Da sauri Hammad ya fice jikinsa na rawa. Na mik'e ni ma da sauri ina nunawa buzu hanya. Cikin rawar jiki ya ce "Hajiya kada ya illatani." Cikin masifa na ce masa "Ka wuce ka tafi, ba ni abinda zai maka zan yi maganinsa." Ya fice da sauri jikinsa na rawa a matuk'ar tsorace yake.
Na kasa samun nutsuwa bayan na yi wanka na kira Kady da sauri cikin matuk'ar damuwa ba ce mata an yanka ta tashi, Hammad dai babban d'an gidannan ya kama mu dumu-dumu da Buzu." Cikin k'arami Kady ta ce "Innalillahi, ya aka yi wannan katob'ara don Allah?" Na runtse idona kafin na ce "Tsautsayi, ni dai ki gaya min mafita." Ta ja ajiyar numfashi kafin ta ce "Shikkenan, akwai mafita amma dole sai mun saka Hammad ya shiga d'akin ki. Mun d'ana masa tarko mai zafi tukun na inda tilas ma ya ja bakinsa ya tsuke, idan ba haka ba tabbas kina ruwa." Na amince da shawararta, kuma na karb'eta d'ari bisa d'ari tunda ba ni da wata mafita da ta zarce wannan.
A ranar muka d'ana masa wannan tarkon, na isa d'akinsa da yake Boys Quaters, yana zaune hannayensa dafe da k'uncinsa, na kira sunansa ya k'i ya d'ago ya kalleni illa had'e fuska da ya yi, kansa a k'asa. "Ka taso mu je akwai bayanin da zan maka." Funfurunfus yaron nan ya min banza. Ko kallona bai yi ba.
Jikina a sanyaye na bar b'angaren nasa, ina mamakin kafiya da taurin kai irin nasa, duk da lallashinsa da na yi. Ina zuwa na cewa Kady "To ya k'i zuwa, don ba kiga ba ko kallona bai yi ba, balle ya san ina wajen, kady ina tsoron kada yaron nan ya tona min asiri." Ranta a b'ace ta ce "Tunda mun biyo masa ta sauk'i ya k'i, dole mu bi da shi ta zafi, kin ganni nan dama na shirya masa idan har ya yi kafiya, kuma kin tabbatar min ba kowa a gidannan bari na kira yaran da za su kawo shi nan ko bai shirya ba." Ta d'auko wayarta tana kiran yaran da ta sabawa sawa su yi mata aiki. "Ku zo yanzun nan, aikin nan na ga dole sai da ku." Ta katse wayar tana cewa "Ba su mintuna goma, za su kawo shi nan ta k'arfin tuwo, zai gane kafiyarsa ba ta da amfani."
Muna zaune kuwa suka yi mata waya sun zo, da kaina na je na bud'e musu gate d'in, suka shigo kasancewar Buzu yana d'aki cikin tashin hankali, ya yi k'ok'arin ya tafi kuma na hanashi, na tabbatar masa ba abinda zai faru.
Su biyu ne, k'arfafa da su. Na kai su har d'akin Hammad. Duk da gani na da ya yi da su bai saka zuciyarsa ta rusuna ba, sai ma wani irin hucin b'acin rai da yake yi, yana jifana da kallon tsana. Da naga ba zai tafi ta dad'i ba da kaina na ce su d'aukeshi ko a kaine su kai shi d'aki na.
Haka kuwa aka yi, aka shimfid'e shi a gadona, su da kansu suka cire masa kaya, aka kuma d'aukeshi a haka yarda ya ke akan gado bayan sun shak'a masa abinda ya saka shi suman dole.
Bayan farfad'owarsa muka saka shi a gaba ni da Kady, anan nake sanar masa Ba zina nake ba da aurena da maigadi. Na ba shi labari tas tare da nuna masa vedion d'auren auren a camera Kady. Fuskata a d'aure bayan na gama gaya masa na ce "Kuma ka ga idan wannan maganar ta fito, to tabbas zan alak'antaka da wanda yayi min fyad'e har cikin d'akina. Na nuna masa hotunan da muka d'aukeshi rabin jikinsa akan cinyata. Ya tsorata sosai da ganin hoton ya dinga jifana da wani irin kallo na tsana muraran kafin mu ga wasu k'walla sun zubo masa idanunsa suka yi jajazur. Ya dinga fitar da wani irin huci kafin ya mik'e ya fice. Wannan shine dalilin da yasa bai fad'a ba ya ja bakinsa ya tsuke, sai dai sam ba ya yarda mu had'a inuwa d'aya da shi, ya tsaneni sosai kuma ya zama silent ya dinga wasu irin abubuwa kafin a tattara shi ya bar k'asar gaba d'aya. Lokacin Hamda tana da shekara biyu.
Bayan faruwar wannan abin, da sati biyu Umar ya dawo da zakwad'insa ya shigo d'akina sai dai murnarsa ta koma ciki bayan na sanar da shi d'an tayin cikin da yake kwance a marata. Ya d'ago yana kallona a firgice cikin sagewar gwiwa ya ce "Yanzu har sai kin haife cikin nan kafin a samu wani ku yi auren kisan wuta a sirrance a mayar da auren mu, anya kuwa zan iya jurewa?" Ya fad'a hankali a tashe..
(Ku yi hak'uri da wannan don kada na sab'a alk'awarine wallahi ba na jin dad'i)
Nagode sosai.
Jikar Nashe ce.
❤️❤️❤️❤️❤️🙏
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.