin mudubi tana k'arewa kanta kallo tana mamakin mai Hammad ya gani tare da ita har idanunsa suka rufe daga tarin matsalolin da za su shiga nan gaba ya aureta. Tana da tsayi sai dai ba can ba, ta fannin dirin jiki kam sai sam barka haka nan fuskarta ba za'a kira ta mummuna ba sai dai ba ta cikin kyawawa matuk'a ainun. Bakinta ya fi komai fisgar hankali a fuskarta don yana da kyau sosai kasancewarsa mara girma kuma mai d'an tudu ga su pink sosai suna kuma shining kamar an shafa wet lip. Ba ta da hanci mai tsayi na ta tudu ne da shi kuma a duk san da tayi dariya yana lob'awa kad'an sai lob'awar da take k'asan hab'arta. Cikakken gashin gira da na ido shine abinda ya ke sake fisgar hankalin mai kallonta. Da kuma yalwataccen gashin da ya kwanta a gaban goshinta. Tana da duhun kala sosai don ba za'a saka ta a layin farare ba sai dai tsaka-tsaki duk da bature ya ce black is black to tabbas itama Hamda ta yarda bak'ace sai dai fatarta mai kyau ce ainun fiye da ta wasu fararen. Ajiyar zuciya ta ja kafin ta shige toilet ta sake wanka sosai duk wani lungu na jikinta sai da ta sake tsaftace shi. Don ta san jikin nata yanzu ba mallakinta bane ita kad'ai.

Ko da ta fito tsaf ta tsane kanta da towel kafin ta saka hand dryer ta busar da shi. Ta shafa oil ta taje shi sosai sai ga shi ya mik'e sai k'yalli yake. D'aureshi ta yi a tsakiyar kanta sai ga shi ya zama kamar doughnuts.

Ba wata kwalliya ta yi ba, powder kawai ta murtsika a fuska ta shafe bakinta da wet lips mai k'amshin strawberry. Brush ta saka ta taje gashin girarta sai kuma Ta d'an zizara eye liner. Sosai ta fito tsaf da ita bayan ta zira wata doguwar riga pink colour. Madadin ta fita kuma sai kunya ta kamata ta tada sallah kawai kasancewar magriba ta yi. Ko da ta idar nan ta yi zamanta idanunta akan tv amma zuciyarta na ga Hammad ganin har lokacin bai sake shigowa ba, ta san fushi ya yi. Kawai sai ta samu kanta da ganin rashin kyautatawarta ta mik'e cikin mutuwar jiki ta fita parlourn.

Baya parlourn amma ta ji alamunsa a kitchen don haka kai tsaye ta nufi kitchen d'in.

Yana tsaye da ludayin miya a hannunsa duk ya yi kaca-kaca da kitchen d'in wajen dafa noodles da kwai sai fruit da ta gani a gefe an yayyanka. Dariya ta so kufce mata ganinsa da rigar girki a jiki (Apron) ya yi wujiga-wujiga da shi. Ta saki d'an murmushi idanunta cikin na sa. Ya d'auke kai duk da matuk'ar kyau da ta yi masa. Ji ya yi tamkar ya rungumota gaba d'aya. "Ya Hammad sannu da aiki, ai da ka sani ka kira ni na dafa, ka ga ka wahalar da kan ka." Bai kula ta ba ya cigaba da juye abincin a plate yana d'ora forks biyu a kai. Sai da ya d'ora a tray sannan ya dubeta "Ki ciro kaza a oven ki had'o da fruits d'in can." D'aga masa kai kawai ta yi. Ya fice ya dire abincin sannan ya shige bedroom d'insa. Wanka ya yi ya fito daga shi sai riga armless da three quarter wando rigar ja ce wandon fari tas sai ya yi kyau sosai.

Tana zaune k'amshin turarensa ya sanar da ita zuwansa. Ta lumshe ido tana jin tamkar ta tashi ta rungumeshi. Turaren nan ya dad'e yana yi mata gizo a hanci da sanya ta fad'uwar gaba ashe dai zata mallaki mai turaren. Daf da ita ya zauna har suna gogar juna amma ya k'i matsawa don ya fi so su saba ta saki jiki da shi ba ya son ta dinga nesa da shi.  "Ka yi hak'uri idan maganar da na fad'a d'azu Ta b'ata maka rai" Ya d'ago yana sauke idanunsa a kanta "Kin damu da b'acin raina ne?" Samun kanta tayi da d'aga kai tana sunkuyar da kai "To idan ba kya son b'acin raina daga yau kada ki sake min irin waccan maganar ko tambayata wacece ke? Idan lokaci ya yi zaki sani abu d'aya na sani aure na dake ba haramun ba ne halak ne kuma a gaban shaidu aka d'aura da hotuna da vedio da komai."

K'asa ta yi da kanta tana wasa da yatsun hannunta. Zuciyarta ta samu nutsuwa ta tabbata iya gaskiyar sa ya fad'a mata. Hannunta ya kamo cikin wani salo ya ce "Yanzu kin amince za ki amshe ni a matsayin miji?" Ya fad'a yana shafa wuyanta da bata san da ta runtse ido cikin wani irin rawar jiki ta d'aga masa kai. Ya saki murmushi idanunsa akan abubuwan da suke tsone masa ido "Ki shirya tarbata da safe." Da sauri ta rufe idanunta, saboda tsananin kunya da maganr ta bata "Ki yi hak'uri yau ba anan zan kwana ba, duk da ban so haka ba, amma ba yanzu nake son Nanna ta san na aureki ba, sai nan gaba a gaban kowa don haka wuni zan dinga yi anan na kwana a can." Ji ta yi ranta ya d'an sosu amma da yake ta san mijin wata ta aura tilas ta runtse idanunta daga hakan. Sosai ya rungumeta a jikinsa Allah ya sani a dole zai koma wajen Nanna ji yake dama su dawwama da Hamda a haka sai dai ba yarda zai yi. Nanna ta cancanci y darajata ko bakomai ai uwar yaransa ce. Ya mik'e yana jan ta tsaye. Manna mata kiss ya yi a goshi "Kada ki ji tsoro ba abinda zai sameki kin ji my wife." Ta lumshe ido tana jin wasu hawaye na shirin zubo mata da gaske ta amince Hammad shine mahad'in gangar jikinta.

Ya Abin Yake?Where stories live. Discover now