❤️❤️❤️❤️❤️🙏
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: K'ok'arin tureshi take yi, amma bai bata damar hakan ba, duk da ya ga Didin na kusanto su sake manna bakinsa ya yi cikin nata, fatansa Didin ta gansu ina ruwansa tunda ya san ba haramun ya aikata ba, ya manna ta da jikinsa sosai ta yarda ba zata samu damar tserewa "Nutsu Malama, kada ki sake tureni da fushin Didi da na mala'iku wanne ki ka fi tsoro?" Hawaye kawai ta ji suna zubo mata ganin Didin dab da su, cikin gigita ta runtse idanunta tana jiran jin saukar sandar mopperr a jikinta. Sai ta ji Didin ta saka salati "Innalillahi, wace jalaba ce wannan cikin dalennan kazo kana lalubeta kai dai an yi tanbad'adde k'warai da gaske." Bai kulata ba, ya mik'e da Hamdan a jikinsa ya sake rik'ota sosai idanunsa cikin na Didin ya ce "Haramun na aikata?" "K'anin haramun ka aikata tunda ni ban amince da wannan tambad'adden auren naka ba." Ciki-ciki ya yi da idonsa kafin ya ce "Kada ki sake tambad'a min aurena, aurena na halak ne da shaidu da komai.." Didi ta wurgi Hamda da take k'ok'arin k'wace hannunta daga nasa da harara "Munafuka da kika ganni ba, ke wato har kin iya biyo dare ki samu namiji saboda kina jin dad'in tumurmusaki da yake yi, tun kina budurwa ai na san kema jalababbiya ce yadda kike kwana kina matse filo a jiki, ba zaki wuce ba tai na maka miki tandan nan." Da sauri Hamda ta fincike Hannunta ta shige d'aki wata kunya da bata san daga inda ta taho ba ta had'u ta rufar mata. Didi ta bi shi da kallon banza kafin ta ce "Wallahi Hammad na sake ganin k'afafunka a nan tai na taka Umalu ya yi mana tsakani da kai." Shiru ya yi mata don gaba d'aya Hamda ta tafi da duk wata nutsuwarsa jin sa yake da kyar yake mayar da numfashinsa ga Didi na neman sake caza masa kai, ya mik'e cike da k'warin gwiwa yake kallonta "Saboda lefe kika rik'e min mata? Idan na yi lefen a gobe za ki bani Matata?" Kallon banzan ta sake watsa masa kafin ta ce "Ai idan kaga na baka ita, an had'a an yi bikinta da na y'an Uwanta da za'a yi ana tallacewa tannan za'a kaita d'akinka, don ban yarda ka sameta a gantale ba." Kallon baki isa ba yake mata kafin ya yi k'wafa ya sa kai zai fice ya jiyota tana fad'in "Ni Za'a kawowa itkanci wallahi ka take zuwa ma tai na fad'awa Tadiya ta titseyeka ka taketa ai dama ba son Auren takeba, na ma
Yi mamaki da hal yanzu bata take tada balli ba." Jikinsa a mace ya wuce sashensa gaba d'aya jallabiyarsa ta nad'e k'amshin jikin Hamda tsaf,
K'amshin da yake sake tada masa zafaffiyar sha'awarta. Wanka ya shiga kafin ya fito ya kwanta gefen Nanna da ta juya masa baya, zuciyarta cike taf da jin haushinsa don ta tabbatar daga gurin Hamda yake tunda ya shigo ta ji k'amshin turaren mata a jikinsa, tsaki ta ja a hankali ba tayi zaton zai ji ta ba, ga mamakinta sai ji tayi ya birkitota yana jifanta da kallo da manyan idanunsa "Allah yasa dai tsakinki ba dani kike ba?" Tsoro ne fal ya cikata shi yasa ta k'i biyewa zuciyatta da take ingizata tace Da shi d'in take sai me? Amma madadin haka sai ta girgiza kai cike da tsoronsa "Magana za ki min, Bana son raini." Murya a shak'e ta ce "Ba da kai nake ba, kaina ne ya ke min ciwo." Ya sassauta rik'on da ya yi mata ta hanyar shafa kan sai ya ji da d'an zafi da alamar da gaske ciwon kan take, sauka ya yi ya samo ruwa da paracetamol ya b'alla yana cusa mata bakinta ta samu ta had'iye da kyar, suka kwanta yana d'an murza mata kanta yana k'okarin yakice tunanin Hamda da ya tsaya masa a k'irji.Hamdan kuwa fad'a ta sha gurin Umma Asman sosai akan yarda ta yi kunnen uwar shegu da jan kunnen da ta yi mata. "Ba zaki bari a siya miki mutuncinki na y'a mace Ba? Ba zaki bari ya dinga d'okinki Ba, zuwa kika yi kika sake sakar masa jiki, kin kyauta to." Kunya ce ta kamata sosai har ta ji takaicin yarda ta fita ta sameshi ta tabbata rigar da take jikinta ce ta janyo ya kasa hak'uri sai da ya jata jikinsa, tunda idan har zai ganta a haka ta tabbata Ba zai iya d'auke kansa ba, dama ya lafiyar giwa, dole kuwa ta ja jikinta da shi, musamman da bata san makomar auren nasu ba, daga yanayin yarda Mahmah take amsa gaisuwarta ta tabbata ba tayi na'am da aurensu da Hammad d'in ba, za kuma ta iya datse shi a duk lokacin da ya yi mata. Ba zan sake kusantarka ba har sai Mahmah ta amince da aurenmu shine tunanin da take a zuciyarta.
