Ya abin yake?
Nazeefah Nashe
08033748387
BONUS PAGE...
16..
(Saboda wasu da suka buk'aci a
D'an k'ara musu free pages shi yasa zan d'an k'ara ko 3 pages ne. Zuwa lokacin ku yi ta payment. 3 to 5 pages kawai zan k'ara. Nagode)____________________________________
Tunda ya isa k'ofar gidan surikansa ya yi parking kansa kawai ya d'ora akan sitiyarin mota yana jin yarda zuciyarsa ke bugawa da tsananin b'acin rai gami da tururin bak'in ciki. Me yasa Abbu zai yanke hukunci cikin fushi ba tare da shi ya ji ta bakinsa ba, ko a kotu ake kafin zartar da hukunci dole sai an ji ta bakin mutane guda biyu. Amma zai bawa Sakina mamaki zai nuna mata shi ma ya iya rashin mutunci kamar ko wane d'an zamani. Ya runtse idonsa gami da cije leb'ensa da k'arfin gaske tamkar zai huda shi, sai kuma ya saki yana furzar da tururin b'acin rai, da gaske sai ya rama yayi alk'awarin yin ramuwar gayya a lokacin da bata yi tsammani ba, sai ya tozartata gaban kowa sai ya kuma fito da ainahin b'oyayyiyan halinta kowa ya gani an kuma yi Allah wadarai da ita. Duka wad'annan zai yi su ne a lokacin da
Ta sakankance ta manta da batun
Shi kuma zai bayyanar mata a matsayin ramuwar gayya.Wayar hannunsa ya shiga dialing
Bayan da yaji Abulkhairi na kiran Dad Dad mun zo ba. Cike da takaici ya d'an shafa kansa.Nanna da take zaune kusa da Mamanta ta d'aga wayar "Ki fito ina waje." Shine kawai abinda ya ce ya katse wayar, Nanna ta tab'e baki don tuni ta saba da halinsa in dai wannan ne. Mayafinta ta yafa ta fice da sauri don ta ji dalilinsa na zuwa shi da ya ce sai dare zai zo d'aukar ta.
Turus ta yi ganin yarda fuskarsa take a matuk'ar d'aure zata iya cewa tun bayan aurensu bata tab'a ganin fuskarsa a wannan yanayin ba. Ko lokacin da yake shiga wancan yanayin idan an b'ata masa rai bata tab'a ganin fuskar sa ta koma haka ba.
Ba tare da ya yi magana ba ya bud'ewa yaran k'ofa yana dubanta cikin yanayi na bada umarni ya ce "Ban amince ko da wasa ki je Gidan mu ba, kuma ku shirya nan da 1 week za mu koma inda muka fito." Idanunsa cikin nata tana k'ok'arin samo kalmar da zata furta masa, tambayarsa take son yi amma kafin furucin ya fito ya ja motar da mugun speed. Nanna ta saki ajiyar zuciya had'e da furta Allah ya kyauta ya kuma saukeke lafiya. Amma wannan jaraba har ina ayi mutum sai kace mai shafar Aljanni.Jikinta a sanyaye ta shiga gidan nasu, Ummanta na ganinta ta ce "Lafiya? Ko k'in zama suka yi ya rakito su nan?" Nanna ta girgiza kai "Ko d'aya, kawo su ma ya yi ya kuma ce ko da wasa kada na sake na koma gidansu, ban san dalili ba." Umman ta girgiza kai had'e da
Lalubo wayarta ta shiga kiran Yayarta.
Sai da tayi ringing sosai kafin Sadiya ta d'aga zuciyarta na harbawa dafatan Allah yasa ba wannan labarin mara dad'in ji bane ya je kunnen K'anwarta da wani ido zata kalli y'an uwanta ta ce "Eeh, hakane Hammad ya yiwa matar ubansa fyad'e har ta haifa masa y'a da kunya ai, duk da tana tantama idan har hakan ya faru da gaske. Jin k'anwarta ta Dida na ta fad'in hello Yaya ba kya ji nane? Na ce me ke faruwa a can gidan ne Hammad ya kawo yara har kuma yana gargad'in Nanna da kada ta sake ta sake zuwa ko k'ofar nan gidan." Sadiya ta saki ajiyar zuciya, murya a dashe ta ce "Wallahi d'an sab'ani aka samu Dida, ta bi umarninsa kada ta zo d'in har muga abinda hali yayi, yanzu haka muna asibiti da Didi bata uhm ba ta uhm-uhm har yanzu kuma likitocin ba su ce da mu komai ba." Dida ta saki salati kafin ta ce "To Allah ya kyauta, ya yi mana maganin koma menene, ita kuma Didin wani asibiti ta ke sai mu zo ai yanzu." Kamar ba zata gaya mata sunan asibitin ba sai kuma ta daure murya a cunkushe ta sanar mata, had'e da kashe wayar, tana sake lalaubar numberr Hammad amma still bai kunna wayar ba. Gabanta ne yake fad'uwa bata son Hammad d'in ya je ya aiwatar da wani abu cikin fushi, sai dai ta san bata da halin tafiya ta bar Didi da iyalinta a cikin wannan yanayin.
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.