/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: "Hukumullahu la ajabun.." shine abinda Didi take ta fad'e tun bayan jin maganganun KK d'in da suka zame musu tamkar labarin irin tatsunuyoyin nan, ko hikayoyi, idanu duk d'aukacin mutanen wajen suka zuba masa, zuk'atansu cike da ta'ajibin lamarin. Hamda kam farin ciki ne ya cika zuciyarta, jin Mahaifinta shine KK, ta kuma tabbatar da hakan musamman da taji ya ce a kashegari zai gabatar da duk wasu shaidu da za su tabbatar da auren su da Sakna. Gaba d'aya ta ji ta sake k'ank'ame jikinsa tana mayar da ajiyar zuciya da sauri, shi d'in ma cikin tarin k'aunar d'iyar tasa ya sake rik'eta sosai yana jin tamkar ya mayar da ita ciki, k'aunar da ta rasa ta shi tana k'arama ita ce yanzu ya d'auki d'amban shayar da ita da dukiyarsa da jikinsa da duk wani abu da ya mallaka. Ammi kuwa idanu ta zuba masa cike take itama da matsanancin mamaki ko a mafarki bata sawa zuciyarta ganin KK Mud'allab ba sai gashi ashe a zahiri ma har shimfid'a suka had'a ba tare da ta sani ba, suka had'a
Jini ta hanyar haihuwar Hamda,
Abinda bata tab'a kawowa ba ko a hasashe, wannan had'ad'dan mutumin mai k'irar larabawa, mai tarin dukiya fiye da zaton mutum don za'a iya saka shi a cikin mutane masu kud'in Nigeria a sahu na biyar idan bai kai na hud'u ba, tabbas ta yarda lamarin Ubangiji mai girma ne, da yake zartar da hukunci a duk lokacin da ya so. hamdan da ta wulak'anta ta tozarta a cikin yaranta, zatonta duk jinin mai gadi ne ashe k'arshenta ita zata samar mata da gata a rayuwa ita zata zame mata sanyin idaniya. Wasu zafafan k'walla suka zubo mata takaici da dana sanin abinda ta shuka a rayuwa ya bi ya dabaibaye zuciyarta, matsananciyar kunyar abinda ta aikata ya cika mata k'irjinta, har bata iya d'aga kai ta had'a ido da mutanen da suke falon.Abbu shi kansa mamakin lamarin yake, da gaske lamarin ya girgiza shi, ganin abin yake tamkar almara shine ya raini jinin KK Mud'allab abinda ya matuk'ar girgiza tunaninsa duk da a kullum dama zuciyarsa tana tunanin ta yarda Hamdan take matsananciyar kama da KK Mud'allab d'in, bai tabbatar ba sai yanzu da ya gansu a tare.
Didi ta sake sakin ajiyar zuciya tana hamdala a zuciyarta da Allah yasa bata bi son ran Sakna ba, sun had'u sun gallazawa Hamda da yanzu da wani ido za su dubi hamshak'in ubanta, ta tabbata da sun tabbata hasararru duniya da lahira tunda suna ji suna gani KK Mud'allab ba zai mora musu komai daga b'angaren dukiyarsa ba, yanzu kuwa ta tabbata shar da ita zata murza dollar ba ma Naira ba, Saudiya kuwa idan duk juma'a take so zata je tunda ta kwana da sanin cewa KK Mud'allab d'in jiragen sama ne da shi ba ma jirgi ba. Ta sake gyara zamanta tana cewa "To Alhamdulillah Masha Allah da Allah yasa na ga lokacin nan ina raye, ashe dai mun had'a jini da bawan Allahn nan.." Gaba d'aya falon suka bud'e baki da idanuwa suka zuba su kan Didi jin furucinta wai sun had'a jini da shi ko ta