e: ." Wani irin kallo Didi take mata kamar ta ga abin kyankyami, ta mayar da kallonta kan Hamdan da take k'ok'arin mik'ewa ta ja wani dogon tsaki kafin ta ce "Ammo ce ta aiko ki ba Ammi ba, ni za'a kawowa kinibibin banza, wato ta ga uban yarinya mai kud'i ne shine za'a zo a kanainayeta, to wallahi ki gayawa Sakina ta fita idona, uban me ma ta baki ki kawo mata, wato yanzu zata nuna min ita ta haifi y'ar bayan da ta banzagatar da lamarinta, zube kayan mu ga wace uwar ce a ciki?" Munira gaba d'aya ranta ya b'aci jin abinda Didin ta fad'a duk da ta san gaskiya ta fad'a amma ai Ammin ta yi nadama me yasa ba za'a bar abinda ya wuce ya wuce ba, ita kuwa Hamda zuciyarta fara k'al ko bakomai Didin yau ta biya ta, da Ammin me ta sani nata ita kam ko ina zata bugi k'irji tace Didi ce babarta, sai Abbu shima ba zata mance kulawarsa gareta ba. "Ki ke kallo na ko duka na za ki yi? Zube kayan nan naga me aka k'unshe za'a je a bata, tun yanzu wato za'a fara koya mata bak'in halin asiri, to wallahi ba zan yarda ba eehe." Asma'u ce ta kashe maganar ta hanyar cewa "Haba Didi, duk me ya kawo haka? Ya za'a yi kice sai sun ware kin ga abinda ke ciki." "Ki kiyayani Asma'u babu ruwanki ta bud'e naga me yake ciki? Na sani ko maganin mallaka ne ta bata a mallake min jika kamar yarda aka mallake ubansa." Cikin takaici Munira bata san sanda ta zazzage kayan ba ta ce "Ga shi nan, kayan gyaran aurene da ake bawa duk wata mace idan za'a mata aure, wannan ki dinga sha da yoghurt wannan zuma ce wancan kuma turaren tsuguno ne, sai kuma tace a gaya miki ki dinga shafa wancan a fuskarki every morning kafin ki yi wanka na gyaran fuska ne kafin a sallace a fara muku gyaran jiki." Didi ta ja tsuka "Zancen banza zancen wofi, ce mata na yi ba zan siya mata kayan gyaran ba, tun yaushe ma Asma'u ta fara mata kinibabbiya kawai, d'auki ki mayar mata." Asma'u ta yi saurin cewa "A'a Didi, ba za'a mayar ba, ko wanne da irin aikinsa wannan na san na can garinsu ne, ki ce mata an gode." Asma'u ta kwashe kayan ta na mayarwa leda, Munira ta juya ranta a b'ace ta fice daga falon.
Ana shan ruwa ya shiga falon Didin, don yau Nanna bata nan a gidansu zata sha ruwa, fuskarsa a d'an had'e take don haushin Hamda yake ji kamar me? Ace mace ta yi banza da mijinta kuma ta ganshi amma ta d'auke kanta, ko gaisuwa a haka za suyi ta su rayuwar auren kenan bai isa ya sata ba, bai isa ya hanata ba?
K'ananan kaya ne a jikinsa na companyn Ck da suka matuk'ar amsar gogaggiyar fatarsa, sosai ta yi kwalliya fuskarta fal annanshuwa musamman aminyarta ta sun iso ita da yayyanta maza guda biyu. Riga ce doguwa a jikinta da ta fitar da duk wani shape na jikinta, sai hula irin ta turban d'in da ake ya yi ta d'an zameta ta yi baya, kwantaccen gashin da yake gaban goshinta ya bayyana bak'i sid'ik da shi, ta yi kyau sosai duk da ba kwalliya ta yi ba, idanunsa ya sauke cikin nata cike da takaicin yanayin shigar da take jikinta ga kuma Maza a wajen, ransa a b'ace ya dinga hurga mata harara. Didi tana ganinsa ta ce "A'a ka daina fushin ne ka shigo?" Sake tsare girarsa ya Yi sosai Yana amsa gaisuwar da suke masa ya kalli Didi "Ban da matata mai k'aunata bata nan, ban ga mai Zai kawo ni nan ba." Asma'u ta guntse dariyar da take shirin kamata don ta lura sosai Hammad yake Jin haushin hanashi keb'ewa da Hamda da aka yi. Hamda kuwa ranta a b'ace bata san sanda ta d'ago ta wurga masa wani kallo ba ya yi kamar bai ganta Ba Kafin ya kalli Sa'ada ya ce "Yarinyar kirki zubo min abinci maza ki kawo min shiyyata." Ya saka kai ya fice ji yake kamar ya mak'ure Hamda ya hukuntata da y'ar banzar shigar da ta yi. Didi tace "Zancen Banza, abincin ma ka yi masa zuciya mana yaro Sai cin tsiya." Sa'ada na shirya abincin ASMA ta kalli Hamda ta ce "Maza ki rakata ku kai masa k'afarki k'afarta kuma." Hamda ta d'aga kai alamar amsawa ko Umma Asman bata ja kunnenta ba, takaicin maganar da ya jefeta da ita ba Zai saka ta zauna ba, ya tafi can wajen matar tasa, ina ruwanta....