__________________
Duk fushi take da Ammin amma tana jiyo muryarta falon Didi sai da ta ji zuciyarta na son ta ganta, tana son Ammi fiye da kowa a rayuwarta, zuciyarta na son fita ta ganta ko da zata yi mata hararar da ta saba, amma tana tunanin lokutan da Ammin ta d'auka tana wahalashsheta akan laifin da Ba nata ba, ashe duka kuskuren ma idan za'a tankad'eshi a taskaceshi na Ammin ne kacokam ba nata ba, ita tabi son zuciyarta Allah kuma ya nuna mata ikonsa ba dai d'a namiji take so ba, to shi kuma Allah bai so ta haifa ba. Kasa jurewa ta yi sai da ta mik'e ta fita jin kukan Ammin a gaban Didi kamar ranta zai fita tana jiyo sautinta tana fad'in "Don girman zatin Allah Didi ki yafe min, Umar ya ce ba zai cigaba da zama da ni ba har sai idan ke kika amince masa, wallahi zan gyara kuskurena zan zauna da kowa Lafiya, zan yi biyayya a gareki Didi ki tuna ko Allah muna masa laifi ya yafe balle d'an Adam, Didi watan azimi muke ki dubi girman Allah alfarmar watannan ki yafe min." Yawan magiyar ya sa Didi taji tausayinta da sauri ta d'aga mata hannu "Ya ita Takina, dama ni ban tab'a k'ullatarki ba, kuma sai a godewa Allah da ba ta hanyar banza kika samar da cikin nata ba, Zan yafe miki amma tai kin ja y'alki a jiki kin nuna mata soyayyar da duk bata samu ba, kin wanke mata wancan bak'in painting da kika goga mata a zuciya, daga yau kuma nake ton na fala ganin canji shima Umalun zan gaya mata. Abu na gaba ki zauna da kowa lafiya, mu nan da kike gani ba wanda yake k'ullatarki kowa son ki yake, ke ki ke ganin kamal ina fifita Tadiya a kanki ko d'aya ba haka bane, Idan kin gyala halinki za mu zauna da ke k'alau. Allah ya take tiltyal da ke alfalmal muhammaduna manzan Allah." Murna da tsananin farin ciki ne yasa ta fara kwararar da hawaye tana furta "Nagode Didi Asma'u ki taya ni godiya." Murmushi Umma Asma'u take ta kuma k'walawa Hamda da take tsaye a bayan k'ofa kira. Farin ciki yasa Hamda tahowa a guje ta zube a gabansu tana sakin hawayen murna, bakinta ya kasa rufuwa wani kallo kawai takewa Ammin tana kallon hannayen da Ammin ta bud'e mata alamar ta taho, Ba tayi wani jinkiri ba ta fad'a cikin k'irjin da ta dad'e tana son jinta kwance a cikinsa tana kuka har mafarkin hakan take, cikin wata iriyar soyayya mai zafi Ammin ta rungumeta tsam a k'irjinta hawayen farin ciki yana zubar musu, tana jin kuma yarda zuciyoyinsu suke bugawa kusan lokaci d'aya. K'aunar nan ta tsakanin uwa da d'a ta taso ta lullub'e zuk'atansu. Daidai Lokacin da Abbu da Hammad suka shigo kamar had'in baki farin cikinsu ya yawaita ganin Hamda rungume a jikin uwarta karo na farko a rayuwa Hammad bai san sanda ya danna wayarsa ba ya shiga yi musu vedio fuskokinsu cike da walwala. Didi fad'i take "Hukumullahi la ajabun, Yanzu kin yarda haihuwa a wajen Allah take ko? Shi yake da ikon bayar da namiji ko mace yanzu haka ita da baki to haihuwarba, ita zata zame miki Tanyin idaniya"
YOU ARE READING
Ya Abin Yake?
General FictionUwa Ta haifi yarinya da cikinta, amma ta tsaneta tsana mafi muni da zata yiwa wani abin halitta a bisa wani b'oyayyen dalilinta.