ina? Abbu kansa duban Didin yake ta yarda take shirin fallasa sirrin zuciyarta, Didi ta galla musu harara wallahi ta ga samu ba zata ga rashi ba, ta dinga raya hakan a zuciyarta ai ni gaba ta kaini, wannan sallahr ma a gidan d'ana zan yi ta. "Naga kuna min kallon mamaki, k'arya na yi bamu had'a jini da shi ba, tunda dai Uban Hamda ne ai kuwa ni daga yau d'a na d'aukeshi, ke dai Sakna Allahu ya saka miki da mafificiyar aljanna, da har kwanyarki ta yi aikin da ya dace kika samu ciki da Kamal na tabbata kina da k'ashin arziki, matsalar d'aya baki yiwa d'iyarsa rik'on kirki ba, abinda nake ta gaya miki baki san ta yarda za ki moreta ba, Yo Allah na tuba ban da ni ai Hamda ba zata rayu ba, Ni na ci kashinta na ci fitsarinta, idan kuma k'arya nake gata nan da ran Allah Kamalu ka tambayeta, a gidan nan sam bana yarda a d'aga mata yatsa, Allah nagode maka da ban yiwa kaina ba yanzu yaushe za muje can wajen tsinannun y'an uban naka su ga kana da yara har guda biyu?" Wannan Gwaggo Asma'u har sai da ta tab'o Didi Jin tana shirin sakin layi, ta ture hannun Asma'u tana cewa "Bar hanani y'ar nan, duka a furuci na babu k'arya, k'afata k'afar Hamda ta je taga dangin ubanta." KK murmushi yayi sam bai damu da abinda Didin ta yi ba shi kansa a yanzu yana buk'atar ya samu wacce zai nuna matsayin uwa a k'asar Nigeria, duk wanda suke ba shi kulawar ya tabbatar ba don Allah suke sonsa ba, Didi kuwa zai iya cewa ba ya shakka a kanta. Ya matsa har kusa da Didin yana kama hannayenta har yana matsasu yana jin tamkar tasa uwarce, sai yaji wasu hawaye suna k'ok'arin zubo masa, da sauri ya matsesu ba wannan a rayuwarsa tuni ya shafe babin kuka ya d'auki jumurin juriya da hak'uri, da karyayyiyar murya mai amsa amo ya ce "Not now Didi na, ba yanzu ba sai na gama duk wani shirye-shirye sannan Zan kai musu card d'in bikin Hamda su ga sunana da nata a had'e b'aro-b'aro na San a lokacin za su buk'aci k'arin bayani ji kuma sai na bayyana musu Hamda da Kamla matsayin yarana." Didi at shafa kansa tana murmushi ta ce "Ranar dai za muga yarda tambad'add'u za su yi hu um." Ta fad'a tana jijina kai. KK ya yi murmushi tare da mayar da kansa kan Alhaji Umar wato Abbu ya isa har wajensa ya durk'usa ya dafa shi shima d'in kama hannusa ya yi yana murzasu kunyarsa yake ji sosai ta yarda yayi tarayya da matarsa ba bisa son ransa ba, ganinsa yake kamar yayansa k'asa ya yi da kansa kafin ya ce "Ka yi hak'uri Umar na san lamarin da ciwo don Allah ka yafe min ba bisa son raina bane, duk da na san ba haramun bane amma a yau na tsinci kaina da jin matsananciyar kunyarka, dafatan zaka fahimceni ka kuma fahimci matarka don wallahi ta cancanci a kirata mata ta gari, tunda da wata ce can zata nemi wani ya yi lalata da ita ta kuma kawo maka d'an tace naka ne ba yarda za kayi dole ka karb'a." Abbu girgiza kai ya yi duk wani tuk'uki da yake ji da b'acin rai ya zagwanye ya bi iska, shi kansa ya hak'kake lamarin