48

217 2 0
                                    

A cikin harabar 'Dan Borno family house ya yi parking, tana k'ok'arin fita ya yi saurin rik'e hannunta ba tare da jin kunyar su Sa'ada da suke baya ba, ganin hakan yasa suma da
Sauri Suka fice daga motar. Idanunsa ya shigar cikin nata sosai kafin ya ce "Remain 3 days dai a daina min rowar jikina." Da sauri ta janye hannun nata tana danna lock d'in motar ta fice, ya bi bayanta da kallo yana sakin ajiyar zuciya Allah ne kad'ai ya san wahalar da yarinyar nan take ba shi. Kafin ya fito ya bi bayanta sai da ya ciji lab'b'ansa yana sakin murmushi.

A falo ta samu Didi a zaune kusa da KK da yake ta barcinsa cikin kwanciyar hankali, da alama ya da'de bai samu barcin irin haka ba, za ta yi magana Didin ta yi saurin saka yatsa a lab'b'anta alamar ta yi shiru, Hamda ta saki ajiyar zuciya tana bin bayan y'an uwanta su Sa'ada da suka shige cikin d'aki. Sai dai kafin ta kai 'daki ta jiyo atishawar KK da sauri ta jiyo shima Hammad daidai lokacin suka shigo da Kamla da Abulkhairi. Gabansa ne ya fa'di ganin KK 'din kamar mara lafiya ya shiga cikin sanyin jiki kafin Didi ta ja tsaki ta ce "Kun tashe shi hankalinku ya kwanta, haba ni ban tab'a ganin jaraba irin wannan ba, kai mai ma ya shigo da kai nan?" Kk ya mik'e yana murmushi hannayensa rik'e da kansa da ya ji yana 'Dan sara masa ka'dan ya ce "Ki barsu Didi, ai na ma 'Dan samu sauk'i dama ciwon kaine ya matsa min." Ya zuba idanunsa akan Hamda da ya ganta kamar mara lafiya ya ce da Hammad "Me ya faru da iyalinnaka na ganta so weak haka?" Tsagal Didi ta yi kafin ta ce "Me zai sameta banda ta sake kwasowa kanta ciki don tsiya irin ta Hamda sai da na ce kada ta sake ta saurari yaron nan sai an danganata da 'dakin miji amma ta yi burus da ni ta nuna ban isa ba, ai ga shi nan ya kai ki ya baro za'a yi taron biki da ciki, dama idan za ki yi Amanki don Allah Hamda ki taimakeni kada ki yi shi kusa da ni." Kunyar duniya ta gama kama Hamda bata san sanda ta mik'e tana hawaye ba ta shige 'daki KK dariya ya yi kawai yana bin cup 'din kunun da Didi take mik'a masa "Maza ka sha kunun tsamiya ne zaka samu afuwa in sha Allah." Gefe guda Kuma peppe soup ne na naman rago ta masa mai yaji mai yawa ganin kamar mura yake. Sosai ya ji da'din kunun ya yi murna da shigowarsa cikin rayuwar su Didi ga shi yanzu ita yake gani matsayin mahaifiyarsa.


_____________________

Sosai babban hall 'din dinnerr ya cika kana ganin wajen zaka san Naira ta ci k'aniyarta. Hamda da yayyanta ba k'aramin kyau suka yi ba, cikin tsadadden lace 'dinsu sea blue, Dinner ce ta mata zalla ba maza ko masu 'daukan hoto mata ne zalla kamar yarda KK da Abbu suka zartar ba sa son caku'de'deniya tsakanin maza da mata sun kiyaye dokokin ubangiji k'warai da gaske.

Yana mota yana jiranta kamar yarda ya yi alk'awarin a yau zai zarce da ita gidansa ba sai gobe ba kamar yarda aka tsara. Ya gaji da wa'dannan bidi'oin ba kuma zai tsaya sai wani gayyar y'an kai amarya sun kai masa matarsa ba, da kansa zai kaita har gidanta, sai dai su shafa su ji ba amarya. K'amshi kawai yake zabgawa daidai lokacin da Ya ganta sun taho tare da Sa'ada kana ganinta ka san a galabaice take don da kyar ma take tafiya sosai take buk'atar hutu. Hannu yasa ya bu'de mata gaban motar kafin ya kalli Sa'ada murya ba wasa ya ce "Please Sa'ada we need privacy ki koma motar su Munira." Sa'ada ta waro ido tana kallonsa ya 'd'aga mata gira cike da son tabbatar mata. Murmushi kawai ta saki ta juya shi Kuma ya shige motarsa.
Kyan da ta yi ne yake sake jan idanunsa yake kallonta yana sakin ajiyar zuciya yana k'iyasta da mai zai kwatanta yarda yake sonta a zuciyarsa. Da sauri ya ja motar ganin tana shirin kuka yana fara tafiya wani barci mai nauyi ya 'dauketa ya saki murmushi a hankali ya furta "Ki farka ki ganki a gadonki na gidan ki na aure haba wannan gantalewar ta yi yawa." Ya fa'da Yana shafa kumatunta masu sulb'i da wadataccen taushi. Hannun ta ta sa ta rik'e masa hannu ba tare da ta sani ba saboda barcin da yake idonta.

Bai tsaya ko ina ba sai a harabar katafaren gidansa da KK ya mallaka masa gari guda mai tsari da zubi irin na k'asar waje. Wani abu kawai ya danna a hannunsa mai kama da mabud'in mota kyakykyawan gate 'din ya bu'de shi kuma ya danna hancin motar ciki, yana bin harabar wajen da kallo da k'amshin damuna da na bishiyoyin wajen suka gama hancinsa ya zuk'i k'amshi yana sakin murmushi ha'de da jaddada godiyarsa ga Allah mamallakin kowa da komai, mai ikon canja komai a duk lokacin da ya so kuma ya ga dama.

Ya Abin Yake?Where stories live. Discover now