Kusan mintuna biyar suna knocking a bakin k'ofar sashen nasa bai bud'e ba, kamar ya san da ita aka zo ya d'au lokaci kafin ya bud'e, fuskarsa a d'aure yake dubanta, yana mamakin yarda lokaci d'aya ta birkice masa kamar ba Hamdan da ya sani ba, mai son sa da jin maganarsa, ta bi ta hau maganar Didi ta zauna a kai kamar wani fad'ar annabi, idanunsa cikin nata yana k'are mata kallo, kallon da ya takurata ta sunkui da kai, gaba d'aya kallon ya saka mata wata irin nutsuwar da bata shirya yinta ba, ita kuwa Sa'ada dariya ce take son kamata ganin yarda ma suka manta da ita a wajen har sai da ta yi gyaran murya sannan Hammad ya ankare ya saki wata malalaciyar ajiyar zuciya kafin ya mik'a hannu ya amshi basket d'in abincin da yake hannun Sa'ada ya ce "Je ki abinki Sa'ada akwai aikin da
Zata min yanzu zata taho." Hamda tayi raurau da idonta kafin ta ce "Wallahi Didi tace min kada na dad'e ka ga fad'a zata min." Ya watsa mata wani irin kallo da yasa Sa'ada wata irin dariya ta so kub'uce mata ta juya da sauri ta wuce don ba su saba y'ar wasa da Yaya Hammad d'in ba, amma kallon da yake jifan Hamdan da shi abin so ne ga kowacce mace mijinta ko saurayinta ya dinga mata shi, kallo mai nuna zallar so da nuna kewa ga wanda akewa shi, hannunta na rawa ta mik'a masa flask d'in kunun "Please Yaya Hammad ka karb'a kafin kasa Didi ta tara min mutane..." "Masifar Didi da tsinuwar mala'iku wanne kika fi gudu? Idan ba zaki shigo ki je kawai." Hawaye ne ya fara k'ok'arin zubo mata kafin ta saka k'afa cikin falon gabanta na fad'uwa, ta tsaya cak a bayan kujera shi kuwa tab'e bakinsa ya yi ya cigaba da zuba abincinsa lura da yayi da ko cewa ya yi ta zuba masa yarda take a tsorace ba zata zuba ba, shi har mamakinta ma yake kada fa ta zamo masa bagidajiya ba irin Nanna da take kanainayeshi ba, da sonsa da ba son ransa take fincikar ra'ayinsa sau tari. Ya fara kurb'ar kunun idanunsa suna yawo a kanta ta ji yace "Wani sabon salo kika samu? Sai kace sabon aure ba zaki dawo nan kusa da ni ki zauna ba? Saboda kina tsoron Didi ko?" Ya taune leb'ensa d'aya kafin ya furzar da huci ya ce "Idan kika ce haka zaki min wallahi a gadon Didin zan zo na karb'i hak'kina haka kawai saboda wata bidi'a ta banza da wofi ki yi ta d'aukan zunubi da azimin nan, ke kika jiyo ni ina da wata matar yau ma rashinta ne yasa nake binki duk da ba ni na jawoki ba, ke zaki je ki yi ta kwana rungumar filo ai dama Sabonki ne tun kina budurwa."
Wani irin kallo take jifansa da shi kamar ta zunduma masa ihu jin abinda yake ce mata, ita zai gayawa wani yana da mata ai ta fisa sani dama ita ta kawo kanta har da zai tsaya ci mata mutunci, haushi da takaicin kalamansa yasa ta juya a zuciye ta fice daga falon duk da tana ji yana k'wala mata kira. Ya saki ajiyar zuciya yana jin takaicin yarda bakinsa ya ja shi ya sake b'allowa kansa ruwa ya santa sarai da d'an banzan kishi, ba waya a hannunta balle ya kirata.
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.