ubangiji abu ne mai girma, muryarsa fresh ya ce "Bakomai haka Allah ya k'addara ubangiji ya yafe mana gaba d'aya." Suka rungume juna cikin aminci. Daga haka hira ta sake b'arkewa Hamda duk inda KK yayi idanunta a kansa wata irin k'aunarsa take ji fiye da komai a rayuwarta tana kuma jin tausayinsa tsawon lokaci da ya d'auka yana fuskantar cusgunawar y'an uba. Sai kusan k'arfe 1:00 na dare sannan ya mik'e bayan ya mik'awa Hisham wasu takardu yana fad'in "Congrats Hisham ginin companynka na gine-gine ya kammala a Abuja, nan da bayan sallah zaka iya fara aiki, ka kuma je ka tattaro komatsanka daga Birmingham ga gida nan guda biyu d'aya a Abuja d'aya a kano, alfarma d'aya zaka min Ka bari a sake bikin Hamda kafin ta tare a gidan da ka zab'a mata." Murna da farin ciki ta bayyana a fuskar duk wani masoyin Hammad musamman Sadiya da kunyar duniya ta riga ta kamata, musamman yarda ta dinga yiwa Hamda ashe dai arzikin uban Hamda d'an nata yake ci. Za su fara zuba masa godiya ya Yi saurin dakatar da su "Hammad d'ana ne, ina jinsa tamkar yarda nake jin Hamda da Kamla a zuciyata, babu godiya a tsakaninmu Zan ci dukiyata yayi kuma iko da ita kamar yarda Hamda da Kamla zasu yi" Didi ta gyara zama tana zabga musu harara "Bar su dai Kamalu masu shegen shishshigin tsiya ina ce tare kuka gansu? Za ku wani bud'e baki ku fara masa godiya, amma kuwa Kamalu don dai kada kace na yi maka katsalandan da makka muka tafi muka je muka dinga yiwa rabbil izzati buwayi gagara misali godiya." Ya saki murmushi yana dafa Didi "Insha Allah Didi Makka har sai kin ce a barki ki huta, ba Makka kad'ai ba ma duk garin da kike so, yanzu an riga an rufe shiga da irin jiragenmu dalilin goman k'arshe ta zo, amma ana sallacewa za ku tafi da ke da ahalin D'an Borno gaba d'aya." Didi na murmushi ta ce "Alhamdulillah Masha Allah, sai
Magana ta gaba, ban yarda na sake ganin k'afar Hammad a sashena ba har sai an kawo lefe idan kuwa ba haka ba ya dinga zuwa da yamma sabida ba abinda yake koyawa yarinyar nan ba sai tsiya irin dai tsiyar nan da ake a tashar fararen fatar nan ganin idona na kamashi yana tand'eta da lasheta alhali uwarsa ma ta ce sakinta zai yi. Wai ni ina Sadiyar ne ma na ji bakinki ya mutu ko a mik'o miki biro da takardar ya rattaba mata sakin?" [1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Shawarar da na yanke ina tantamar idan abin zai yiwu sai dai na tabbata idan ba hakan ba, ba ta yarda za'a yi na samu gudan jini na a rayuwa, tunda su burinsu gado ne, na mutu su gaji dukiyata shi yasa na b'ullo musu ta yarda ba zasu tab'a tsammani ba, zan kuma shayar da su ruwan mamaki idan abinda nake so ya afku.Rana guda na ware na fita k'asar waje inda na sa aka k'era min fuska, ta yarda duk k'wak'warka ba zaka tab'a zata ni ne ba, a b'oye na fara neman aure sai dai duk gidan da naje aka ganni ba alamun kud'i a tare da ni ba a maraba da ni balle ma a bani damar da zan nemi aure a gidan.
Fuskar Buzu Mai gadi itace fuskar da nayi amfani da ita nazo nan gidan neman aiki, na ci sa'a kuma aka bani, inda na nemo wani ya yi representing d'ina ta hanyar saka masa waccan fuskar da nasa aka k'era min, na kuma koyar da shi yarda zai dinga karya harshe ya dinga maganar buzaye. Saboda a lokacin wata y'ar talakawa na gano anan k'asan layinku bana so kuma a san ni ne shine na yi wannan fasahar na saka shi ya saka mata ido ya tabbatar da nagartar halayenta, sai dai ba'a je ko ina ba ya gano min bata da tarbiyya ko kad'an hijabi take sanyawa take ci da addini, a kuma ranar ne shi wannan mutumin da ya maye gurbina anan gidan yazo min cikin matuk'ar tashin hankali yake sanar da ni abinda matar gidan nan ta buk'ace shi yayi, hankalina ya tashi jin ta yarda ta b'ullo masa sai dai na samu sukuni da ya tabbatar min bata da aure, hakan yasa wani tunani ya bak'unci zuciyata, na ji mai zai hana na gwada sa'ata akan Sakna, tsawon lokaci ina neman fita har naji na aminta da cewa Allah ne ya kawo min Sakna don cikar muradina tunda dai ta tabbatar tana da aure. A take a wajen na amshi fuskar nan daga wajen Habeeb wanda Aminina ne na k'ud da k'ud, na mayar da fuskar a tawa fuskar ina kallonsa da murmushi fal a tare da ni na ce "Habeeb wannan aikin nawa ne, kaga idan har Allah ya taimakeni za'a rainan min d'a ba tare da an san ni ne ubansa ba, sai sanda na so fallasuwar sirrin sai naje mata da zancen ta bani d'a na idan kuma ta k'i sai na saka dole ayi DNA test inda na tabbata za'a gano k'wayoyin halittunsa daidai suke da nawa, kaga anan balli zai tashi." Habeeb ya saki murmushi shima yace "Bas, shikkenan." Daga nan nace masa yaje ya ce mata ya amince ta fad'i masallachin da za'a d'aura auren.
A ranar da daddare aka d'aura mana aure da ita, ita a zatanta ni d'in BUZU ne, amma na tabbata a wajen d'aurin auren ta ji ana cewa an d'aura da Muhammad Dini. Duk da na san a lokacin ba damuwa ta yi ta san sunan nawa ba, buk'atar ta a d'aura auren ta samu abinda take buk'ata.
Kashegarin ranar komai ya wakana tsakani na da ita, a kuma lokacin Hammad ya ganmu duk da fuskata bata bayyanu k'uru-k'uru ba, takaici ya kamani sosai na yi dana sani don gani nayi kamar da laifin kwarton gaske aka kamani, na so tun a lokacin na bayyanawa Hammad gaskiya zance sai dai na rasa ta yarda zan yi in gaya masa. Har sai ranar kwana biyu da na sake shigar basaja naje gidan, abokina shi kuma yaje duba matarsa da bata da lafiya a asibiti. A lokacin ne Hammad ya sameni a kuma ranar na bayyana masa kaina ta hanyar zame mask d'in da yake fuskata, mamaki sosai ya bayyana a kan fuskarsa har kusan suman wuncin gadi ya yi, sai da na rik'o hannunsa na tabbatar masa da gaske ni ne, na kuma ba shi labarina, hankalinsa ya tashi ba tare da ya shirya ba ya shiga amsar alk'awarin rik'e min Sirrina. Da ni aka shiga aka fita wajen sama masa makaranta da duk abinda zai buk'ata a Birmingham, a cikin gidana yake zaune a can d'in ni kuma na samar masa aiki a can d'in. Na san duk wani motsin Hamda itama ban dai bayyana kaina ba ne ina jiran lokaci yayi, sai yanzu Allah ya kawo. Ita kuwa Kamla sanda matata ta samu cikinta ni da kaina na wuce da ita garin Birmingham tana haihuwa na kira Hammad ni mik'a masa ita tare da rok'on alfarmar ya rik'e min Sirrina, ya amsa kuwa ban kuma sake waiwaitar ba itama sai yanzu. Da kaina na d'aura auren Hammad da Hamda a garin Birmingham. Yanzu ma shi ya kirani yake gaya min tashin hankali da ya fara wanzuwa a gidan nan shi yasa na zo na bayyana kaina, dafatan duk za ku min afuwa duk da tarin laifina..."___________________
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.